Hajjin Bana: Hukumar Alhazai Ta Kano Ta Yi Kira Ga Maniyyata Aikin Hajin Bana, Da Su Cika Kudinsu Ya Kai Miliyan Biyu Da Dubu Dari Diya
Sakaaren zartarwa na hukumar, Ambasada Muhammad Abba Danbatta ne, yayi wannan kiran a ranar Asabar cikin wata sanarwa da ya bayar.
Danbatta yace tun a ranar 28 ga watan da ya gabata ne wa’adin
da hukumar kula da aikin hajji ta kasa (NAHCON) ta bayar ga hukumomin kula da
jin dadin alhazai na jahohi, na cika kudaden adadin kujerun da aka basu ya kare,
inda suka nemi alfarmar kara wa’adi domin bawa maniyyatan dama
“Bayan sanya hannu kan yarjejeniya ta gudanar da aikin Hajjin
2023 ta umarci jahohi da su kai a kalla daga miliyan daya da dubu dari biyar
zuwa sama”
Sakataren zartarwar wanda ya bayyana cewa tun a kwanakin
baya, bayan da suka dawo daga kasa Indonesiya wajen taron masu ruwa da tsaki
kan harkokin aikin Hajji na kasa da kasa, yace a lokacin hukumomi sun fito da
sababbin dokoki wanda aka umarci hukumomin alhazai na johohi su fadawa
maniyyatansu dasu cika kudinsu ya kai naira miliyan biyu da dubu dari biyar
kafin a ayyana kudin kujerar
“Wannan ne ya sa muke kira ga maniyyata wadanda suka biya ko
aka biya musu, dasu cika kudinsu ya kai naira miliyan biyu da dubu dari biyar
kafin a tantance abun da za a biya”