Search This Blog

Tuesday, 1 September 2026

Jiga-jigan NDC magoya bayan Gawuna na shirin komawa APC

……Sun kai ziyarar nuna goyon baya ga Gwamna Yusuf da Mataimakinsa

Wasu daga cikin jiga-jigan jam’iyyar NDC da ake alakanta su da tsohon Mataimakin Gwamnan Kano, Nasiru Yusuf Gawuna, sun fara shirye-shiryen komawa jam’iyyar APC.

Tawagar ta kai ziyarar nuna goyon baya ga Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, da Mataimakinsa, Murtala Sule Garo, a wannan Talatar da yamma.

Tawagar, wadda babban aminin Gawuna, Hon. Muhammad Badaru Umar, ya jagoranta, ta ƙunshi Hon. Ali Datti Yako, Mataimakin Shugaban NDC na Jihar Kano; Hon. Mansur Isa Gawuna; Hon. Uba Tanko Mijinyawa (Uba Danzainab); Hon. Aminu Umar Faruk; Hon. Sani Jibrin; Hon. Salisu Muhammad; Hon. Musa Sani Indabo; Hon. Muhammad Kabir Bala; Hon. Hassan Abba Abdullahi da Comrade Abdurrahman Muhammad.

Da yake bayani kan dalilin ziyarar, Hon. Muhammad Badaru Umar ya ce ƙaunar ci gaban Jihar Kano ce ta sa suka ga ya dace su gana da Gwamna Abba Kabir Yusuf.

Ya ce suna son ganin Kano ta ci gaba, yana mai bayyana ziyarar a matsayin wani ɓangare na tuntuba da tattaunawa kan makomar siyasa da ci gaban jihar.

A nasa bangaren, Hon. Ali Datti Yako ya ce kowa ya san irin ƙoƙarin da Gwamna Abba Kabir Yusuf ke yi wajen sauya fasalin Kano.

“Dukkanmu mun san cewa Gwamna Yusuf yana aiki tuƙuru wajen sauya fasalin Kano,” in ji Ali Datti Yako.

Ziyarar na zuwa ne a daidai lokacin da ake samun sauye-sauyen siyasa a Kano, yayin da manyan ’yan siyasa ke ci gaba da sake tsara matsayinsu gabanin zaɓen 2027.

Ana ganin shirin komawar waɗannan jiga-jigai zuwa APC a matsayin wani babban sauyi da zai iya ƙara wa jam’iyyar ƙarfi a Kano.

Sai dai, kawo yanzu, tawagar ba ta bayyana takamaiman ranar da za ta ayyana komawarta APC a hukumance ba.


Kada Ku Nemi Na Saki 'Yan Daba - Muhuyi Magaji Ya Gargadi 'Yan Siyasa

Jiga-jigan NDC magoya bayan Gawuna na shirin komawa APC

……Sun kai ziyarar nuna goyon baya ga Gwamna Yusuf da Mataimakinsa Wasu daga cikin jiga-jigan jam’iyyar NDC da ake alakanta su da...