‘Kusan Sau Miliyan 13 Aka Yi Yunkurin Yi Wa Najeriya Kutse Yayin Zaben Shugaban Kasa’


 Gwamnatin Tarayya ta ce akalla sau 12,988,978 aka yi yunkurin yin kutse a shafukan intanet na Najeriya yayin zaben Shugaban Kasa da na ’yan Majalisun Tarayya da aka yi a ranar 25 ga watan da ya gabata.

Hare-haren, a cewar gwamnatin an kai su ne daga ciki da wajen kasar, kuma an yi su ne kan shafukan gwamnati, kusan sau 1,550,000 a kullum.

Ministan Sadarwa, Isah Ali Pantami ne ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa ranar Talata.

To sai dai ya ce yunkurin kutsen ya yi tashin gwauron zabo zuwa sau 6,997,277, a ranar zaben Shugaban Kasa ta Asabar.

Ministan ya kuma ce ma’aikatarsa ta kafa wani kwamitin yaki da irin wadannan hare-haren, kuma ya fara aiki ne ranar 24 ga watan na Fabrairu, sannan ya kammala ranar 28.

AMINIYA

Popular posts from this blog

Yanzu - Yanzu: Bankuna Zasu Karbi Tsofaffin Kudi Ko da Bayan Karewar Wa'adi - Emefiele

Zababben Gwamnan Kano Ya Kafa Kwamitin Karbar Mulki