Sanatan Kano Ya Ba Dalibai 620 Tallafin Karatu A BUK

 


Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa kuma Sanatan Kano ta Arewa Barau Jibrin ya ba wa daliban mazabarsa 628 tallafin karatu a Jami’ar Bayero ta Kano (BUK).

Aminiya ta gano cewa duk dalibin mazabar da ya rabauta ya samu tallafin N50,000 daga dan majalisar.

Da yake bude rabon tallafin, shugaban ma’aikatan Sanata Barau, Farfesa Muhammad Ibn Abdullahi, ya ce dan majalisar ya yi haka ne domin ba wa daliban mazabarsa damar neman ilimi a manyan makarantu.

Kakakin Mataimakin Shugaban Majalisar, Ismail Mudashir, ya ce daliban mazabar Kano ta Arewa da ke sauran manyan makarantu a fadin Najeriya ma za su amfana da tallafin.

Don haka ya bukaci daliban da suka amfana da su yi amfani da abin da aka ba su ta hanyar da ta dace sanna su kara jajircewa wajen neman ilimi.Wani dalibin aji hudu a jami’a da ya samu tallafin, Adama Iliyasu Rabiu, ya yaba wa dan dan majalisar tare da rokon Allah Ya saka masa.

(AMINIYA)


Popular posts from this blog

Yanzu - Yanzu: Bankuna Zasu Karbi Tsofaffin Kudi Ko da Bayan Karewar Wa'adi - Emefiele

Zababben Gwamnan Kano Ya Kafa Kwamitin Karbar Mulki