A nasa ra'ayin, ษ“ata kudi ne kawai gwamnati ke yi wajen tafiyar da majalisun biyu.

Najeriya na da zauruka biyu na majalisar dokokin tarayya, wadda ta haษ—a da Majalisar Dattaijai mai wakilai 109.

Sai kuma Majalisar Wakilan Tarayya, wadda take da wakilai 360.

A tattaunawarsa da BBC, Shekarau ya ce kamata ya yi Najeriya ta rungumi tsarin mulki irin na Birtaniya, wanda aikin ฦดan majalisar bai wuce na wucin-gadi ba.

Sai dai Shekarau ya ce gyara irin tsarin na majalisar dokoki a Najeriya abu ne mai matuฦ™ar wahala domin sai an yi gyara a kundin tsarin mulkin ฦ™asar.

Kuma cewarsa, akwai yiwuwar ฦดan majalisar dokokin, waษ—anda dole ne sai an samu amincewarsu kafin a iya sauya dokar, ba za su goyi bayan canza ta ba.

...

Sanata Shekarau ya ce “kowane daga cikin ฦดan majalisar tarayya 469, an ba shi dama ya ษ—auki ma’aikata guda biyar.”

Ya kuma ฦ™ara da cewa “kowane kwamitin majalisar yana da ma’aikata aฦ™alla biyar.”

"Ko kuษ—in da ake kashewa kan irin waษ—annan ma’aikata abu ne da ya kamata a duba." - In ji shi.

Shekarau ya ce ana kafa kwamitoci a majalisar dokokin ta tarayya waษ—anda ba a buฦ™ata, kuma ษ“arnar kudi ne kawai da lokaci.

Majalisar Dattijan ita ce zaure mafi ฦ™oluluwa a batun yin dokoki a ฦ™asar, inda Majalisar Wakilai ke biye mata.

An dai sha tafka mahawara kan yawan kuษ—in da gwamnati ke kashewa a ฦ™asar wajen tafiyar da gwamnati, wani abu da ake ganin za a iya yin gyara a kai, ta yadda ฦ™asar za ta iya amfani da kuษ—in wajen samar da kayan more rayuwa ga sauran al’ummar ฦ™asar sama da miliyan 200.

Sai dai har yanzu babu wani yunฦ™uri da aka yi a hukumance wajen tabbatuwar hakan.

Ibrahim Shekarau na daga cikin ฦดan majalisar dokoki na tara, sai dai ba zai kasance a majalisa ta 10 da za a ฦ™addamar ba cikin watan Yuni

BBC