Yanzu Yanzu: Gwamna Abba Kabir Yusuf Ya Sake Nada Shugabannin Hukumomin Gwamnati

Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya amince da nadin karin shugabannin hukumomin gwamnati.

A sanarwar da babban sakataren yada labaran Gwamnan Sunusi Bature Dawakin Tofa ya sanyawa hannu, ta ce Wadanda aka nada sune kamar haka.

1. Kabiru Getso Haruna, Babban Sakataren Hukumar ba da tallafin karatu ta Jihar Kano.

2. Farfesa Aliyu Isa Aliyu, Darakta Janar na Hukumar Kididdiga ta Jihar Kano.

3. Dr. Kabiru Ado Zakirai, Babban Sakataren Hukumar Kula da Manyan Makarantun Sakandare ta Jihar Kano (KSSMB).

4. Alkasim Hussain Wudil, Coordinator, Cibiyar koyar da sana'o'i Aliko Dangote

5. Farouq Abdu Sumaila, Babban Sakataren Hukumar Ba da Shawara ta Jihar Kano.

6. Alh. Umar Shehu Minjibir, Shugaban Hukumar Ma’aikatan Jihar Kano.

7. CP Kabiru Muhammad Gwarzo mai ritay, Darakta Janar na Cibiyar Tsaro ta Kasuwanci ta Jihar Kano, Gabasawa.

8. Dr. Abdullahi Garba Ali, Darakta, Kano Informatics Institute, Kura.

9. Hajiya Shema'u Aliyu, Darakta a Cibiyar Kula da Baƙi ta Jihar Kano.

10. Dr. Musa Sa'ad Muhammad, Daraktan Cibiyar Wasanni ta Jiha, Karfi.

11. Dr. Abubakar Shehu Minjibir, Daraktan Cibiyar Raya Jarida ta Jihar Kano.

12. Abdullahi S. Abdulkadir, Darakta a Cibiyar sarrafa gonaki ta Jihar Kano, Kadawa.

13. Jazuli Muhammad Bichi, Daraktan Cibiyar Kula Dabbobi ta Jihar Kano, Gargai.

14. Dr. Maigari Indabawa, Daraktan Cibiyar Fina-Finai ta Jihar Kano, Tiga.

15. Kabiru Yusuf, Daraktan Cibiyar Koyar da kiwon  Kifi ta Jihar Kano, Bagauda.

Dukkan nade-naden zai fara aiki nan take kamar yadda aka umurci wadanda aka nada da su karbi sabbin ayyukansu cikin sa'o'i 48 masu zuwa na wannan sanarwar.

Popular posts from this blog

Yanzu - Yanzu: Bankuna Zasu Karbi Tsofaffin Kudi Ko da Bayan Karewar Wa'adi - Emefiele

Zababben Gwamnan Kano Ya Kafa Kwamitin Karbar Mulki