Tinubu Ya Yi Alawadai Da Harin 'Yan Bindiga A Zamfara, Kano Da Katsina is a Tare Da Jajantawa Wadanda Abun Ya Shafa

Tinubu ya kuma yi ta'azziya ga iyalan Abacha da na Sheikh Gumi 

Zababben shugaban kasa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya yi Allah-wadai da hare-haren da ‘yan bindiga da wasu da ba a san ko su wanene ba suka kai a karamar hukumar Maru ta jihar Zamfara da kuma garin Maigari na karamar hukumar Rimin Gado a jihar Kano a karshen mako.
Rahotanni sun ce an kashe jami’in ‘yan sanda na Dibision (DPO), sufeto ‘yan sanda da dan banga a harin da ‘yan bindiga suka kai a Zamfara. A harin na Kano wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun shiga gidan wani basarake inda suka harbe shi har lahira.

A cikin wata sanarwa da ofishin yada labaran sa ya fitar a ranar Litinin, Tinubu ya ce harin da aka kai a garin Maru bayan an samu zaman lafiya a jihar Zamfara, abin tunatarwa ne cewa akwai bukatar a kara kaimi domin murkushe ‘yan bindiga da ‘yan ta’adda gaba daya.

“A matsayinmu na kasa dole ne mu hada kai domin mu fatattaki wadannan ‘yan kasuwa na mutuwa da ta’addanci gaba daya, kashe-kashen rashin tunani da ta’addanci irin wannan bai kamata ya zama wani wuri a kasarmu ba,” inji shi.

Zababben shugaban kasar ya jajantawa Sufeto-Janar na ‘yan sanda, Usman Alkali Baba, da gwamnatin jihar Zamfara da iyalan jami’an tsaron da abin ya shafa bisa rasuwar.

Tinubu ya kuma bukaci a gudanar da bincike kan kisan Hakimin Maigari a Jihar Kano, wanda shi ne mahaifin shugaban karamar hukumar Rimin Gado, Munir Dahiru Maigari.

Ya mika ta’aziyyarsa ga shugaban karamar hukumar, gwamnatin jihar Kano da iyalan mamacin bisa mummunan kisan da aka yi wa shugaban al’umma.

A cikin sakon ta’aziyya daban-daban, zababben shugaban kasar ya jajantawa fitaccen malamin nan Sheikh Ahmad Gumi da ya rasa mahaifiyarsa tsohuwa da kuma iyalan marigayi Janar Sani Abacha bisa rasuwar dansu Abdullahi.

“Yana shafar rabuwa da masoyi komai yanayi da shekaru, ba za mu iya kokwanton nufin Allah ba sai dai kawai mu yi addu’a Allah Ta’ala ya ba su hutun dawwama, ya kuma ba mu karfin gwiwar jure wa rasuwarsu,” inji shi.

Zababben shugaban kasar ya jajantawa dukkan iyalan da suka rasa ‘yan uwansu tare da addu’ar Allah ya jikan wadanda suka rasu.


Popular posts from this blog

Yanzu - Yanzu: Bankuna Zasu Karbi Tsofaffin Kudi Ko da Bayan Karewar Wa'adi - Emefiele

Zababben Gwamnan Kano Ya Kafa Kwamitin Karbar Mulki