An Kawo Karshen Rashin Fahimtar Juna Tsakanin Ma'aikatar Al'adu Da Hukumar Tace Finafinai Ta Kano

A ranar Juma'a ne kwamishinan shari'a na Jahar Kano,  Barista Haruna Isah Dederi ya shirya wani taro irinsa na farko tsakanin kwamishinan raya al'adu da yawon rude ido ta Jahar Kano Hajiya ladidi Garko da Kuma Manajin Darakta na hukumar kula da masu yawon Bude ido Alh. Tukur Bala Sagagi tare da Shugaban Hukumar tace Fina-finai da Dab'i ta Jahar Kano Alh. Abba El-mustapha

Shugaban Hukumar Tace Finafinai da Dab'i ta Jahar Kano, Abba El-Mustapha, Shi ne ya walllafa labarin a shafinsa na #Facebook 

El-Mustapha ya ce an shirya taron ne  domin nemo bakin zaren rashin fahimtar dake faruwa wajen gudanar da aiyukan daya rataya a tsakanin hukumomin biyu akan masu sana'ar gidajen kallo tare da masu gidajen shirya tarur-ruka (event centers). 

Tunda farko dai kwamishinan shari'ar na Jahar Kano Barista Haruna Isah Dederi yayi dogon jawabi dangane da hakki tare da aiyukan da rataya a kan dukkannin hukumomin biyu inda bayan doguwar tattaunawa tsakankanin shuwagabannin Hukumomin biyu aka sami daidaito dangane da shawarar da Shugaban Hukumar tace Fina-finai ta Jahar Kano Alh. Abba El-mustapha ya kawo na araba aiyukan gida biyu inda kowacce hukuma zata dauki daya danta maida hankali akan sa.

Hajiya Ladidi Garko ita ce kwamishiyar hukumar lura da al'adu tare da yawon bude ido ta Jahar kano a inda a madadin hukumar tayi na'am da hakan la'akari da hakan kwamishina shari'a na Jahar Kano Barista Haruna Isah Dederi ya tabbatar da bawa ko wacce hukumar aiki daya dan ta maida hankali akai domin cimma nasarar da gobnati tasa agaba

A yanzu haka dai, Hukumar tace Fina-finan da Dab'i ta Jahar Kano ita ce keda alhakin kula da aiyukan masu sana'ar gidajen kallo(Viewing Centers), Inda Hukumar kula da al'adu tare da masu yawon buda ido keda alhakin kula da aiyukan masu gidajen shirya tarur-ruka (Event centers).

Ana su jawabansu Daban-daban,  shuwagabannin sun nuna farin cikin su dangane da yadda ma'aikatar shari'ar ta kawo karshen takaddamar tare da samun nasarar da taron yayi na cimma matsaya 


Popular posts from this blog

Yanzu - Yanzu: Bankuna Zasu Karbi Tsofaffin Kudi Ko da Bayan Karewar Wa'adi - Emefiele

Zababben Gwamnan Kano Ya Kafa Kwamitin Karbar Mulki