DSS ta kama mutum biyu a Kano kan zargin tayar da rikici

 


Hukumar tsaro ta farin kaya DSS ta ce ta kama wasu mutane biyu da take zargi da tunzura mutane domin tayar da hankali a jihar Kano gabanin zaÉ“en gwamna da na ‘yan majalisun jiha da za a yi a ranar Asabar.

 

Cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na Twitter hukumar ta DSS ta ce mutanen sun naÉ—i hoton bidiyo ne da suke bayanan tunzura jama’a a cikinsu, sannan suka riÆ™a wallafa shi a shafukan sada zumunta.

 

Ta kuma wallafa sunayen Sharu Abubakar TaÉ“ule mai shekara 37 a duniya, da kuma Isma’il Iliyasu Mnagu mai shekara 51 a matsayin waÉ—anda ta kama.

 

“Cikin waÉ—annan saÆ™onnin masu haÉ—ari, sun nuna jam’iyyar siyasar da suke goyon baya kuma suka yi kira ga magoya bayansu su kai wa abokan hamayyarsu hari duk inda suka gansu.

 “WaÉ—anda ake zargin sun yi kira da a kai wa jami’an tsaro hari yayin zaÉ“en gwamnoni da na ‘yan majalisar jihohi da za a yi a ranar Asabar.


“Wata jam’iyyar siyasa a Kano na barazanar shirya zanga-zanga a sakamakon shirin kai hare-haren,” in ji hukumar ta DSS.


Sanarwar ta Æ™ara da cewa jam’iyyar siyasar ta shirya kutsawa ofisoshin wasu hukumomin tsaro a ranar 16 ga watan Maris a matsayin nuna goyon baya ga waÉ—anda ake zargin.“Yayin da hukumar ke sanar da mutane kan wannan haramtaccen mataki, ta kuma yi kira ga jam’iyyar da ta dakatar da wannan lamari, ko kuma ta shirya yaba wa aya zaÆ™inta.


“DSS ba za ta zuba ido tana kallon mutane suna tunzura al’umma ba su tayar da hankali da rashin tsaro a jiha ba.”


Sanarwar DSS ta ce za ta haɗa hannu da sauran hukumomin tsaro domin tabbatar da an samar da cikakken tsaron da zai bayar da damar da gudanar da zaɓe mai inganci a jihar.


Baya ga Kano hukumar tsaron ta kama wasu mutane da ke irin wannan kiraye-kiraye a wasu jihohi a faɗin ƙasar.


Hukumar ta shawarci jam’iyyun siyasa a fadin Najeriya da su gargadi mabiyansu su zama masu bin doka da oda, domin tabbatar da dimokuraÉ—iyya ta samu wurin zama yadda ya kamata


BBC

Popular posts from this blog

Yanzu - Yanzu: Bankuna Zasu Karbi Tsofaffin Kudi Ko da Bayan Karewar Wa'adi - Emefiele

Zababben Gwamnan Kano Ya Kafa Kwamitin Karbar Mulki