Search This Blog

Wednesday, 10 May 2023

Yakin Sudan: Akwai Yiwuwar Maniyyata Su Kara Biyan Wasu Kudin


 Hukumar Aikin Hajji ta Kasa (NAHCON) ta tabbatar da cewa yaƙin da ake yi a kasar Sudan zai shafi jigilar maniyyatan Najeriya na bana, wanda ka iya sanadin karin kudin kujerar.

A ranar Talata hukumar da kamfanonin sufurin jiragen sama na cikin gida suka rattaba hannu a kan yarjejeniyar jigilar mahajjatan ta bana

A makon jiya dai sun gaza yin hakan saboda batun ƙarin kuɗi.

Sai dai hukumar ba ta bayyana ko matakin na nufin, maniyyata aikin hajji ne za su biya ƙarin kuɗin da dogon zagayen zuwa kasa mai tsarki ko a’a ba.

Kwamishinan Tsare-tsare da Gudanar da Gikin Hajji a hukumar, Abdullahi Magaji Hardawa, ya ce har zuwa yanzu ba a cimma matsaya kan ko mahajjata ne za su yi ƙarin kuɗin ba.

A cewarsa, matuƙar ba a buɗe sararin samaniyar kasar Sudan ba, har aka fara jigilar maniyyatan bana daga Najeriya, to dole sai jiragen sama sun yi zagaye, wanda zai haddasa ƙarin kuɗi.

Jami’in ya ce babban hatsari ne jirgin sama ya ratsa ta sararin samaniyar Sudan, shi ya sa hukumomin ƙasar suka dakatar da zirga-zirgar jiragen sama a kasar.

Harɗawa ya ce matuƙar aka fara jigilar maniyyata aikin hajji na bana, ba tare da an bi ta Sudan ba, za a fuskanci matsaloli guda biyu ko fiye.

“Na farko, in ba za a shiga ta sararin samaniyar Sudan ba, dole za a shiga ta wasu ƙasashe. To ƙasashen nan akasari, za a biya su kuɗin ratsawa ta sararin samaniyarsu.

“To maimakon kuɗin da za a biya na ƙasa ɗaya, wato Sudan. (A yanzu) mai yiwuwa a biya na ƙasashe da yawa. Kun ga an samu ƙarin kuɗaɗe ke nan,” in ji shi.

Na biyu, a cewarsa, tun da akwai ƙarin tazara kamar na sa’a biyu a tafiyar jirgin sama, man da jirgin yake sha ma zai ƙaru, wanda ke nufin ƙarin kuɗin jigilar alhazai.

Abdullahi Harɗawa ya ce kamfanonin jiragen sama sun sa hannu a kan yarjejeniyar jigilar aikin hajjin na bana ne bayan an daddale tsakaninsu da Hukumar NAHCON a kan matsalolin da za a iya fuskanta.

Ya ce: “Sun amince sun sa hannu ɗin, amma an yarda akwai bukatar a san yadda za a yi, a ƙara musu farashi.”

Jami’in ya ce kasanceaw maniyyata sun riga sun biya kuɗi, “bisa yadda aka tallatar masa,”  yanzu ba zai iya tabbatar da ko za a bukaci maniyyaci ya kara biyan wasu kudin ba.

“Amma dai abin da nake tabbatar muku so hi ne, akwai bukatar ƙarin kuɗi. Akwai tazara da yawa. Akwai ɗawainiya da yawa. Karin kuɗin nan daga ina zai fito? Shi ne ba a cimma matsaya ba”.

Kamfanonin sufurin jiragen saman da suka sa hannu kan yarjejeniyar sun haɗar da – Air Peace da Azman Air Services da Aero Contractor da kuma Max Air.

AMINIYA

Gamu Da Tafiya A Motar Haya Kashi Na 4- Dr Dukawa

HALIN DA TITUNAN NAJERIYA SUKE CIKI
Tafiyar da muka yi daga Kano zuwa Yola ta dauke mu kimanin awa tara (9.30 na safe – 6.30 na yamma). Kuma na yaba da tukin direbanmu, wani matashi mai suna Uzairu dan kimanin shekara 25/6. Wannan tafiyar ta tuna min da wani majigi da shahararren masanin kimiyar siyasa, Farfesa Ali Mazrui, ya yi a shekarun 1980. Ali Mazrui dan asalin Kenya ne, ya auri ‘yar Najeriya, sun rayu a America har rasuwarsa. 

Guda daga cikin hanyoyin da Ali Mazrui ya bi wajen nuna tazarar da take tsaknin manyan kasashe da masu tasowa shine yadda ya dauko hoton wani titi a wata babbar kasa (watakil America) da motoci suna gudu kowacce a layinta. Sai ya ce: “duk wanda ka gani yana tuki yana kwane-kwane anan, to a cikin maye yake”. Sai kuma ya dauko wani titi na wata kasar mai tasowa (watakila Kenya ko Najeriya), da motoci suna ta kwane-kwane suna kaucewa ramukan kan titi. Sai ya ce: “anan kuma, duk wanda ka gani yana tafiya sambel babu kwane-kwane to a buge yake!” 

Yau kimanin shekara arba’in da wannan majigin na Ali Mazrui amman har yau titinan Najeriya sai ana tafiya ana ta kwane-kwane a wurare da yawa. Ga arziki Allah yana ta dada tuttudowa kasar amman lafiyayyun hanyoyin mota sun gagara. Illolin rashin hanya mai kyau suna da yawa. Ko ba a yi hatsari an rasa rayuka da dukiya ba fargabar yiwar afkuwar hakan ta ishi matafiya. Ga kuma saurin lallacewar abin hawa. 

Sai dai ko babu komai na lura gwamnatocin jihohin Adamawa da Taraba sun kokarta wajen samar da titinan cikin gari da magudanan ruwa masu kyau. Amman fa akwai tarin shara da ta rufe magudanan ruwa masu yawa. Yana da matukar muhimmanci gwamnatocinmu su samo kan yadda za a yi da shara a birananmu. Sannan akwai bukatar ko hadin guiwa ne su yi wajen gyara manyan titina idan gyaran ya gagari gwamnatin tarayya.

Mu Tashi Tsaye Domin Kawo Karshen Rikicin Sudan — Aisha Buhari

Uwargidan Shugaban Najeriya, Aisha Buhari ta roki a hada karfi da karfe don ganin kurar rikicin Sudan ta kwanta.

Jaridar Premium Times ta ruwaito Aisha Buhari na wannan kira a wani taro da ta jagoranta jiya Litinin a Fadar Gwamnati da ke Abuja.

A cewar jaridar, Aisha Buhari na ganin akwai rawar da matan shugabannin Afirka za su iya takawa musamman wajen kai agaji Sudan.
Sama da mutane 500 ake kyautata zaton cewa rikicin ya yi sanadin rasuwarsu kawo yanzu.

Mutum sama 700,000 sun rasa muhallansu

Alkaluman mutanen da rikicin Sudan ya raba da muhallansu ya ninka zuwa sama da mutum 700, 000, a cewar Majalisar Dinkin Duniya.

Karuwar mutanen da ke guje wa muhallansu ya sanya fargaba kan yaduwar fadan duk da tattaunawar tsagauta bude wuta da ake yi a Saudiyya.

Khartoum na da al’umma kusan miliyan 5.4, sai dai an daidaita birnin mai cike da zaman lafiya a baya tun bayan barkewar fada a ranar 15 ga watan Afrilu.

Tun ranar 15 ga watan Afrilu, yaki ya barke a Sudan kuma har wannan lokaci, an kasa cimma yarjejeniyar tsagaita wuta ta dindindin.
Khartoum na da al’umma kusan miliyan 5.4, sai dai an daidaita birnin mai cike da zaman lafiya a baya tun bayan barkewar fada a ranar 15 ga watan Afrilu.

Ana gudanar da fadan ne tsakanin sojojin kasar da Janar Abdel Fattah al-Burhan ke jagorata da kuma dakarun RSF bangaren Janar Mohamed Hamdan Dagalo, wanda aka fi sani da Hemedti.

Sama da mutum 600 ne aka kashe kawo yanzu tare da jikkata 5,000.

Tuesday, 9 May 2023

Abin Da Ya Haddasa Yakin Sudan Jamhuriyar Musulunci (Kashi Na Biyu)



Datti Assalafiy✍️

Mutane biyu ne sukayi sanadiyyar yakin da ya barke a Kasar Sudan, kuma Musulmai ne abokan juna na kut da kut.

Na farko sunansa:
General Abdel Fattah al-Burha, shine Shugaban Sojojin Sudan wanda ya jagoranci kifar da mulkin tsohon shugaba Umar Al-Bashir ya haye kujeran mulki

Na biyu sunansa:
Janar Muhammad Hamdan Dagalo (Hemetti), shine mataimakin Shugaban Kasar Sudan, kuma shine babban Kwamandan rundinar tsaro na agajin gaggawa da ake kira Rapid Support Forces (RSF)

Wanene Dagalo? 
Kamar yadda na fada a sama, yanzu haka Dagalo shine mataimakin Shugaban Kasar Sudan, kuma shine Babban Kwamandan RSF, wato yana rike da matsayi guda biyu a Sudan kenan 

Rapid Support Forces (RSF) rundinace ta tsaro da aka kafata tun a lokacin yakin basasar da akayi a yankin Dafur na Kasar Sudan, suna aiki da sarrafa makaman yaki kamar sojoji

Janar Muhammad Hamdan Dagalo gawurtaccen dan ta'adda ne, kuma dan tawaye, a lokaci guda kuma dan siyasa, kamar dai misali da a nan Nigeria mu ce Bello Turji, sannan kazamin mai kudi ne na fitar hankali, bincikena ya nuna min cewa a Sudan babu wanda ya kai Dagalo arziki, shine shugaban masu satar zinare na Kasar Sudan, kusan shine yake juya akalar hako zinare na Kasar Sudan, yayi karfin da a Sudan babu wanda ya isa ya nuna masa yatsa tun daga kan shugaban Kasa

Saboda ku tabbatar da kudinsa, lokacin da Amerika tasa aka yiwa Shugaba Umar Al-bashir zanga-zanga da tawaye, anyi wata uku a jere babu albashi a Sudan, Dagalo ne ya ara wa Gwamnatin sudan kudi aka biya albashi a fadin Kasar, yana da mayakansa na RSF sama ds guda dubu dari don har sun fi sojojin Kasar yawa,, makamin da yake hannunsu yafi na sojojin Sudan aminci

To lokacin da aka fara zanga-zangar da ta kai ga kifar da shugaba Al-bashir, kafin Sojoji su hadu da RSF su hambarar da Al-bashir, shugaba Al-bashir sai yayi wata dabara na siyasa don ya kara karfi, sai ya kira Dagalo ya bashi jagorancin rundinar  RSF, amma haka Dagalo ya zagaya ya hada kai da abokinsa shugaban Sojojin Sudan Janar al-Burhan suka kifar da Gwamnatin Al-bashir, to daga nan ne sai rundinar sojin Sudan da tayi juyin mulki ta bawa Dagalo matsayin mataimakin Shugaban Kasa, saboda suna tsoron zai iya musu juyin mulki suma, domin ya fisu karfi ya fisu kudi

Abinda ya haddasa yakin Sudan:
A cikin azumin watan Ramadan da ya gabata, Shugaban mulkin Soji na Kasar Sudan Janar al-Burhan ya kira abokinsa kuma mataimakin Shugaban Kasa sannan babban Kwamandan rundinar RSF Janar Dagalo tattaunawa na musamman, yace masa muna so rundinar RSF ta dawo cikin rundinar sojin Kasar Sudan a zama daya, to shi kuma Dagalo sai yaki amincewa, yace a wani dalili? shine sukace masa ai ba zai yiwu ayi rundinar soji biyu ba, kuma ba zai yiwu ayi shugaban Kasa biyu ba, haka dai suka watse ba tare da fahimtar juna ba

Shi kuma Dagalo da ya fahimci Sojin Sudan zasu bashi matsala, daga kammala wannan tattaunawa sai ya fita ya yaje da mayakansa na RSF ya fara karban iko da wasu gurare a Sudan, shi kuma shugaban Kasa Janar al-Burhan kawai sai ya fito ya ayyana RSF a matsayin rundinar 'yan ta'adda, kunga ya halatta zubar da jininsu kenan, to wannan ne babban abinda ya haddasa yakin Sudan a halin yanzu, a cikin sati guda sau uku rundinar RSF na yunkurin yiwa sojojin Sudan juyin mulki wanda ya kai ga gwabza kazamin fada

RSF Sunyi kokarin kwace babban filin tashi da saukar jiragen sama na Sudan dake Khartoum to amma Allah bai basu nasara ba, shi kuma al-Burhan sai yayi sauri ya rufe filin jirgin saboda ya san karfin abokin nasa Dagalo, saboda idan RSF suka kwace filin jirgi, wato aka bari jirage suna sauka, to abinda zai faru shine, Dagalo zai samu tallafi daga abokan huldarsa na duniya irinsu Yariman Saudiyyah Muhammad bin Salman, shugaban Kasar Egypt Janar Abdulfatah al-Sisi, shugaban Kasar Faransa Emmanuel Macron, shugaban Kasar Russia Vladimir Putin  da sauransu, musamman saboda ya yiwa Russia alkawari zai bata damar kafa sansanin soji a Sudan, ita kuma Amerika bata so, tana tare da al-Burhan

A rubutuna gaba zanyi bayani akan kudaden da ake kashewa a wannan yaki na Sudan, da salon yakin da karfin makamai da barnan da akeyi a Sudan, da kuma inda yakin ya nufa har zuwa lokacin da masana ilmin tsaro suke hasashen za'a iya kawo karshen yakin

Muna rokon Allah Ya kare bayinsa a Sudan, Ya sa yakin ya cinye wadanda suka yiwa shugaba Al-bashir zanga-zanga da tawaye


Hajj2023 : Kamfanonin Jiragen Sama na Najeriya, Sun Sanya Hannu kan Yarjejeniyar Jigilar Alhazai

Hukumar alhazai ta kasa NAHCON da kuma kamfanin jiragen saman Najeriya hudu sun amince da jigilar maniyyata zuwa aikin hajjin 2023 daga karshe sun sanya hannu kan yarjejeniyar jigilar alhazai ta 2023 tsakanin bangarorin biyu. 

A sanarwar da Mataimakin Daraktan yada labarai na hukumar NAHCON, Mousa Ubandawaki ya fitar, Taron wanda ya gudana a dakin taro na gidan Hajji a ranar Talata, ya samu halartar shuwagabannin kungiyoyin hudu.

A nasa jawabin, Shugaban Hukumar NAHCON, Alhaji Zikrullah Kunle Hassan, ya yabawa kishin kasa da kamfanonin jiragen sama suka sadaukar domin tunkarar kalubalen da rikicin kasar Sudan ke fuskanta. 

“Ba mu manta da kalubalen da rufe sararin samaniyar kasar Sudan ya haifar ga aikin Hajjin ku ba; duk da haka, ina so in yi kira ga lamirinku da kishin ƙasa da ku da kada ku ƙara dora wa mahajjata ƙarin kuɗi ko canje-canje”.

A jawabansu daban daban, Manajan Daraktan Kamfanin  Jirgin Aero, Kaftin Ado Sanusi ya ce jiragen ba su damu da halin da Alhazan da suka biya kudin aikin Hajji a baya ba kafin rikicin ya barke, amma an takura musu da daukar wannan matakin domin kuwa an hana mu daukar wannan mataki ne. na kayan aiki da buƙatun aiki. Ba za mu so wani abu da zai kawo cikas ga aikinmu yayin jigilar "

Hakazalika, Shugaban Hukumar Air Peace, Cif Allen Onyeama, ya ce kiran da suka yi na a sake duba yarjejeniyar jigilar alhazan da NAHCON, ba wai a yi amfani da rikicin kasar Sudan don samun riba ko dama ba. “Muna kula da alhazan Najeriya da yawa wadanda muka san sun sadaukar da kansu wajen biyan kudin aikin Hajji. Muna kuma lura da cewa maniyyata sun riga sun biya kafin wannan rikici ya barke. Ba ma so mu hana su wannan damar don yin tafiya zuwa ƙasa mai tsarki. Muna yin hakan ne don alfaharin kasa”.

Yarjejeniyar a hukumance tare da kamfanonin jiragen sama guda hudu na gida- Air Peace, Azman Air Services, Aero Contractor da Max Airline ya haifar da rashin jituwa tsakanin Hukumar da masu jigilar Alhazai na 2023 da aka amince da su. Har ila yau, yana wakiltar gagarumin ci gaba a tattaki na fara jigilar jirage zuwa Hajji 2023 wanda za a fara a hukumance a ranar 21 ga Mayu tare da jigilar jirgin na tawagar farko daga filin jirgin saman Nnamdi Azikwe, Abuja.

Idan za a iya tunawa, jirgin saman Saudiyya Flynas ne ya rattaba hannu kan yarjejeniyar tashi da saukar jiragen sama na shekarar 2023 da Hukumar a ranar Talata 2 ga Mayu, 2023 yayin da wakilan sauran hudun suka ki sanya hannu kan rikicin Sudan da kuma bukatar tuntubar shugabanninsu. dalilai.
 

Hajj2023 : Labari Cikin Hotuna ; A karshe dai Kamfanonin Jiragen Sama sun sanya Hannu kan yarjejeniyar dibar maniyyata aikin Hajin bana

A karshe dai Kamfanonin Jiragen Sama na Azman, Max Air, Aero Contractors, Air Peace, Arik Air sun rattaba hannu kan yarjejeniyar jigilar Hajji ta 2023 a yau Talata, 9 ga Mayu, 2023 
Wannan ci gaba shi ne ya kawo karshen fargabar da Maniyyatan ke yi wajen samun jinkirin tashin su zuwa kasa mai tsarki 
 NAHCON MEDIA UNIT

Abun Da Ya Haddasa Yakin Sudan Jamhuriyar Musulunci (Kashi na daya) - Datti Assalafiy

Datti Assalafiy✍️

Shimfida:
Akwai taba addini a yakin Sudan, saboda shi tsohon shugaban Kasar Sudan Umar Albashir wanda aka masa tawaye aka hambarar dashi da karfin tsiya ya bawa Musulunci kariya sosai a Sudan, yana bawa Musulunci kariya a Sudan wanda ko Saudiyyah bata yin irinsa a Kasarta

Yana daya daga cikin shugabannin Kasashen Musulunci a duniya wanda idan makiya Musulunci suka taba addinin Allah da Musulmai yake fitowa yayi magana, Kasar Iran daular masu bin addinin shi'ah sun taba yin mummunan batanci ga Sahabban Annabi (SAW) guda biyu Abubakar da Umar, a ranar ya kori Ambasadar Kasar Iran, kuma yasa aka rushe embassy na Iran dake Sudan, aka gina Sabon Masallaci a gurin, aka sanya wa Masallacin sunan Abubakar da Umar wato sunan Sahabban Annabi (SAW)

Lokacin Shugaba Umar Albashir babu gidan sayar da giya a Sudan, babu gidan karuwai a Sudan, babu gidan caca da sauran guraren sabon Allah, mata basa shiga harkokin shugabanci, to wannan kariyar da ya bawa Musulunci, sai Kasar Amerika ta dauki hayar wasu gurbatattun Musulmai suka tayar da zanga-zanga mai taken "HURRIYA-SALAMA-ADALA". ma'ana 'yanci, adalci da zaman lafiya, wato su sun gaji da dokokin Musulunci tsaurara suna neman 'yanci don suyi rayuwa irin na yahudu da nasara, akan haka suka kifar dashi, to Allah suka taba

A lokacin da suke dab da zasu kifar da Albashir, ya fito yayi rantsuwa yace Billahillazi zaku ce na fada muku idan kuka sake kuka hada kai da Amerika, Wallahi sai kunyi da na sanin abinda kuke min na zanga-zanga da tawaye, to bayan sun kifar dashi, shugaban Sojojin Sudan General Abdel Fattah al-Burhan da ya maye gurbinsa karen farautar Amerika da Isra'ila ne, nan take ya bude wa Kasar Isra'ila hanyar mubayi'ah, kuma kafin fara wannan yakin, a ranar 1-2-2023 General Al-Burhan ya gayyato Ministan harkokin waje na Kasar Isra'ila Eli Cohen zuwa Khartoum babban birnin Sudan, wannan ne abinda ya faranta ran Amerika ta cire manyan takunkumi da ta kakabawa Sudan lokacin mulkin Umar Albashir, kuma ta nemi Shugaban Sojojin ya mika mata Albashir don ta wulakantashi

An yaudari Mutanen Sudan da neman 'yanci, to ga inda 'yancin ya kaisu a yau, mutum sama da dubu dari uku suna sansanin 'yan gudun hijra a sati uku da aka fara wannan yakin, 'yan Sudan sama da dubu dari da hamsin sun tsere daga Kasar, an kashe mutane kusan dubu daya zuwa yanzu, asibitoci sun rufe, manyan kasuwanni sun rufe, babu inda za'a kai marassa lafiya, kafar internet na Kasar na neman rufewa gaba daya, harkokin bankuna na Kasar duk sun tsaya saboda mummunan harin bomb da akayi a babban bankin Kasar Sudan, farashin kudin Sudan yayi mummunan karyewa mafi muni a tarihi, a tsakanin sati uku da fara wannan yakin anyi barna a Sudan wanda za'a dauki tsawon lokaci kafin a gyara lamura, na karanta bayanin wani masanin tsaro yace za'a kai nan da shekaru 15 kafin Sudan ta dawo hayyacinta ko a gama wannan yakin

Wannan bayanin da nayi shinfidane kawai, ku biyoni a rubutu na gaba don jin abinda ya haddasa wannan yaki da tarihin yakin, da inda aka nufa, akwai babban darasi garemu akan wannan kazamin yaki da yake faruwa a Sudan
 
Muna rokon Allah Ya tausaya wa bayinSa salihai da kananan yara da mata dake Sudan Ya kawo musu mafita na alheri

Allah Ya sa fitinar ta cinye wadanda suka tayar da ita da wadanda suka tsara zanga-zangar kifar da shugaba Umar Albashir 


Game Da Tafiya A Motar Haya Kashi Na 3 - Dr Dukawa


HALIN DA WASU TASHOSHIN MOTA SUKE CIKI 

A bisa kiyasi, tashar Na’ibawa a Kano ba za ta gaza shekara arba’in (40) ba. Saboda an samar da ita ne a zamanin marigayi gwamnan tsohuwar jihar Kano Alhaji Abubakar Rimi (1979 – 1983). Amman har izuwa yau tashar tananan jiya ya yau: kango wanda babu wani abu da yake nuna ana samun kudi a wurin; babu kwalta, babu interlocks, babu dabe kowane iri! Zaiyar kasa. Sai yalwar leda da sauran nau’i na shara. Babu wani lafiyayyen makewayi. Da na bukaci wurin yin bawali sai aka nuna min wani uban juji a yammacin cikin tashar. Sai da roki wani dan bola jari cewar ya dan kauce zan kama ruwa. 

Na tabbatar idan ruwa ya sauka mummunan halin da tashar ke ciki ba zai gaza na tashar Unguwa Uku ta Kano ba, wacce na yi rubutu akan nata halin da take ciki a sherarar 2020. 

An yayyanka pilotai a cikin tashar Na’ibawa. Wasu an gina shaguna ana gudanar da ciniki wasu kuma an saka fandisho na gini ba a yi ginin ba. Babu Masallaci sai ‘yar musalla amman har da lasifika. Ko yaya aka yi a kasar Musulmi irin Kano za a yi tashar mota ta shekara arba’in ba a samar da masallaci ba sai abin ya daurewa mutum kai. Alhali ya kamata ace izuwa yanzu har dakin shan magani, da karamin dakin ATM da ofishin aika sako (akwatin gidan waya) na gaggawa, da kuma ofishin ‘yansanda ya kamata ace an samu.

Halin da na samu tashar mota a Yola da Jalingo bai sha banban da yadda na baro a Kano ba. Babu wani abu na cigaba. Sai turbaya da shara da bola.
Anan zan nanata kirana ga kananan hukumomi (LGAs) a Arewacin Najeriya cewar su tuna amanar da suka dauka na gudanar da ayyukan da aka zayyana a makale na hudu (fourth schedule) na Tsarin Mulkin Najajeriya. Daga ayyukansu akwai samarwa da kula da tashoshin mota. Wannan ba ya nufin a shata kango motoci su rika shiga suna lodi ‘yan rabanu (masu karbar kudin shiga) kuma suna karbar haraji kawai ba. 

Amman yana nufin a inganta tashoshi ta hanyar samar da yanayi mai kyau da tsabta da tsaro. Kunyoyin da suke karbar nasu kason a wurin direbobi su ma su sani cewar babban aikinsu shine su inganta sana’ar ta hanyar bibiyar hukumomi da neman su sauke nauyinsu da kuma taya hukumomin samar da wasu abubuwan inganta rayuwa a wurin sana’a. sabanin haka za su rika cin haram ne na wannan kudaden da suke karba.

Monday, 8 May 2023

'Yan sandan Najeriya sun ceto mutane 58 daga hannun 'yan bindiga

 


‘Yan sanda a Najeriya sun ce sun ceto mutane 58 da ‘yan ta’adda suka yi garkuwa da su a jihar Kogi, yayin da daya daga cikin wadanda aka yi garkuwa da sun ya rasa ransa yayin artabu tsakanin jami’an tsaro da ‘yan ta’addan

A cikin wata sanarwa da kakakin rundinar ‘yan sandan jihar Josephine Adeh ta fitar a wannan Lahadin, ta ce wannan nasara da suka samu wani bangare ne na aikin hadin gwiwa tsakanin rundunar da sauran jami’an tsaro, tare da hadin gwiwar ‘yan banga da mafarautan jihar. 

Adeh ta ce lamarin ya faru ne a dajin Udulu da ke Karamar Hukumar Gegu mai nisan kilomita 145 daga bababban birnin tarayya kasar. 

A cewarta, an yi musayar wuta tsakanin ‘yan ta’addan da kuma jami’an tsaro kuma daga bisani suka tsere suka bar mutanen da suka yi garkuwa da su.  

Sai dai bata bayyana inda aka sace mutanen ba da kuma tsawon lokacin da suka dauka a hannun ‘yan ta’addan.  

RFI

Game Da Tafiya A Motar Haya Kashi Na Biyu


 


Daga Dr Sa'idu Ahmad Dukawa

TSARIN DAUKAR FASINJA A TASHA

Bayan da na yi tambayi game da tsarin daukar fasinja a tashar mota, na sami bayanin cewa mutum zai iya zuwa tsahar Na’ibawa (wacce a yanzu aka sakawa suna “tashar Kano Line”) ya yi booking (biyan kudi kafin ranar tafiya). Don haka sai na je ofishin Adamawa Sunshine (wanda alal hakika shago ne a cikin tashar da dan teburi da mutumin da yake karbar kudi ya rubuta rasiti), na biya kudina ana kashegarin ranar tafiya.

Na tambaya mutum nawa ake dauka a mota kirar sienna? Aka ce min ana daukar mutum takwas ne, fasinja biyu a gaba, uku a tsakiya, uku a karshe. Amman fa Bature ya yi motar ne domin daukar fasinja biyar: guda a gaba, biyu a tsakiya, biyu a karshe. Don haka ana wuce kima (overload) na mutum uku. A motar ‘yankasuwa kuwa har mutum hudu ake sakawa a tsakiya, kamar yadda na ganewa idona a yayin dawowata daga Jalingo zuwa Kano. Allah ya kiyaye, a duk lokacin da aka gamu da hadari, za ta yiwu a yi asarar rayuka tara zuwa goma a cikin mota guda. A inda aka san kimar rai, duk yadda za a yi a rage asarar rai guda ana yi.

Ko me yasa dole sai an yi overload a motocin haya a Najeriya? Dalilan sanannu ne. farko dai akwai tsadar man fetur. Na biyu akwai biyan haraji hawan hawa, hukuma ta karba, kungiyoyi su amsa, yan kamasho su yaga, a dankawa ‘yan wururu masu taro fasinja daga hanya su kawo shi gindin mota, a dankawa masu gadin tasha, a yi ta mikawa jami’an tsaro kashi kashi (na kidaya shingen jami’an tsaro kimanin dozen guda a tsaknin Jalingo da Gombe kadai). Ga kuma tsadar kayan mota (spare parts) tunda kusan komai sai an yi odarshi, ba a kera komai a kasar. Ga mamallakin mota yana so ya mayar da kudinsa da wuri, don haka yana son a rika kawo balance mai tsoka a duk rana.

A karshe ga bukatar Direban motar na ya samu abinda zai shiga gida da shi ya sallami iyali. Idan aka hada duk wadannan bukatun akan fasinja kuma ba zai iya dauka ba. Don haka akan dole ake gwammacewa a cunkusa fasinja, wani a jikin wani, kamar kifin sardine.

Akwai kuma abinda yake ya shafi dabi’a ta rashin tsari da ci da zuci da rashin ganin kimar dan Adam wacce take tattare da mutane da yawa, barin idan sun san babu wata doka za ta hau kansu. Alal misali, na biya kudin kujera uku na tsakiya yayin da zan tafi, saboda tare da iyali zan yi tafiyar.

Amman ko da muka zo tasha sai muka taras an cushe wurin ajiyar kaya, babu inda zamu saka ‘yan kananan jakunkunanmu kwara biyu, wadanda idan mun yi tafiya a jirgin sama ba ma auna su, da su muke shiga jirgi, saboda karancin girma ko nauyi da suke da shi. Sai aka nemi wai tunda mu biyu ne kacal a tsakiya, wurin zai ishemu har kayanmu. Ni kuma nace ban amince ba. Daga dukkan alamu kuma sun riga sun sayar da wurin ajiyar kayana, sun karbi sakon kaya wanda shima na samu labarin kudin kujera ake biyansu. Na duba rasitin da aka bani ko akwai lambar wayar ofis sai na kai korafi sai naga in banda sunan na “Adamawa Sunshine” babu komai a jiki, babu lambar waya, babu adireshi! A karshe dai sai saukemu aka yi daga motar, ni da iyalina, na jira wata ta yi lodi bayan sa’a uku, sannan muka kama hanya.

A nan akwai bukatar ace daga cikin jerin masu karbar kudin shiga akwai wadanda suke sa ido wajen ganin an bi ka’ida, an cika alkawari, ko Allah ya sa albarka a harkar da kuma a rayuwarmu baki daya. Wasu shawarwarin da za su biyo baya da za su karfafi wannan, da yardar Allah.

Kada Ku Nemi Na Saki 'Yan Daba - Muhuyi Magaji Ya Gargadi 'Yan Siyasa

Kano Business Community Endorses Gov. Yusuf for Second Term

The leadership of the Kano business community, comprising representatives of 25 major markets across the state, has endorsed Gov...