Search This Blog

Friday, 19 May 2023

Yajin aikin likitocin Najeriya ya jefa majinyata a halin kunci


Tarin asibitoci a sassan Najeriya sun fada halin garari saboda karancin likitocin da ke duba marasa lafiya sakamakon yajin aikin gargadin da kungiyar likitoci masu neman kwarewa ta NARD ke yi kasar, inda bayanai ke nuna cewa tuni majinyatan da ke bukatar kulawar gaggawa suka sauya akalar duba lafiyarsu zuwa asibitoci masu zaman kansu sakamakon cunkoson da ake gani a asibitocin gwamnati.


A larabar da ta gabata ne mambobin kungiyar ta NARD suka tsunduma yajin aikin a wani yunkuri na nuna bacin ransu game da rashin cika musu alkawuran da ke tsakaninsu da gwamnati ciki har da karin albashi da akalla kasha 200.

Sai kuma yunkurinsu na kalubalantar kudirin dokar da ke gaban Majalisar kasar da ke shirin kange daga fita ketare don yin aiki har sai bayan sun yi aikin shekaru 5 a cikin Najeriya.

Haka zalika kungiyar likitocin na bukatar gwamnatin Najeriyar ta biya mambobinta bashin kudaden albashin da suke binta tun shekarar 2015 baya daukar tarin ma’aikatan bangaren lafiya saboda karancin ma’aikata a sashen.

Cikin kwana 3 da faro yajin aikin, tuni marasa lafiya suka fara ji a jikinsu saboda rashin likitocin da ke duba lafiyarsu, musamman a biranen da suka kunshi Abuja da Lagos da kuma Kano.

Yanzu haka dai gwamnati Najeriya ta bakin Chris Ngige ta fara tattaunawa da shugabancin kungiyar ta NARD ko da ya ke kungiyar ta musanta.

RFI 

Thursday, 18 May 2023

Ba Ni Da Gida A Kasar Waje - Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya ce ba shi da gida a wajen Najeriya.

Ya bayyana haka ne a lokacin da yake karbar wasikar girmamawa daga jakadan Birtaniya a Najeriya, Richard Hugh Montgomery da takwaransa na Sri Lanka Velupillai Kananathan a fadar shugaban kasa a ranar Alhamis.

Buhari ya ce “A daya daga cikin ganawarmu da Sarki Charles III, ya tambaye ni ko ina da gida a Ingila, amma na shaida masa cewar ba ni da gida a wajen Najeriya.”

Ya kara da cewa, an shafe shekaru da yawa ana musayar al’adu ta hanyar ilimi da horarwa tare da Birtaniya, inda ya nuna cewa ya samu horon soji a makarantar Mons Officer Cadet da ke Aldershot a Ingila 1962 zuwa 1963.

Buhari ya shaida wa jami’in diflomasiyyar Birtaniya cewa kyakkyawar fahimtar banbance-banbancen al’adu, da mutunta cibiyoyi shi ne ya share fagen yawan nasarorin da Birtaniya ta samu.

Ya ce jami’an diflomasiyyar da suka gabata sun kulla alaka da Sarkin Musulmi, Sarkin Kano, Shehun Borno da Sarkin Ilorin.


Shugaba Buhari ya kuma umarci Montgomery da ya ci gaba da kiyaye kyawawan manufofin diflomasiyya, kamar yadda magabata suka yi, ta hanyar mutunta cibiyoyin gargajiya a Najeriya.

Ya ce dangantakar da ke tsakanin Birtaniya da Sri Lanka za ta kara inganta tare da la’akari da al’adun gida, sarakunan gargajiya, da sauransu.

“Ina jin dadin yadda ake girmama sarakunanmu da hukumominmu, duk da sauyin zamani, ilimi, da karuwar son abin duniya.

“Akwai abubuwa da yawa da za mu koya daga al’adunmu, kuma cibiyoyin gargajiya su ne masu kula da su, kuma ya kamata kowa ya mutunta su,” in ji Buhari.

Ya shaida wa jakadan Birtaniya cewa, huldar diflomasiyyar da ta shafe shekaru da dama tana ci gaba da dorewa bisa mutunta al’adu za ta kara karfi.

A nasa bangaren, Montgomery, ya ce Birtaniya a kodayaushe tana girmama Najeriya da al’adunta, yayin da ya bayyana fatan alheri ga Sarki Charles III, a daidai lokacin da Najeriya ke shirin mika mulki a ranar 29 ga watan Mayun 2023.

Shi ma a nasa jawabin, jakadan Sri Lanka ya shaida wa shugaba Buhari cewa kasar za ta ci gaba da bai wa sojojin Najeriya kwarewa da gogewa wajen yaki da ta’addanci.
AMINIYA 

El-Rufai Zai Rushe Kamfanoni 9 Mallakar Makarfi

Gwamna Nasir El-Rufai na Jihar Kaduna, ya soke lasisin mallakar kamfanoni tara na tsohon gwamnan jihar, Sanata Ahmed Muhammed Makarfi.

An kuma shirya rushe kamfanoni tara mallakar tsohon gwamnan Jihar.

Aminiya ta fahimci cewa an kai sanarwar janye  hakkin mallaka ga jami’an kamfanonin da abin ya shafa.

Sanarwar ta fito ne daga Daraktan kamfanin rake da ke lamba 11 a Murtala Square, Alhaji Ibrahim Makarfi wanda ya mayar da martani da cewa, “lauyoyinmu za su mayar da martani kan kwace hakkin mallakar kamfanonin”.

Sai dai da yake mayar da martani kan soke hakkin mallakar a wani sakon da ya aike wa Sanata Makarfi, ya tabbatar da samun wasikun soke kamfanonin har guda tara.

Ya ce, “Akwai babban batu. Muna bukatar ganawa da Ustaz Yunus (SAN) domin mu garzaya kotu don dakatar da gwamnatin jiha; kawai sun aiko mana da takardun soke mallaka guda tara”.

Daga cikin kadarorin da abin ya shafa sun hada da filaye guda biyar a Mogadishu, filaye uku a kan titin Kwato, da fili daya a Doka.

A cikin takardun soke hakkin mallakar da magatakardar hukumar kula da bayanan kasa ta Kaduna (KADGIS) ya sanya wa hannu, Mahmud Aminu ya ce, “An umarce ni da na sanar da ku cewa mai girma Gwamnan Jihar Kaduna a cikin ikon da aka ba shi a karkashin sashe na 28 (5) (a) da (b) na dokar amfani da filaye ta 1978, ya kwace hakkin mallakar wadannan kadarori da aka ambata”.

AMINIYA 

Hajj2023 : Hukumar NAHCON Ta Kaddamar Da Tawagar 'Yan Jaridu

Shugaban Hukumar Alhazai ta Najeriya, NAHCON, Alhaji Zikrullah Kunle Hassan, ya kaddamar da tawagar kafafen yada labarai na kasa domin gudanar da aikin Hajji na shekarar 2023 a kasar Saudiyya.

Taron ya gudana ne a ofishin da ke Abuja ranar Alhamis.

Hassan ya jaddada mahimmancin bin ka'idojin ƙwararru, gami da daidaito a aikin jarida.

Ya taya ‘yan tawagar murna da aka zabo su, ya kuma bukace su da su dauki kansu a matsayin abokan hadin gwiwa da NAHCON wajen gudanar da aikin Hajji ba tare da wata matsala ba.

Shugaban hukumar ya bayar da tabbacin cewa za a kwashe dukkan maniyyatan da suka yi rajista a jirgi a kan lokaci, inda ya ce jami’an NAHCON za su tafi kasar Saudiyya ranar 21 ga watan Mayu domin yin shirye-shiryen da suka dace.

Ya nanata kudurin hukumar na tabbatar da cewa alhazai sun samu kimar kudinsu kuma an dauke su cikin gaggawa.

Da yake magana kan da rawar da kafafen yada labarai ke takawa, shugaban NAHCON ya yi kira ga kungiyar kafafen yada labarai ta kasa da su bayyana Musulunci da Hukumar da kyau.

Ya bukaci goyon bayansu, hadin kai, da kuma gaggauta bayar da rahoton duk wani jinkirin da aka samu a hidimar, inda ya bukace su da su tuntubi NAHCON kafin su buga bayanai a yanar gizo.

Sheikh Suleman Mommoh, kwamishinan tsare-tsare, bincike, kididdiga, bayanai, da kuma ayyukan dakunan karatu, ya taya tawagar yada labarai murna tare da jaddada muhimmancin bayar da rahotanni masu inganci da daidaito.

A nasa bangaren, Kwamishinan Ma’aikatar Kula da Ma’aikata da Kudi, Alhaji Nura Hassan Yakasai, ya bayyana bukatar da ke akwai na samar da rahotanni na hakika da ke fifita muradun Musulunci, Nijeriya, da kuma NAHCON.

Alhaji Mousa Ubandawaki mataimakin daraktan yada labarai da yada labarai na NAHCON ya baiwa ‘yan jarida muhimman bayanai game da ayyukansu na sana’a a kasa mai tsarki tare da yi musu fatan Alheri.

Wednesday, 17 May 2023

Labari da dumiduminsa : Tinibu Zai Zo Kano Domin Bude Ayyuka - Ganduje

Gwamnan jihar kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa ana sa ran zaɓaɓɓen shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu zai zo jihar kano domin bude wasu aiyuka da gwamnatinsa gudanar a nan kano.

 
” A yayin da muka cigaba da bude wasu daga cikin aiyukan raya kasa da gwamnatinmu ta yi a kwarya birnin kano da kewaye, Muna sa rana Zaɓaɓɓen Shugaban kasa Asiwaju Bola Ahmad Tinubu zai zo Kano domin kaddamar da sabuwar gadar da muka Samar a kofar mata zuwa Ibrahim Taiwo Road”.


Kadaura24 ta rawaito Ganduje ya bayyana hakan ne yayin da yake jagorantar taron majalisar zartarwar ta jihar kano na wannan makon a gidan gwamnatin jihar kano.


Ganduje yace ya bude aiyuka Masu tarin yawa Kuma zai cigaba da bude aiyukan don raya kasa da gwamnatinsa ta gudanar.

Ganduje dai ya na bude aiyukan da ya gudanar ne a wani bangare na bankwana ga al’ummar jihar kano sakamakon karewar wa’adin gwamnatin sa a ranar 29 ga watan mayu.

An faɗa mana ƙarasa ayyukan da wasu suka faro babbar nasara ce - Zaɓaɓɓun gwamnoni

 


An faɗa wa zaɓaɓɓun gwamnonin da za a rantsar ranar 29 ga watan Mayu a Najeriya, cewa a cikin nasarar shugabanci, akwai ƙarasa ayyukan da magabatansu, suka faro.

Matakin zai taimaka wajen tabbatar ci gaban ƙasa da alkinta dukiyar al'umma da rage kashe kuɗi wajen gudanar da harkokin mulki a matakan jihohi.

Wannan jan hankalin, na cikin ɗumbin bayanai da shawarwari da aka gabatar wa zaɓaɓɓun gwamnonin Najeriya, yayin wani taron sanin makamar aiki da aka shirya musu a babban birnin ƙasar, Abuja.

Manufar taron na kwana uku, ita ce shirya gwamnonin masu jiran gado da dabaru da hikimomin shugabanci kafin a rantsar da su nan da kwana 12.

Ƙungiyar gwamnoni ta Najeriya ce ta shirya taron a Abuja, inda ta gayyato ƙwararru a fannoni daban-daban game da sanin dabarun shugabanci a ciki da wajen ƙasar domin bunƙasa ƙwarewar sabbin gwamnonin.

Jiga-jigan 'yan siyasa kamar Simon Lalong na jihar Filato da Nasiru El-rufa'i da su Kayode Fayemi sun ja hankalin zaɓaɓɓun gwamnonin da za su hau karagar mulkin jihohi su fifita muradan al'umma a kan bambancin siyasa da ta aƙida.

Haka zalika, an ja hankalin sababbin gwamnonin kada su yi ƙasa a gwiwa wajen koyon dabaru da salon ayyukan raya ƙasa daga wasu jihohi, don hanzarta ci gaban jihohinsu.

Ɗaya daga cikin mahalarta taron, zaɓaɓɓen gwamnan jihar Sokoto, Alhaji Ahmed Aliyu ya ce horon sanin makamar aikin, ba shakka zai taimaka wajen inganta gudanar da harkokin mulki a jihohi da zarar sun fara aiki.

Ya ce "kusan in ce mun koma aji. Don aji ne ake shiga tun bakin ƙarfe 9 na safe zuwa 9:30, wata ran a kai ƙarfe 4 ko 5 na yamma".

A cewar Ahmed Aliyu, duk da yake ya yi mataimakin gwamna tsawon shekara huɗu, kuma ya sha gudanar da ayyukan da gwamna ke yi, amma ya koyi sabbin dabaru da bai taɓa samu ba a baya.

"Musamman an nuna mana muhimmancin ƙarin hanyoyin samun kuɗin shiga a jihohinmu.

Kuma an ja kunnenmu game da buƙatar kammala ayyukan da gwamnoni masu barin gado suka faro, saboda da kuɗin jihohinmu ake yinsu", in ji zaɓaɓɓen gwamnan na Sokoto.

A ranar 29 ga watan Mayun nan ne, za a rantsar da su, bayan zaɓen gwamnoni a ranar 18 ga watan Maris.

Governors Induction

ASALIN HOTON,BIODUN OYEBANJI/FACEBOOK

Zaɓaɓɓun gwamnonin za su jagoranci jihohinsu ne tsawon shekara huɗu mai zuwa.

Taken horon “Shugabanci Don Ganin Tasiri: Gina Matakan Mulki a Ƙasa” na da burin ƙarfafa gwiwar sabbin gwamnonin wajen lalubo mafita ga matsalolin da za su fuskanta.

A cewar ƙungiyar gwamnonin ƙasar (NGF) wata manufar taron ita ce faɗakar da sabbin gwamnonin irin girman nauyin da zai rataya a wuyansu na amanar talakawa da kuma hanyar da ta fi dacewa su bi wajen sauke wannan nauyin.

Daraktan watsa labarai na ƙungiyar ta NGF, Abdurrazak Barkindo ya ce da ma an saba gudanar da taron don sanar da zaɓaɓɓun gwamnoni da waɗanda suka ci zaɓe wa'adi na biyu game da wahalhalun rayuwa da mutanensu ke ciki da kuma hanyoyin da za su tunkari matsalolin.

Governors Induction

ASALIN HOTON,GOV AA SULE/FACEBOOK

Abdurrazaƙ Barkinɗo ya ce yayin taron ana tafka muhawara da gabatar da maƙaloli da kuma musayar ra'ayoyi da gogayya da wasu fitattun shugabanni da suka yi mulki.

A cewarsa, ƙungiyar ta gayyato ƙwararru daga cikin Najeriya waɗanda suka haɗar da tsoffin gwamnoni da wasu ƙwararru da masana daga ƙasashe kamar Kenya da Amurka da sauransu.

Governors Induction

ASALIN HOTON,SENATOR UBA SANI/FACEBOOK

Governors Induction

ASALIN HOTON,SENATOR UBA SANI/FACEBOOK

Bayanan hoto,

Sanata Uba Sani, zaɓaɓɓen gwamnan jihar Kaduna shi ma yana halartar taron sanin makamar

Ko da yake, galibi wannan horon ya karkata ne kan yadda za a haɓɓaka tattalin arziƙi da kyautata shugabanci a matakin jihohi, akwai matsaloli da dama shimfiɗe a ƙasa cikin jihohin da sabbin gwamnonin za su karɓi ragamarsu nan da 'yan kwanaki.

Kamar dai na rashin tsaro da kantar talauci da rashin aikin yi da dimbin bashi da kuma rashin biyan hakkokin ma’aikata masu ci da wadanda suka yi ritaya da dai sauransu.

Governors Induction

ASALIN HOTON,ZAYYANU ZAKARIYA GUSAU/FACEBOOK

Bayanan hoto,

Zaɓaɓɓen gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawal Dare da Gwamnan jihar Yobe Mai Mala Buni


BBC

Tuesday, 16 May 2023

Abun Da Tinibu Da Kwankwaso Suka Tattauna A Kasar Waje


Shugaban kasa mai jiran gado, Bola Tinubu ya yi wata ganawar sirri da dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar NNPP, Sanata Rabiu Kwankwaso a kasar Faransa.

Wata majiya mai tushe ta ce Tinubu ya yi wa Kwankwaso tayin tafiya tare da shi a sabuwar gwamnati da kuma duba yiwuwar sulhu tsakaninsa da Gwamnan Kano mai barin gado, Abdullahi Ganduje.

A ranar Litinin, mako biyu kafin Tinubu ya karbi rantsuwar fara aiki, suka shafe sama da awa hudu suna ganawar sirrin da Kwankwaso a birnin Paris na kasar Faransa.

Majiyarmu ta ce a yayin ganawar, Tinubu ya bukaci hadin kai domin aiki tare da Sanata Kwankwaso — wanda ya lashe kuri’un Jihar Kano a zaben 2023.
Kwankwaso da shugaban kasar da ke jiran rantsarwa nan da mako biyu masu zuwa sun kuma amince za su ci gaba da tattaunawa kan wannan batu.

Majiyar ta ce mai dakin Kwankwaso da zababben Sanata Abdulmumini na Jam’iyyar NNPP ne suka raka madugun Kwankwasiyya zuwa wurin ganawar.

A bangaren Tinubu kuma, matarsa, Sanata Oluremi da Mataimakin Shugaban Majalisar Wakilai mai barin gado, Femi Gbajabiamila, ne suka raka shi.

Majiyar ta ce “Matar Tinubu, Sanata Oluremi ce ta karbi bakuncin Hajiya Hafsa, a yayin da ‘yan siyasar kuma suka dauki tsawon lokaci suna tattauna a kan hadin kan kasa da abubuwan da sabuwar gwamnati za ta ba wa muhimmanci.

“Sauran sun hada da batun shugabancin Majalisar Dokoki ta Kasa da kuma aniyar zababben shugaban kasan na kafa gwamnatin hadin kan kasa da ake fatan damawa da Kwankwaso a ciki.

“Sun kuma yi waiwaye a kan kawancensu na siyasa tun suna lokacin da suke Majalisar Dokoki ta Kasa a shekarar 19992,” in ji majiyar.

Majiyar ta kara da cewa a yayin zaman an kuma fara tunanin sasanta tsakanin Kwankwaso da tsohon mataimakinsa, wato Gwamnan Kano mai barin gado, Abdullahi Ganduje.

A shekarar 2015 Ganduje ya gaji kujerar Kwankwaso, amma ba da jima ba daga baya suka raba gari, kuma har yanzu ba sa ga-maciji.
AMINIYA 

Osinbajo: Shaida a kan hidima da kishin kasa- Alwan Hassan

 Daga Alwan Hassan


 

Nan da kusan mako biyu masu zuwa, Farfesa Yemi Osinbajo zai kammala aiki a matsayin mataimakin shugaban tarayyar Najeriya.

 

Ba tare da wata fa’ida ba, ’yan Nijeriya, ciki har da naku da gaske, sun ga a cikin shekaru 8 da suka wuce, abin da ake nufi da mutum ya sadaukar da kai ga manufofin gina kasa; ya ba da kansa gaba ɗaya don inganta ƙasarmu da inganta ɗimbin ƴan ƙasa. A cikin Osinbajo, ’yan Najeriya sun ga mutum mai jajircewa da jajirtacce, ya sadaukar da rayuwarsa gaba daya a hidimar Nijeriya, ya kuma mik’e kan sa kusan ya kai ga gaci, domin yin hidimar abin yabawa ga wannan kyakkyawar kasa.

 

Kwanan nan, na ci karo da wani jawabi da Farfesa Osinbajo ya gabatar a Cibiyar Nazarin Siyasa da Dabarun Najeriya (NIPSS) da ke Jos, Jihar Filato. A cikin laccar da ake magana a kai, mataimakin shugaban kasar ya yi magana game da bukatar masu ruwa da tsaki a aikin Najeriya don kare hadin kan al’ummar kasa ta hanyar kau da kai daga “yin amfani da son zuciya da kuma kira na kyamar kabilanci.” Ya yi kira da a da’a a matsayin abin da ya dace wajen tabbatar da zaman lafiya ya dore a Najeriya.

 

A wannan lokacin, kamar yadda aka saba, ya yi magana cikin sha'awa da kuma dukkan karfin muryarsa, yana mai kira ga kowane dan Najeriya da ya rungumi dan kasa, maimakon na farko.

 

A cikin shekaru takwas, a gida da waje, Osinbajo yayi magana ne a kan Najeriya da kuma a madadin ‘yan Najeriya a kowane lokaci, yana amfani da karfin halinsa, kudinsa, dabi'unsa, mutuncinsa da basirarsa wajen aiwatar da kasarmu. Ban da haka ma, bai taɓa ƙyale aikin hukuma ya ruɗe kansa ba; zama gaskiya ga kansa duk ta hanyar da kasancewa mai ladabi da abokantaka da kowa, babba ko ƙarami, wanda ya zo hanyarsa

 

 Kuma duk yadda ka kasance babban mai suka, wani abu da ba za ka yi la’akari da shi ba a kan Osinbajo, shi ne irin kishin kasa da tsantsar kaunarsa ga kasar nan, wanda ya nuna a kai a kai ta hanyar gudanar da aikinsa na Mataimakin Shugaban kasa da hali, cancanta da rikon amana. .

 

Da kaina, a lokacin da nake kusa da mataimakin shugaban kasa, na fara fuskantar aininhin yadda halinsa yake, na tausayi da kuma yin komai a bude a matsayin jagora. Yana da hankali. A matsayinka na wanda ke da ra’ayi sosai, duk abin da kake bukata ka sa Farfesa Osinbajo ya sa hannu a kan ra’ayinka ko shawararka shi ne ka gamsar da shi kan kimarta da tasirinta ga Nijeriya.

 

Wannan shine dalilin da ya sa na yi imani da gaske cewa Mataimakin Shugaban kasa mai barin gado ba kawai mai gudanar da aiki ba ne amma kuma mai kishin kasa na gaske.

 

Hakika, idan ’yan Najeriya suka waiwayi baya a tsakanin 2015 zuwa 2023, tabbas za su yaba da gagarumar gudunmawa da tasirin da wani mutum mai sanya hular Awolawo ya bayar, wanda mutane da yawa suka bayyana a matsayin wanda ke da kwarewa mai ban sha'awa wanda "ya nuna kwarin gwiwa da sha'awar gudanar da aikinsa."

 

 Da yake ya kasancewa ƙwararren haziƙi a cikin harkokin mulki da hidimar jama'a, Osinabajo ya ɗaga tsammanin da ke da alaƙa da ofishin maitaimakin shugaban kasa kuma ya tabbatar da cewa yana yiwuwa a iya samun tasiri yayin riƙe dabi'u da halaye masu nagarta.

 

Yayin da zai koma gida nan da mako biyu don yin hutun da ya dace, watakila ba za a dade ba, ina addu’ata  Allah Ya ci gaba da haskaka tafarkin jagoranmu mai daraja Farfesa Osinbajo. Ni da kaina, ina gode masa saboda abokantakarsa da sadaukarwar da ya yi a kasarmu; kuma ina rokon Allah (SWT) ya karawa mai girma mataimakin shugaban kasa da tsawon rai don ganin Nijeriya ta samu daukakar da aka kaddara.

 

Na gode Farfesa, saboda karramawar da ka yi min da kuma  darussa da sadaukarwa da ka koyar damu da sadaukar da kai da kishin kasa, hakika ni kaina da ‘yan gidanmu zamu ci gaba da daukarka a matsayin dan uwanmu.

 


Zargin Batanci: Kotu Ta Ba Da Belin Dokta Idris Abdulaziz

Kungiyar Fityanul Islam ta maka shi a kotu bisa zargin batannci ga Manzon Allah (SAW), zargin da malamin ya karyata.
Kotu ta bayar da belin malamin Musuluncin nan, Dokta Idris Abdulaziz Dutsen Tanshi, wanda ake zargi da batanci ga Manzon Allhah (SAW).

Kungiyar Fityanul Islam ce dai ta maka malamin a kotu bisa zargin sa da kalaman batannci ga  Manzon Allah (SAW), zargin da malamin ya musanta.

 

Da dumi-dumi: Kwankwaso yayi ganawar sa’o’i hudu da Tinubu a birnin Paris

Zababben shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, da Rabiu Musa Kwankwaso, wanda ya yiwa jam’iyyar NNPP a zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu, sun yi ganawar akalla sa’o’i hudu a birnin Paris na kasar Faransa a ranar Litinin, kamar yadda jaridar TheCable ta ruwaito.

A tsakiyar tattaunawar, TheCable ta fahimci cewa, akwai yuwuwar shigar Kwankwaso cikin gwamnati mai zuwa yayin da Tinubu ke shirin kafa “gwamnatin hadin kan kasa” – wanda ke nufin bai wa jam’iyyun adawa wasu mukamai a cikin gwamnatin.


Taron ya kuma tattauna batutuwan da suka shafi zaben shugabannin majalisar kasa, gabanin kaddamar da majalisar ta 10 a ranar 13 ga watan Yuni.

Zaben gwamnan kano: Inda aka Kwana game da karar APC da NNPP a Kotu

An fara taron Paris tsakanin Tinubu da Kwankwaso ne da karfe 12:30 na rana kuma aka kammala da karfe 4:45 na yamma, kamar yadda wasu majiyoyi suka shaida wa jaridar TheCable.

Ko Kun zabi aiki ko ba ku zaba ba, mun yi titin Kurna babban layi ne saboda Allah -Ganduje

Femi Gbajabiamila, kakakin majalisar wakilai kuma shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, ya halarci taron yayin da Abdulmumin Jibrin, dan takarar jam’iyyar NNPP kuma tsohon jigo a kwamitin yakin neman zaben Tinubu na daga cikin wadanda suka raka Kwankwaso.

Oluremi Tinubu, Sanata kuma matar zababben shugaban kasa ita ce ta tarbi matar Kwankwaso, Salamatu.

Idan za’a iya tunawa Tinubu da Kwankwaso sun yi aiki a matsayin gwamnonin kano da Lagos a Shekarar 1992.


Kada Ku Nemi Na Saki 'Yan Daba - Muhuyi Magaji Ya Gargadi 'Yan Siyasa

Kano Business Community Endorses Gov. Yusuf for Second Term

The leadership of the Kano business community, comprising representatives of 25 major markets across the state, has endorsed Gov...