2023: Idan Na Zama Gwamna Zan Bawa Kananan Hukumomin 'Yancinsu - Gawuna

Mataimakin gwamnan jihar Kano kuma dan takarar gwamna na jam’iyyar  APC, Dr. Nasiru Yusuf Gawuna ya yi alkawarin baiwa kananan hukumomin jihar ‘yancin cin gashin kansu idan aka zabe shi a matsayin gwamna.

Ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da shirin gidan talabijin na NTA cikin shirin "The Balot".

"Ƙananan Hukumomin wani bangare ne na gwamnati kuma su ne matakin kusa da jama'a wanda ke taimakawa hatta ci gaba da rarraba albarkatu da ayyuka".

"A matsayina na tsohon shugaban karamar hukumar na san abin da ya shafi gudanar da mulkinta".

Lokacin da nake shugaban karamar hukuma, an ba ni cikakkiyar dama nayi  aiki. Hakan ya sa muka samu nasarori da dama don haka idan aka zabe mu a matsayin Gwamna zan mayar da martani kamar yadda Gawuna ya bayyana”.

A sanarwar da babban sakataren yada labaransa, Hassan Musa Fagge ya fitar, Gawuna Ya kara da cewa shi ne wanda ya fi cancanta kuma a shirye ya ke ya zama Gwamnan Jihar Kano bayan ya yi aiki da gwamnatocin da suka gabata kuma ya samu kwarewa da dama, duk da haka ya ba da tabbacin karfafa nasarorin da suka samu a wani bangare na manufofin ci gaba.

Gawuna ya kuma bukaci masu kada kuri’a da su guji tashin hankali su gudanar da rayuwarsu cikin kwanciyar hankali da lumana a lokacin zaben.


Popular posts from this blog

Yanzu - Yanzu: Bankuna Zasu Karbi Tsofaffin Kudi Ko da Bayan Karewar Wa'adi - Emefiele

Zababben Gwamnan Kano Ya Kafa Kwamitin Karbar Mulki