Search This Blog

Sunday, 7 May 2023

Yin Waya Fiye Da Minti 30 A Sati Na Kara Hawan Jini —Bincike


Masana kiwon lafiya sun gano cewa yin waya na sama da minti 30 a mako guda na haddasa karuwar cutar hawan jini da kashi 12.

Rahoton da Kungiyar Likitocin Zuciya na Nahiyar Turai ta fitar a ranar Juma’a ya bukaci jama’a da su takaita yin waya domin kare lafiyar zukatansu.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa rahoton likitocin da aka wallafa a mujallar Digital Health yana nuna yin waya na sama da minti 30 a mako na kara barazanar kamuwa da cutar hawan jina da kashi 12 cikin 100.

Mujallar, wadda a mayar da hankali a kan yadda na’urorin zamani ke shafar lafiyar zuciya, ta ce hakan bai shafi yawan shekarun da mutun ya yi yana amfani da waya ko sanya waya a lasifika ba.

Farfesa Xianhui Qin na Jami’ar Aikin Likita tat Kudancin Guangzhou da ke kasa China, ya kara da cewa masu amfani da waya sun fi mara sa yi yiwuwar kamuwa da hawan jini da kashi 7 cikin 100.

Farfesa Qin ya a halin yanzu kusan biliyan 1.3 masu shekaru 30 zuwa 70 na da hawan jini, wadda ke iya kawo shanyewar barin jiki da kuma mutuwa farat-daya.

Masanin ya bayana cewa “Wayoyin hannu na fitar da maganadisun da ke kara hadarin kamuwa da hawan jini bayan wani lokaci.

“Duk da haka yanayin amfani da waya da ke kawo hawan jini ya bambanta a tsakanin masu kira ko amsawa, da kuma masu tura sakonni ko kuma yin wasanni da ita,” in ji Farfesa Qin.

AMINIYA

Saturday, 6 May 2023

Game Da Tafiya Da Motar Haya A Najeriya Kashi Na Daya

Daga 
Dr. Saidu Ahmad Dukawa

SHIMFIDA
A ranar Talata, 25/4/2023, na shiga motar haya daga Kano zuwa Yola, babban birnin jihar Adamawa a Najeriya. Ranar Alhamis kuma, 27/4/23, na shiga wata motar hayar daga Yola zuwa Jalingo, babban birnin jihar Taraba. Rabona da tafiyar motar haya wacce ta kai tsawan haka tun a shekarun 1983 zuwa 1984 a yayin da na yi hidimar Kasa (NYSC) daga jihar Kano zuwa jihar Bauchi, sai kuma jihar Lagos da na je bayan kammala hidimar kasa a wajejen shekarar 1985.

A wannan karon ma tafiyar ta taso min ne a dalilin wata hidimar Kasar, watau aikin kula da yadda jarrabawar shiga jami’o’i ta kasa (UTME) take gudana. Tun daga lokacin da aka nada Farfesa Is’haq Oloyede a matsayin Magatakardar Hukuma mai tsarawa da gudanar da jarrabawa domin shiga jami’a a Najeriya (JAMB), a shekarar 2016, ya fitar da sababbin tsare-tsare na yadda ake gudanar da wannan jarrabawar. Daga ciki akwai samar da kwamitoci daban daban, har guda goma sha daya (11), domin gudanar da ayyuka daban daban. Guda daga cikin wadannan kwamitoci shine wanda aka lakabawa suna a Turance da “Roving Group”. Watau kwamiti mai kewayawa santocin da ake gudanar da jarrabawa domin kula da yadda jarrabawar take gudana da nufin gano al’amuran da suke bukatar daukar mataki na gaggawa da kuma wadanda za a zauna a tsanake, a yi musu tunani, a samar da yadda za a ingantasu a shekara mai zuwa. Na sami kaina a cikin wannan kwamiti, a inda na shekara biyu ina aiki a Abuja, shekara guda a Adamawa, shekara uku a Kano, bana kuma aka bukaci na je aiki a Adamawa da Taraba.

Abubuwa uku kwamitin da na yi bayaninsa aka dorawa nauyin kula da su, kamar haka:

1. Yanayin tsaro a ciki da kewayen wurin jarrabawa (CBT Centre); saboda Farfesa Oloyede ya karbi aiki a yayin da a ake cikin kamarin kalu-balen tsaro akasa, musamman na ‘yan Boko Haram;

2. Yanayin tantance dalibai masu zana jarrabawa; saboda amfani da fasahar zamani na tantance masu zana jarrabawa (biometrics) da aka shigo da shi; da kuma

3. Yanayin da dakunan da ake gudanar da jarrabawar suke ciki, da inganci da yalwar na’urori masu kwakwalwa (computers); saboda sababbin santoci masu zaman kansu da aka yiwa rajista ta gudanar da jarrabawar.

Amman fa ba akan wannan aikin zan yi bayani ba, saboda aiki ne da ya shafi hukuma, kuma duk wani bayani ita ake turawa ita kuma ta fitar da wanda ya shafi al’umma ta rike na rikewa. Na dan yi wannan tsokacin ne domin a san dan kadan daga irin hidimar da ake yiwa jarrabawa. Zan yi wannan dan takaitaccen rubutun ne akan abubuwa guda biyar:

1. Tsarin daukar fasinja a tasha
2. Halin da wasu tashoshin mota
 suke ciki

3. Halin da titunan Najeriya suke ciki a shekara ta 2023

4. Yanayin tuki da yanayin larurar bukata a yayin tafiya

5. Yanayin tsaro da alakar jami’an tsaro da direbobin mota.

Babban burina da wannan rubutun shine fata da nake da shi na ko Allah ya sa masu ruwa da tsaki su ci karo da rubutun kuma ya sa su inganta al’amura game da abinda ya shafi tafiya a motar haya a Najeriya.
Manya daga cikin masu ruwa da tsaki kuwa sun hada da Kananan Hukomomi (Local Government Authorities), Kungiyoyin sufuri, da na mamallaka motocin haya, da na direbobin haya, da na ‘yan kamasho, da kuma jami’an tsaro, da sauransu. Zan yi kokarin takaita bayani domin gudun kosarwa. Kuma zan raba posting din kashi kashi duk dai saboda gudun kosawa.

(Za a cigaba da magana akan Tsarin Daukar Fasinja a Tashar Mota, da yardar Allah) 

Hukumar Lafiya ta Duniya ta ayyana karshen annobar Covid-19

A jiya Juma’a ce hukumar Lafiya ta Duniya ta ce an kawo karshen annobar Covid-19, wadda ta yi sanadin mutuwar mutane da dama tare da wargaza tattalin arziki da sha’anin zamantakewar duniya, sama da shekaru 3 bayan da ta ayyana ta a matsayin annoba. 

Shugaban hukumar Tedros Adhanom Ghebreyesus ne ya sanar da haka a jiya Juma’a, inda ya yi gargadin cewa har yanzu cutar na nan a matsayin barazana.

Wannan mataki na hukumar Lafiyar na zuwa ne bayan da kwamitin kwararru mai zaman kansa da ta nada a game da wannan cuta ta Covid ya ce cutar ba a bukatar mayar da hankali sosai a kan cutar daga hukumar.

Sai dai a cewar Tedros, hatsarin cutar bai kau ba, inda ya yi kiyasin cewa ta kashe sama da mutane miliyan 20 a fadin duniya, kimanin ninki 3 na mutane kusan miliyan 7 da aka ce ta kashe a hukumance.

A ranar 30 ga watan Janairun shekarar 2020 ce hukumar Lafiya ta Duniya ta ayyana cutar Covid-19 a matsayin annoba, makwanni bayan da ta bulla a birnin Wuhan na kasar China.
RFI 

Zaben Adamawa: An Ba Da Belin Kwamishina Hudu

 


’Yan sanda sun bayar da belin Kwamishinan Zabe na Jihar Adamawa da aka dakatar, Hudu Yunusa-Ari, bayan da ya yi kwana uku a tsare a hannunsu.

’Yan sanda sun cafke shi ne kan wata sanarwa mai cike da rudani da ya yi  cewa Sanata Aisha Dahiru Binani ta lashe zaben gwamnan jihar Adamawa, alhali ba a kammala karbar sakamakon karashen zaben ba.

Tun a lokacin INEC ta soke sanarwar, sannan ta bukaci ya gabatar da kansa a hedikwatarta da ke Abuja, amma maimakon ya je, sai ya yi layar zana.

Daga bisani hukumar ta rubuta Shugaban ’Yan Sandan Najeriya wasikar neman ya binciki kwamishinan zaben, kan yamutsa hazon da ya yi.

Amma wata wasika da ya aike wa shugaban ’yan sanda, Hudu ya ce ya yi sanarwar ne a bisa doka, saboda dalilan tsaro.

A ranar Talala ’yan sanda suka sanar cewa sun kama Hudu, wanda ya ce ba ya nadamar sanarwar da ya ya yi cewa Binani ta ci zabe.

Amma kakakin rundunar ’yan sandan Najeriya, Muyiwa Adejobi, ya sanar a ranar Juma’a cewa rundunar ta bayar da belin kwamishinan zaben.

Muyiwa ya cen an umarci Hudu ya rika zuwa hedikwatar rundunar a ranakun aiki domin ci gaba da binciken da ake gudarwa.

AMINIYA

Friday, 5 May 2023

#Hajj2023: Shugaba Buhari Ya Amince Da Cire Kaso 65 Na Kudaden Haraji Da Kamfanonin Jirage Ke Biya

A ci gaba da shirye-shiryen gudanar da aikin Hajjin shekarar 2023, Hukumar Alhazai ta kasa NAHCON ta gana da masu ruwa da tsaki a harkar sufurin jiragen sama a dakin taro na Hajj House dake Abuja. 

A sanarwar da Mataimakiyar Daraktar harkokin hulda da jama’a ta hukumar NAHCON, Hajj2023 Hajiya Fatima Sanda Usara ta fitar, tace an yi hakan ne domin inganta shirye-shiryen da suka kasance masu tasiri wajen jigilar maniyyata Hajji.
 
A taron shirye-shiryen kulla yarjejeniyar jigilar alhaza tare da masu jigilar kayayyaki da aka zaba, Alhaji Zikrullah Kunle Hassan ya bayyana matakan da hukumar ta riga ta dauka na dakile cikas da za a iya samu da zarar an fara jigilar Alhazan 

Shugaban NAHCON ya yi albishir da cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da rage kashi 65 cikin 100 na kudaden sufurin jiragen sama na jiragen sama.
 
Ya kuma sanar da cewa, domin tabbatar da an samar da man jirgi a wadace don jigilar alhazai , NAHCON ta yi shiri da Kamfanin Mai na Najeriya (NNPC) domin kawo karshen hakan. An shawarci masu jigilar maniyyatan da su gana da NNPC da nufin tattaunawa don gujewa matsala 

A cewar shugaban hukumar ta kuma tuntubi masana harkokin sufurin jiragen sama don samun shawarwarin kwararru kuma hukumar za ta ci gaba da bin shawarwarin domin amfanin alhazan Najeriya da kuma kare lafiyar alhazan baki daya 
 
Darakta Janar na Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Najeriya (NCAA), Kyaftin Musa Nuhu wanda ya halarci taron ya bayyana cewa, hukumar tasu ta duba dukkan filayen saukar jiragen sama na Hajji da aka tanada domin samar da tsaro da kayan aiki. Ya yi kira ga wadanda aka zaba da su bi ka’idoji da sharuddan yarjejeniya da za su sanya hannu. An kuma shawarce su da su cika sharuddan da za a fayyace a cikin yarjejeniyoyin domin NCAA a shirye take ta sanya takunkumin karya doka. 

Ya koka da batun jinkiri da soke jigilar jiragen sama kamar yadda aka samu a shekarar da ta gabata, yana mai bayyana hakan a matsayin mai yin tasiri a dukkan ayyukan da ma ya shafi ayyukan Saudiyya ma. A kan wannan cikas na dindindin, tun da farko Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama (GACA) ta gayyaci NCAA don auna irin tasirin da take da shi a ayyukan Hajjin filayen jiragen sama na Madina da Jeddah. Don haka, NCAA ta ษ—ora tsauraran matakai don guje wa sokewa da jinkirin tashin jirgin a wannan shekara.
 
Kaftin Nuhu da sauran masu jawabi a wurin taron sun bayyana damuwarsu kan rufe sararin samaniyar Sudan sakamakon yakin da ake yi a kasar. An bayyana cewa alhazai na iya yin tafiyar sa'o'i bakwai da rabi a kowace tafiya saboda yiwuwar sauya hanya.
 
A wani labarin kuma hudu daga cikin biyar din da aka zaba domin gudanar da jigilar daukar alhazai, sun bukaci karin lokaci kafin sanya hannu kan yarjejeniyar. Dukkansu  kamfanonin jiragen sama ne na cikin gida. 

A cewar ma’aikatan jirgin, akwai bukatar su ci gaba da tuntubar juna da yin lissafin kafin su koma tattaunawa da hukumar ta NAHCON don bayyana amincewarsu ta karshe zuwa ranar Talata 9 ga watan Mayu. 

Sai dai kamfanin FlyNas na Saudiyya ya rattaba hannu tare da nuna shirin fara jigilar Hajji na 2023. Don haka, an ci gaba da ci gaba da aiwatar da tsarin jigilar jirgin tare da FlyNas.
 
Tawagar farko ta aikin Hajji na 2023 da ta kunshi zababbun ma’aikatan NAHCON da ma’aikatan lafiya kadan ne ake sa ran za su bar kasar nan da ranar 21 ga Mayu, 2023.

Kotu ta ษ—aure Ekweremadu shekara tara a gidan yari

An yanke wa wani hamshaฦ™in ษ—an siyasar Najeriya, Ike Ekweremadu, da mai ษ—akinsa, hukuncin ษ—auri a gidan yari bayan kotu a Birtaniya ta same su da laifi kan yunฦ™urin safarar sassan jikin ษ—an'adam.

Kotun ta yanke musu hukuncin ne tare da wani likita "mai shigar musu tsakani" bayan sun kai wani matashi Birtaniya daga Lagos.

Yanzu dai, Sanata Ike Ekweremadu zai shafe kusan shekara goma a gidan yarin Birtaniya.

Sanatan mai shekara 60, da mai ษ—akinsa Beatrice 'yar shekara 56, sun so a cire wa matashin sashen jikinsa ne da nufin dasa wa 'yarsu Sonia 'yar shekara 25, kamar yadda ma'auratan suka bayyana wa Kotun Old Bailey
An kuma samu "mai shiga tsakani" Dr Obinna Obeta da matar sanata Ekweremadu, Beatrice, da laifi

Tun da farko kotu ta samu ma'auratan da likita Dr Obinna Obeta, mai shekara 50, da laifin haษ—a baki don ci da gumin mutumin ta hanyar cire ฦ™odarsa.

Ita ce shari'a ta farko a ฦ™arฦ™ashin dokokin haramta bautar zamani.

Yadda aka kama Sanatan Najeriya bisa zargin yunkurin cire sassan jikin mutum
24 Yuni 2022
Kotu ta samu Ekweremadu da laifin yunฦ™urin safarar sassan ษ—an adam
23 Maris 2023
Matashin da aka yi yunฦ™urin cire wa ฦ™oda domin bai wa ฦดar Ekweremadu
25 Maris 2023
Ike Ekweremadu, wanda alฦ™alin kotun ya bayyana a matsayin "jigon da ya shirya abin da ya faru gaba ษ—aya", zai yi zaman gidan yari tsawon shekara tara da wata takwas.

Hkaa kuma ta yanke wa Dr Obinna Obeta hukuncin ษ—aurin shekara 10 bayan alฦ™alin ya gano cewa shi ne ya samo mutumin da zai ba da gudunmawar wanda matashi ne talaka, kuma mai rauni.

Ita kuma matar sanatan na Najeriya, Beatrice Ekweremadu an yanke mata hukuncin ษ—aurin shekara huษ—u da wata shida saboda yadda ta ษ—an sa hannu wajen aikata laifin.

A wani zaman yanke hukunci da aka nuna ta talbijin, Mai shari'a Justice Johnson ya nunar cewa Ike Ekweremadu, mutum ne da "ฦ™imarsa ta yi matuฦ™ar zubewa".

Ya ce: "Masu fasa-ฦ™waurin mutane a tsakanin ฦ™asashen duniya don cire sassa jikin mutum, abin da suke aikatawa wani nau'in bautar da ษ—an'adam ne."

Mutumin da suka yi safarar tasa, wani talaka ne mai sana'ar tireda a Lagos, da suka kai shi Birtaniya don a cire masa ฦ™oda guda ษ—aya, da nufin dasa wa 'yar Ekweremadu.

Ya dai tsere ne saboda tsoron mutuwa, inda ya kai kansa ofishin 'yan sanda kimanin shekara ษ—aya da ta wuce kuma ya ba da rahoton abin da ya faru, bayan asibitin Royal Free Hospital ya nemi a dakatar da aikin da aka tsara yi a kan kuษ—i £80,000.
BBC 

Thursday, 4 May 2023

Wani Yaro Ya Kashe Mahaifiyarsa A Kano

Wani karamin yaro a unguwar Rimin Kebe da ke Karamar Hukumar Nassarawa a Jihar Kano ya daba wa mahaifiyarsa wuka lamarin da ya sa ta ce ga garinku nan.

Wani ganau mazaunin yankin, Muhammad Abdu, ya shaida wa Aminiya cewa lamarin ya faru ne yayin da aka sami jayayya tsakanin marigayiyar da dan nata da ake wa lakabi da Kwarangwal.


Ya bayyana cewa, “lokacin da muka ji ihunta mun garzaya gidan don kai dauki inda muka same ta kwace cikin jini male-male ga kuma yanka a jikinta.”

A cewarsa tuni wanda ake zargi ya cika wandonsa da iska bayan ya yi aika-aikar.

Haka kuma ya bayyana cewa daga baya an garzaya da marigayiyar Asibitin Koyarwa na Muhammadu Abdullahi Wase.

Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Alhamis, inda ya ce zai yi karin haske akan lamarin daga bisani.
AMINIYA 

Rano Air Zai Fara Aiki Ranar Lahadi

Daya daga cikin sabbin kamfanonin jiragen sama a kasar, Rano Air, ya ce zai fara aikin zirga-zirga a ranar Lahadi, 7 ga Mayu, 2023.

Kamfanin jirgin wanda ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na Twitter ranar Alhamis, ya ce gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje, zai kaddamar da jirgin da zai tashi daga filin jirgin sama na Aminu Kano.

Hukumar gudanarwar kamfanin na Rano Air na sanar da al’umma cewa gwamnan jihar Kano Dr. Umar Abdullahi Ganduje zai tashi da jirgin a ranar Lahadi 7 ga watan Mayu, 2023 a tashar jirgin kasa ta Malam Aminu Kano. Kano karfe 10:00 na safe. Jirgin kasuwanci na Abuja da Kano zuwa garuruwa daban-daban na Najeriya za su fara aiki nan take."

Jaridar PlatinumPost ta rawaito cewa Rano Air mallakin hamshakin attajirin dan kasuwa ne kuma hamshakin mai kasuwanci Man Fetur dan asalin Kano, Auwalu Rano, shi ne Shugaban Rukunin kamfanin A.A. Rano.

Kamfanin jirgin, wanda aka kafa a shekarar 2019, ya samu lambobi biyar na EMB 145, kuma yana aiki a Abuja.


Labari Cikin Hotuna : Kamfanin Flynas Ya sanya Hannu kan Yarjejeniyar Jigilar Alhazan Najeriya

Kamfanin Flynas dake kasar Saudiyya ya sanya hannu kan yarjejeniyar dibar maniyyata aikin Hajin bana

An gudanar da taron sanya hannun ne a hedikwatar hukumar alhazai ta kasa NAHCON dake babban birnin tarayya Abuja

Saudiyya Ta Yi Wa Messi Tayin Ninkin Albashin Ronaldo

 


Kungiyoyin kwallon kafa a kasar Saudiyya na zawarcin gwarzon dan wasan duniya, Lionel Messi, na kungiyar PSG, da tayin albashin da ya zarce na kowane dan wasa a duniya.

Rahotanni sun nuna cewa wata kungiya da ke zawarcin Messi a Saudiyya ta yi masa tayin albashin Naira biliyan 183.5 (Dala miliyan 400) a shekara, idan kwantaraginsa ya kare da PSG a wata mai zuwa.

Kafar labarai ta Telegraph ta kasar Birtaniya ta ce dan wasan ya fara tunanin duba tayin kuma tuni kungiyar ta fara tattaunawa da Kyaftin din na kasar Argentina kan kwangilar da take masa tayi, bayan dakatarwar da PSG ta yi masa.

Idan hakan ta tabbata, Messi zai rika karbar kusan ninki biyun albashin babban abokin hamayarsa Cristiano Ronaldo, wanda a halin yanzu Al Nassr ta kasar Saudiyya ke biyan sa Naira biliyan 96.3 Dala miliyan 210 a shekara, zuwa 2025.

Wannan sabuwar ta taso ne bayan da kungiyar PSG ta dakatar da Messi na tsawon mako biyu ba tare da albashi ba, saboda wata ziyara da ya kai Saudiyya ba da izinin kungiyar ba.

A baya dai an yi ta rade-radin kungiyar Al Hilal ta Saudiyya ce ke neman daukar Messi, daga baya da PSG ta takatar da shi kuma maganar ta kara tasowa.

AMINIYA

Kada Ku Nemi Na Saki 'Yan Daba - Muhuyi Magaji Ya Gargadi 'Yan Siyasa

Kano Business Community Endorses Gov. Yusuf for Second Term

The leadership of the Kano business community, comprising representatives of 25 major markets across the state, has endorsed Gov...