Search This Blog

Wednesday, 4 January 2023

BIDIYO: Isowar Bola Tinubu filin wasa na Sani Abacha


Duk wanda ba shi da kuri'a ba zai yi zabe ba - INEC


Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa ta jaddada cewa babu wanda zai kada kuri'a a zaben 2023 mai zuwa sai mai katin zabe 

Jami'in zabe na karamar hukumar Gwarzo Mal.Bello Ismail ya bayyana haka a lokacin taron masu ruwa da tsaki a ofishinsa. 

Bello Ismail ya kara da cewa an samar da sabbin rumfuna saba'in da uku domin rage cinkoso da masu kada kuri'a sama da dubu daya a Gwarzo,Getso,Kutama,Lakwaya,Mada da ,Unguwar tudu dake karamar hukumar Gwarzo.

 Jami’in zaben ya kuma kara da cewa INEC za ta kai unguwanni goma na kananan hukumomin domin rabon kaya daga ranar 6 ga watan Janairu zuwa 15 ga watan Janairu.

Da yake jawabi a wajen taron sakataren jam’iyyar A.P.C. Samaila Abdullahi ya shawarci hukumar zabe da ta kaucewa tarin pVC na uku.

A nasu jawabin jami'in 'yan sanda DSS, da Civil Defence kira suka yi INEC da su bayar da motocin daukar kayan zabe da jami’ai domin kaisu wuraren da ya dace. 

Sauran wadanda suka halarci taron sun hada da wakilan babban limami, hakimin gundumar, shugabannin jam'iyya da dai sauransu.

Hukumar Asibitin Koyarwa na Aminu Kano ta yi Allah wadai kan sakacin da wani likita ya yi lokacin da yake kula da lafiyar wani jariri

 Jaririn wadanda aka haifa makon da ya gabata ya zo da wata matsala wadda ta bukaci yi masa gwaji ta hanyar daukar jininsa a inda likitan ya shiga dimuwa wanda ya haifar da abin da ya faru.

A cikin sanarwar da shugabar sashen hulda da jama’a ta Asibitin Hajiya Hauwa Muhammad Abdullahi ta sanyawa hannu, Hukumar Asibitin ta girgiza da Jin Wannan mugun labari Wanda a shekaru  talatin da uku da kafuwar Asibitin Hakan bai tabar faruwa ba. 

Hukumar tana jajentawa iyayen wannan jariri bisa ga abin da ya faru.

A Kuma halin da ake ciki an mika wa kwamitin da yake bibiyar matsalolin badakala da sakacin aiki wato (Committee on Negligence of Duty)domin yin zurzurfan bincike tare da daukan mataki akan duk Wanda yake da hannu a cikin wannan sakaci da ya faru.

Shugaban Asibitin Koyarwan farfesa Abdurrahman Abba Sheshe ya yi kira ga duk Maras lafiya ko Yan Uwan marasa lafiyan da su ga ba su gamsu da yadda ake kula da lafiyar su ko ta Yan Uwansu ba ,da su gaggawa wajen sanar da hukumar Asibitin ta Hanyar jami'anta wadanda ake kira da( Servicom Desk Officers).

Ya ce Asibitin yana da  irin wadannan jami'i kimanin Arbanin , wadanda aka raba su a sassan gudanar da aiki daban daban a cikin Asibitin.

Baya ga sashen hurda da Jama'a da wajen Matron Matron na dakin kwanciya wadanda suke aiki tsawon awa ashirin da biyar.

Farfesa Abdurrahman,ya kara da cewa ta Hanyar mika korafi ne kawai hukumar Asibiti za ta iya kamowa tare da hukumta masu laifi.

Ya Kuma Yi kira ga Mahaifin wannan jariri da ya    taimaka wajen isar da makamancin wannan korafi ga kwamitin binciken ko Kuma sashen hurda da Jama'a na Asibitin

Tuesday, 3 January 2023

Tinubu ya ziyarci Sarkin Kano tare da neman addu’a

Sarkin Kano Alh Aminu Ado Bayero ya yi kira ga al’ummar jihar da su ci gaba da mutunta shugabanni a lokacin zabe domin kara inganta zabe mai inganci don ci gaban kasa. 

Sarkin ya bayyana haka ne a lokacin da ya karbi bakuncin dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Apc, Asiwaju bola Ahmad tunibu a fadarsa, 

Sarkin wanda ya bayyana Kano a matsayin cibiyar zabe ya yi kira ga jama'a da su yi amfani da kwarewarsu wajen zaben wadanda suka yi shugabancesu don zama babban fa'ida ga al'umma 

Tun da farko dan takarar shugaban kasar Cif Bola Ahmad Tunibu ya ce ya je jihar Kano ne domin kaddamar da yakin neman zabensa a Arewa maso Yamma kuma ya nemi addu'ar sarakuna da kuma al'ummar jihar 

 A yayin ziyarar dan takarar shugaban kasa Bola Ahmad Tunibu ya samu rakiyar gwamnan jihar Dr. Abdullahi umar Ganduje, da mataimakinsa Dr. Nasiru yusif Gawuna, gwamnan jihar Zamfara, Sanata barau jibrin, shugaban jam'iyyar na jiha Abdullahi Abbas, tsohon gwamnan jihar. s, da manyan jami'an gwamnatin tarayya na tarayya.

Hotuna: Bola Tinubu ya ziyarci Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero a fadarsa


Tinubu ya kai ziyarar ban girma ga Sarkin Kano, inda ya nemi sanya albarka gabanin zaben Shugaban Kasa A 2023 
Gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya Jagoranci Dan Takarar Shugabancin Kasa Na Jam'iyyar APC, Alhaji Asiwaju Bola Ahmed Tinubu. domin kai ziyara ga Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero.

Matawalle ya dakatar da yakin neman zaben APC a Zamfara

Gwamna Bello Mohammed Matawalle ya dakatar da yakin neman zaben Jam’iyyar APC a Jihar Zamfara har zuwa ranar 18 ga watan Janairu da muke ciki.

Rohotanni sun bayyana cewa kwamitin yakin neman zaben jam’iyyar ya dakatar da harkkokin kamfe din gwamnan ne don mayar sa hankali kan zaman lafiya a jihar.

“Na yi alkawarin mayar da hankali wajen dawo da zaman lafiya a mulkina na biyu a Jihar Zamfara,” cewar Matawalle.

Aminiya ta ruwaito cewa Ya bayyana haka ne a lokacin da jam’iyyar ta kaddamar da yakin neman zabensa a Karamar Hukumar Kaura Namoda, a ranar 27 ga watan Disamba, 2022.

Matawalle dai ya nada tsohon gwamnan jihar, Abdulaziz Yari a matsayin shugaban kwamitin yakin neman zabensa.

A nasa bangaren, tsohon gwamnan jihar ya ce matsalar tsaro za ta inganta idan Matawalle ya sake darewa kujerar mulkin jihar a karo na biyu.

Yari, wanda ya jagoranci kwamitin yakin neman zaben APC zuwa kamfe din jam’iyyar ya ce zai goyi bayan takarar Matawalle dari bisa dari.

Kungiyoyi da dama sun so daukata amma na yi wa Al-Nassr alkawari - Ronaldo


Cristiano Ronaldo ya ce kungiyoyin kwallon kafa da dama a sassan duniya sun nuna sha’awar daukar sa amma ya yanke shawarar sanya wa Al-Nassr hannu.

A lokacin da Al-Nassr ta gabatar da shi a matsayin dan wasanta a gaban dubban magoya bayan kungiyar a ranar Talata, Ronaldo ya bayyana cewa kungiyoyi a nahiyar Turai da Brazil Amurka da Australia da Portugal sun nemi su dauke shi amma ya zabi zuwa Saudiyya.

Jaridar Aminiya ta rawaito Ronaldo na cewa “Kamar yadda na fada a baya wannan dama ce a gare ni ba wai a harkar kwallon kafa ba, dama ce da zan sauya tunanin matasa masu tasowa.

“Kungiyoyi da dama daga Nahiyar Turai da Brazil da Amurka da Australia da ma Portugal son so dauka ta amma na yi wannan kungiya alkawari.


“Na san abin da nake so da wanda ba na so, kuma wannan babban kalubale ne a gare ni na zuwa wannan kasa, ba don komai ba sai don na kara samun ilimi.

“Ina son sabon yanayi, kasa don cimma wani buri na daban tare sa Al-Nassr, wannan shi ne dalilin da ya sa na rungumi wannan dama,” in ji Ronaldo.

Ronaldo, dan shekara 37 a duniya, ya rattaba hannun zama a Al-Nassr na tsawon shekara biyu da rabi bayan raba gari da Manchester United a watan Nuwamban 2022.

Tinubu ba zai ci amanar ’yan Arewa ba, ya dace ya yi mulki – Gwamna Badaru




Gwamnan Jihar Jigawa, Muhammadu Badaru Abubakar, ya karyata rade-radin da ake yi na cewa dan takarar Shugaban kasa na APC, Ahmad Bola Tinubu zai yi butulci ga Yan arewa idan ya ci zabe


Ya yi ikirarin cewa makusantan dan takarar shugaban kasa sun nuna shi ba maciya amana ba ne. Kuma sun tabbatar da shi a matsayin wanda ba mai kabilanci ba ne kuma mai kishin addini.”

Gwamnan jihar Jigawa ya kara da cewa duk abin da Bola Tinubu ya yi a burinsa na zama shugaban kasa, ya yi tare da cikakken masaniyarsa d Ganduje da Nuhu Ribadu, mutanen da suka yi fice wajen kishin kasa.


Muhammadu Badaru wanda ya  tuno kan yadda Malamai suka tursasa shi ya janye aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban kasa a Kudu, ya ce zabin Bola Tinubu an yi shi ne da duk wani mai ruwa da tsaki a harkar Nijeriya.

“Magana game da lafiyar kwakwalwarsa da lafiyarsa, ziyarar da muka yi a Makka kwanan nan a Ummara inda Tinubu ya yi tafiya mai nisa ba tare da shiga mota ba da kuma yadda ya yi dawafi  da Sa'ayi ya nuna cewa ba shi da wata matsala ta rashin lafiya 

"Ya kamata 'yan Najeriya su sani cewa zamanin amfani da ra'ayi, kabilanci, da kishin addini ya kare, duk tattaunawa da zarge-zarge marasa tushe. ”
(Daily Post) 

Yau sabuwar majalisar Amurka za ta yi zamanta na farko

A yau Talata sabuwar majalisar dokokin Amurka za ta fara aiki inda dan Republican Kevin McCarthy zai nemi zama shugaban majalisar wakilai.

Bayan zaben rabin wa’adi da a aka yi a watan Nuwamba, ‘yan Republican sun karbe ragamar shugabancin majalisar wakilai amma da dan kankanin rinjaye.

Majalisar dokokin Amurkar a wannan ta rabu gida biyu, inda ‘yan Democrat suka ci gaba da rike shugabancin majalisar dattawa yayin da ‘yan Republican suke karbe majalisar wakilai.

Wani abu da zai fi jan hankali a yau shi ne yadda ‘yan Republican za su zabi shugaban majalisar ta wakilai.

McCarthy na fatan ganin ya gaji Nancy Pelosi ‘yar Democrat amma kuma yana fuskantar kalubalen rashin samun goyon baya - har daga abokansa.

Wannan shi ne karon farko cikin shekaru 100 da dan takarar neman shugabancin majalisar wakilai ya gaza samun goyon baya daga wasu ‘yan jam’iyyarsa.

Tsohon Shugaban Amurka Donald Trump na goyon bayan McCarthy.

Dan majalisar wakilai Andy Riggs na jihar Arizona da Steve Scalia mai wakiltar Louisiana na daga cikin ‘yan Republican din da suke adawa da McCarthy.

Bayanai sun yi nuni da cewa daukacin ‘yan Democrat ba za su goyi bayan McCarthy ba, abin da ke nufin dole sai dai ya mayar da hankalinsa kan kuri’un ‘yan Republican.

Zamu duba yiwuwar taimakawa Burundi da man Fetur - Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce ฦ™asar za ta duba buฦ™atar taimakon makamashi, musamman man fetur da gwamnatin ฦ™asar Burundi ta gabatar wa ฦ™asarsa.

Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ฦ™asar Femi Adeshina ya sanya wa hannu, shugaba Buhari ya yi alฦ™awarin ne bayan karษ“ar baฦ™uncin ministan kuษ—i , kasafi da tsare-tsare na ฦ™asar Burundi Audace Niyonzima a fadarsa da ke Abuja.

Sanarwar ta ce Buhari ya tabbatar wa da mista Niyonzima cewa Najeriya za ta taimaka wa ฦ™asar Burundi ta hanyoyi da dama ฦ™arฦ™ashin inuwar zumunci da 'yan uwantaka da ke tsakanin ฦ™asashen Afirka.

Shugaba Buhari ya ฦ™ara da cewa ya san yadda ฦ™asa ke ji musamman idan tana fama da ฦ™arancin makamashi, tare da alฦ™awarta cewa zai tura batun ga babban kamfanin mai na ฦ™asar NNPC domin duba buฦ™atar.

Buhari ya ce a yanzu batun zaษ“en ฦ™asar, da batun saukarsa daga mulki ne a gabansa, tun da dai ya yi wa'adi biyu da kundin tsarin mulkin ฦ™asar ya ba shi dama.

A nasa ษ“angare ministan na Burundi ya yi wa ฦ™asar fatan alkairi a manyan zaษ“ukan da za ta gudanar cikin wannan shekara.





Kada Ku Nemi Na Saki 'Yan Daba - Muhuyi Magaji Ya Gargadi 'Yan Siyasa

Governor Yusuf Celebrates ATM Gwarzo at 66

Kano State Governor, Alhaji Abba Kabir Yusuf, has congratulated the former Deputy Governor and State Coordinator of Arewa For As...