Search This Blog

Friday, 7 April 2023

Kano: Kungiyar ALGON Sun Gargadi Kwamitin Karbar Mulki Na NNPP Kan Zafafa Siyasa

Reshen jahar Kano na kungiyar Shuwagabannin kananan hukumomin Najeriya (ALGON) sun bukaci shugaban kwamitin mika mulki na jam’iyyar NNPP na jihar Kano da ya daina zafafa harkokin siyasa da haifar da tashin hankali a jihar tare da bayar da shawarwarin da ka iya haifar da hargitsi.

Shugaban ALGON na jihar Kano, Bappa Muhammad ya yi wannan kiran ne a wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a, inda ya mayar da martani kan zargin karkatar da kudaden al’umma da ake yi wa shugabannin kananan hukumomin jihar a tsakanin majalisunsu da ma’aikatar kananan hukumomi ta jihar domin bayar da tallafin karin zabe da ke tafe nan ba da jimawa ba. shugaban kwamitin mika mulki na gwamna na NNPP.

Jaridar SOLACEBASE ta ruwaito cewa ALGON a cikin sanarwar ya ce, ''An ja hankalin ALGON, jihar Kano kan wata 'Shawara ta Jama'a mai lamba 3' wacce ta fitar a sama mai take kuma AB Baffa Bichi ya sanya wa hannu, inda ta yi zargin cewa shugabannin kananan hukumomi na shirin yin hakan. karkatar da kudaden jama’a domin gudanar da zabubbuka masu zuwa na mazabar Jihohi da na tarayya a jihar.”

Sanarwar ta yi kira ga shugaban kwamitin da ya yi aiki da hankali domin irin wannan tashin hankalin jama’a ba zai iya tasowa ba a wannan tafiyar ta dimokuradiyya.

Sanarwar ta ce '' Zarge-zargen da ake yi na wannan dabi'a ya zama ruwan dare a duk lokacin da aka samu sauyi a sandar shugabanci, misalai da dama na da yawa," in ji sanarwar.


“Musamman muna so mu tunatar da mai rattaba hannu kan ‘Shawarwari’ da aka fadi akan irin wannan zargi da aka yi wa tsohon Gwamnan Jihar Kano, Dr. Rabi’u Musa Kwankwaso a shekarar 2014 na yin amfani da kudaden al’umma da ya karbo daga kananan hukumomi 44 da aka yi wa shugaban kasa. buri. Idan dai za a iya tunawa dai an yi zargin an karbo makudan kudade har naira miliyan saba’in daga kowace kananan hukumomi 44 da ake da su ba bisa ka’ida ba, wanda har yanzu shari’ar ta na kan gaban hukumomin yaki da cin hanci da rashawa’’.

Sanarwar ta kara da cewa, an yi hakan ne domin a daidaita bayanan, duk da cewa an bayar da shawarar ‘Shawarwari’ ne kafin zaben gwamna da kuma kaddamar da kwamitin rikon kwarya (wanda aka sanya wa hannu da kwanan wata 060323).

Kwamitin Abba Gida-Gida Ya Gargadi Kananan Hukumomi Kan Almubazzaranci

 


Kwamitin Karɓar Mulki na Gwamnan Kano mai jiran gado, Abba Kabir Yusuf, ya gargadi shugabannin kananan hukumomi 44 da ke jihar da manyan ma’aikatansu da su guji bari ana amfani da kudaden kananan hukumominsu ta hanyar da ta sabawa doka.

Shugaban Kwamitin, Abdullahi Baffa Bichi ya ce gargadin ya zama dole domin kuwa sabuwar gwamnatin ba za ta lamunci yin almubazzaranci da dukiyoyin al’ummar Jihar Kano ba.

A cikin wata takarda da Babban Sakataren Watsa labarai na zababben gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya sanya wa hannu, Baffa Bichi ya ce, “Mun sami labari cewa ana shirin amfani da kudaden kananan hukumomi wajen kammala zabuka a inda ba su kammala ba, a wasu kananan hukumomin Jihar Kano, wanda yin hakan ba dai-dai ba ne kuma ya saba wa doka.”

Abdullahi Bafa Bichi ya ce gwamnati mai jiran gado a jihar ba za ta bari a ɗauki kudaden al’umma a yi wa wata jam’iyyar siyasa aiki ba.

AMINIYA

#Hajj2023: Labari Da Dumiduminsa; Hukumar NAHCON Ta Sanar Da Kudin Kujerar Aikin Hajin Bana

 


Shugaban Hukumar, Alhaji Zikirulla Kunle Hassan ne ya sanarwa manema labarai hakan, a yayin wani kwarkwaryar taron da hukumar ta gudanar da shugabannin hukumomin alhazai na jahohin Najeriya wanda ya gudana a ranar Juma'a

Zikirulla yace karin kudin kujerar aikin Hajin na 2023 ya faru ne sakamakon tashin farashin canjin Dalar Amurka da kuma wasu inganta ayyukan kula da alhazai ta hukumomin Saudi Arabia suka yi

Shugaban ya kuma sanr da ranar 21 ga watan Afurilu a matsayin ranar karshe da hukumomin da abun ya shafa zasu sanyawa hukumar aikin hajin ta kasa kudaden Maniyyatan da zasu ta shi a jahohinsu ko kuma kamfanoninsu

Da yake warware yadda biyan kudaden zai kasance tsakanin shiyyoyi ko jahohin Najeriya, Kunle ya ce Jahohin dake yankin Arewa maniyyatansu zasu biya naira miliyan biyu da dubu dari tara da sha tara (2,900,19,000.00) 

Sai kuma jahohin da zasu tashi ta jahohin Maiduri da Yola, su kuma maniyyatan zasu biya naira miliyan biyu da dubu dari takwas da casa'in ( 2,890,000.00). Yayin da jahar Edo zasu biya naira miliyan biyu da dubu dari tara da sittin da takwas (2,968,000.00). Sai Ekiti da Onda su kuma zasu biya naira miliyan biyu da dubu dari takwas da tamanin (2,880,000.00)

Haka kuma jahohin Cross River da Osun zasu biya miliyan biyu da dubu dari tara da arba'in da takwas (2,943,000.000) da kuma miliyan biyu da dubu dari tara da casa'in da da uku (2,993,000.000)

Sai kuma jahohin Lagos da Ogun da Oyo, su kuma zasu biya naira miliyan biyu da dubu dari tara da casa'in da tara (2,999,000.000)

Sai yankunan Kudu masu Kudu da Kudu maso gabas, su kuma maniyyatansu zasu biya naira miliyan biyu da dubu dari tara da sittin da takwas (2,968,000.000)

Daga na Shugaban Hukumar ya ayyana kamfanonin jiragen da gwamnatin Najeriya ta sahalewa yin jigilar maniyyatan na bana da suka hada da NAHCON  Azman Air, Max Air, Air Peace, Flynas, Aero contractors, Arik Air da kuma Value Jet Air 


Fiye da kashi 48 na al'ummar Afrika ba sa samun kulawar lafiya- WHO

 


Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta ce ‘yan Afrika miliyan 672 wanda ke wakiltar kashi 48 na al’ummar nahiyar basa samun kulawar lafiyar da ya kamata yayinda suke rayuwa cikin cutuka.

WHO ta ce dai dai lokacin da kasashe ke baje hajar gagarumin ci gaban da suka samu a bangaren kiwon lafiya, yayin bikin ranar Lafiya ta Duniya har yanzu Afrika na ganin mummunan koma baya a bangaren.

Daraktar hukumar WHO shiyyar Afrika Dr Matshidiso Moeti ta ce bangaren kiwon lafiya na ci gaba da samun koma baya a nahiyar wanda ke da nasaba da rashin kulawar shugabanni don habaka sashen.

A sanarwar da ta fitar a ranar lafiya ta Duniya wato World Health Day da ke gudana a kowacce ranar 7 ga watan Aprilu, shugabar ta WHO reshen Afrika, ta ce gazawar bangaren lafiya ya haddasa karuwar cutuka a sassan nahiyar da kuma tsanantar cutuka masu hadari.

Dr Matshidiso Moeti ta ce abin takaici yadda hatta kananun cutukan da basu kai su yi kisa ba, su ke iya kashe tarin jama’a a nahiyar ta Afrika saboda gurguncewar bangarorin kiwon lafiya.

A cewar jami’ar akwai karancin tsare-tsaren tafiyar da bangarorin kiwon lafiyar da kuma kin sanya kudi ga sashen kamar yadda ya kamata.

Haka zalika shugabar ta WHO a Afrika ta kuma koka da rashin kwararrun jami’an kiwon lafiya da kasashen nahiyar ke fama da kamfarsu.   

Moeti ta bayyana cewa tasirin illar da annobar covid-19 ta yiwa nahiyar da kuma illolin dumamar yanayi da tuni kasashen nahiyar suka fara ganin tsanantarsu, sun sake wargaza kokarin kasashen na bunkasa bangaren lafiya.

RFI

Ganawar da ‘yan majalisar wakilan jam’iyyun adawa suka yi a Najeriya sun yi azarɓaɓi - Masana

 


Masu sharhi kan harkokin siyasa a Najeriya na ci gaba da tsokaci a kan ganawar da ‘yan majalisar wakilan da suka fito daga bangaren jam’iyyun hamayya suka yi a makon nan.

Ganawar dai ta samu halartar sabbin ‘yan majalisun da kuma wadanda aka sake zaba domin wakiltar jama’arsu a majalisa ta 10 da ake shirin kafawa a watan Yunin 2023.

Farfesa Kamilu Sani Fagge, malami ne a tsangayar siyasa a Jami’ar Bayero ta Kano, ya shaida wa BBC cewa, irin wannan ganawa rikita-rikitar siya ce kawai.

Ya ce: “ A gaskiya sun yi sauri wajen gudanar da wannan taro, to amma ina ga sun yi kokari ne da ake cewa a tauna tsakuwa don aya ta ji tsoro domin idan an zo an rantsar da majalisar, kuma ba su yi wani abu da zai kawo rudani ba, to ko shakka babu ba za a yi da su a majalisar ba.”

Ya ce, ya kamata ‘yan majalisar da suka yi wannan taro su sani cewa har yanzu fa akwai sauran zaben ‘yan majalisun da ba a kammala su ba.

Malamin ya ce: “ A ka’idar zabe na majalisar wakilai kafin a ce jam’iyya na da rinjaye, dole sai tana da kujeru guda 180, wato rabin kujeru 360 din da ake da su a majalisar ke nan.”

Ya ce, “ To ko da wadannan ‘yan majalisar da suka fito daga jam’iyyun hamayya sun hade kansu, to ba su yi rinjayen da za a ce sun kafa rinjaye a majalisar ba.”

Farfesa Kamilu Sani Fagge, ya ce a yanzu a majalisar wakilan babu jam’iyyar da ke da wakilai 180, don haka za su iya hada gwiwa su yi aiki tare, to amma kuma idan aka yi hakan a gaba za a iya samun matsala musamman idan aka zo batun rabon mukamai.

Ya ce, “ Idan har aka samu matsala a tsakaninsu to ita kanta majalisar da ma mambobinta ba za su ji dadin aiki ba, saboda rarrabuwar kawuna.”

BBC

Wednesday, 5 April 2023

Kujerar Dan Majalisa: Ban Gamsu Da Nasarar NNPP Ba, Zan Tafi Kotu – Dan Ganduje


 Umar Abdullahi Gandujedan Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Ganduje, wanda ya tsaya takarar dan Majalisar Wakilai a jam’iyyar APC, ya ce bai yarda da sakamakon zaben da ya ba NNPP nasara ba.

Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) dai ta ayyana Injiniya Tijjani Abdulkadir Jobe a matsayin wanda ya lashe kujerar dan majalisar a mazabar Dawakin Tofa/Tofa/Rimin Gado, a jam’iyyar NNPP.

Jaridar Aminiya ta rawaito cewa, Tuni dai Umar, wanda aka fi sani da Abba Ganduje ya maka Tijjani Jobe a gaban kotun sauraron kararrakin zabe.

Abba, ta bakin lauyansa, Barista A.T Falola, ya kuma kalubalanci INEC kan ayyana Jobe a matsayin dan takarar da ya samu rinjayen kuri’un da aka kada a lokacin zaben.

Da ya ke gabatar da kara a gaban kotun, Falola ya roki kotun da ta gudanar da shari’ar a kan Jobe da kuma jam’iyarsa ta NNPP mai sakatariya a unguwar Sharada a Kano

Bukukuwan Easter: Gwamnati Ta Ayyana Juma’a Da Litinin A Matsayin Ranakun Hutu

 


Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranakun Juma’a da Litinin, 7 da 10 ga watan Afrilu a matsayin hutu albarkacin bukukuwan Easter da Kiristoci za su yi a fadin Najeriya.

Ministan Cikin Gida, Rauf Aregbesola ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da Babban Sakataren ma’aikatar, Shuaib Belgore, ya fitar a Abuja ranar Laraba.

Ya bukaci mabiya addinin na Kirista da su yi amfani da lokacin wajen kwaikwayon halayen sadaukarwa, kaunar juna, yafiya, soyayya, hakuri da zaman lafiya da Annabi Isah (A.S) ya koyar.

Ministan ya kuma bukace su da su yi amfani da lokacin wajen yi wa Najeriya addu’o’i na musamman saboda kalubalen tsaron da take fama da su.

“Tsaro sha’ani ne da ya shafi kowa. Saboda haka, nake kira ga ’yan Najeriya da ma ’yan kasar waje mazauna kasarmu da su ci gaba da nuna halin kishin kasa ta hanyar taimaka wa jami’an tsaro wajen dawo da zaman lafiya da tsaron rayuka da dukiyoyin ’yan kasa,” in ji shi.

Ya kuma ba da tabbacin cewa gwamnati na yin duk kokarinta wajen ganin an mika mulki lami lafiya bayan kammala zaben sabuwar gwamnati.

AMINIYA

Tuesday, 4 April 2023

An Kama Donald Trump Kan Zargin Aikata Laifuka

An kama Tsohon Shugaban Kasar Amurka, Donald Trump kan zargin aikata laifuka.

An kama shi ne ranar Talata yayin da aka gurfanar da shi a gaban kotun hukunta manyan laifuka ta Manhattan.

An tsare ‘yan sandan da suka yi sanadin mutuwar matashi a Filato
’Yan bindiga sun yi garkuwa da matar Dagaci da danta a Kano
Ana zargin tsohon shugaban ne da biyan wata mai fina-finan batsa, Stormy Daniels toshiyar baki don kada ta yi bayani game da alakar nema a tsakaninsu lokacin da yake takarar shugaban kasa a zaben 2016.

Shi ne tsohon shugaban Amurka na farko da aka taba kamawa a tarihin kasar.

To sai dai, a lokuta da dama Trump ya musanta zargin.

Sai dai Trump ya ce duk wadanan tuhume-tuhumen da ake masa ba komai ba ne face yi wa takararsa ta neman wa’adi na biyu zagon kasa.
AMINIYA 

Yadda masu son muƙamin shugaban majalisa ke sayen ƙuri'un sanatoci - Ndume

 


A Najeriya bayan kammala zaɓukan ƙasar a yanzu hankali ya karkata kan shugabancin zaurukan majalisun dokoki.

Tuni dai wasu 'yan majalisun da ke son ɗarewa kujerun shugabancin majalisun suka fara bayyana sha'awarsu ta hanyar kamun ƙafa a wajen masu ruwa da tsaki na jam'iyyunsu da kuma zaɓaɓɓun 'yan majalisar.

Sai a watan Yuni mai zuwa ne za a ƙaddamar da majalisar dokokin ta goma, daga nan kuma a fara shirye-shiryen zaɓen shugabannin majalisun.

To sai dai wasu 'yan majalisun sun fara zargin cewa ana amfani da kuɗi wajen sayen bakin 'yan majalisun domin zaɓen wasu a matsayin shugabannin majalisun.

Sanata Ali Ndume ɗan majalisar dattawa ne daga jihar Borno ya kuma shaida wa BBC cewa akwai zargin da ake yi na cewa wasu na amfani da kuɗi wajen ganin sun samu ɗarewar kujerar shugaban majalisar dattawa.

Ya ce a yanzu siyasar ƙasar masu hannu da shuni, ko masu kuɗi su ne ke juya ɓangaren siyasar ƙasar.

''Dandalin siyasarmu ya cika da irin waɗannan mutanen da suke ganin za su iya sayen komai suke so da kuɗi'' in ji Sanata Ndume.

Dan majalisar dattawan ya ce a baya ana maganar cewa ana sayen ƙuri'ar talaka, matakin har ya kai ga talakawan ƙasar suna ganin komai nasu na sayarwa ne a ɓangaren zaɓen ƙasar.

'A yanzu har ƙuri'ar sanata ake saya'

Majalisar Dattawa

ASALIN HOTON,NIGERIAN SENATE

Dan majalisar dattawan ya ce matakin ya kai a yanzu har ƙuri'ar sanata ma ana so a saya.

Ya yi zargin cewa a yanzu masu son ɗarewa kujerar shugabancin majalisar dattawan sun fara sayen ƙuri'un sanatoci.

''Akwai sanatocin da suke bai wa 'yan majalisar dattawa kuɗi a kan suna so su nemi shugabancin majalisar'' In ji Ali Ndume.

Ali Ndume ya ce bayan kwarewa a majalisar, idan mutum yana da kuɗi to damar da yake da ita ta zama shugaban majalisar ta fi yawa.

Sanatan ya kuma yi zargin cewa a yanzu akwai sanatocin da ba su da kwarewa a aikin majalisar, amma suna son mukamin shugaban majalisar dattijai.

''Amma saboda suna da kuɗi, amma yanzu suna son ɗarewa shugabancin majalisar, kawai saboda suna da kuɗi''.

'Kamun ƙafa da kuɗi a maimakon cancanta'

Ali Ndume

ASALIN HOTON,SANATA ALI NDUME/FACEBOOK

Dan majalisar ya kuma yi zargin cewa ba kawai sanatocin masu muradin shugabancin majalisar ke saya ba, har da sauran hukumomi.

''A yanzu duk abinda kuɗi bai baka ba a Najeriya to sai in kuɗin ne ya gaza, kuma idan ka ƙara za ka samu'', in ji Ndume.

Dan majalisar ya ce abu biyu ne a yanzu suke yin tasiri wajen samun shugabancin majlisar wato da kamun ƙafa da kuma kuɗi, maimakon cancanta.

Sanata Ndume ya kuma yi ƙorafin cewar a yanzu maimakon ya mayar da hankali kan cancanta domin zaɓen shugaban majalisar, an mayar da hankali wajen kamun ƙafa da kuma bayar da kuɗi.

'Ya kamata a bi cancanta maimakon tsarin shiyya-shiyya'

Sanata Ali Ndume ya kuma ce bai ga dalilin da zai sa a bi tsarin shiyya-shiyya a shugabancin majalisar dattawan ƙasar ba, a cewarsa kamata ya yi a bi cancanta.

''A lokacin babban zaɓe na yadda da batun shiyya-shiyya, amma a zaɓen da za a yi tsakanin waɗanda sun riga sun ci zaɓe ban goyi bayan shiyya ba'', in ji shi.

A cewar ɗan majalisar bin tsarin shiyya-shiyya zai haifar da samun shugabannin majalisar waɗanda ba su cancanta ba.

''Akwai wasu fa a majalisar nan waɗanda suna da tabo na laifi, sannan a matayinmu na dattawa, kuma a ce an sa mana shugaba wanda ba dattijo ba''?, a cewarsa.

Ya ce kamata ya yi a bar mambobin majalisar da kansu, su zaɓi wanda suke ganin ya cancanta.

Kujerun shugaban majalisar dattawa da ta kakakin majalisar wakilan Najeriya na da matuƙar muhimmanci da tasiri a siyasar Najeriya.

BBC

Gwamnatin Najeriya Na Zargin Peter Obi Da Cin Amanar Kasa

 


Gwamnatin Tarayya ta shawarci dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar LP a zaben da ya gabata, Peter Obi, da ya guji tunzura jama’a su tayar da zaune tsaye kan sakamakon zaben da ya gabata.

Ministan Yada Labarai da Al’adu, Alhaji Lai Mohammed ne ya bayar da shawarar yayin wata tattaunawarsa da kafafen yada labarai a birnin Washington DC na Amurka.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya rawaito cewa Ministan ya je Amurka ne don tattaunawa da kafofin kan abubuwan da suka wakana yayin zaben da ya gabata a Najeriya.

NAN ya ce ya zuwa yanzu, Ministan ya tattauna da jaridar Washington Post da Muryar Amurka da mujallar Foreign Policy da kuma kamfanin dillancin labarai na AP.

Lai Mohammed ya kuma gargadi Peter Obi da cewa ba daidai ba ne ya rika neman hakkinsa a kotu, sannan kuma ya rika kokarin tayar da zaune tsaye a daya bangaren.

“Obi da Mataimakinsa Datti, bai kamata su rika yi wa zababben Shugaban Najeriya, Bola Tinubu na APC barazana cewa muddin aka rantsar da shi ranar 29 ga watan Mayu mai zuwa, Dimokuradiyya ta kare a Najeriya.

“Wannan cin amanar kasa ne. Neman tayar da zaune tsaye ne. Kuma abin da suke kokarin yi ke nan.

“Kalaman Obi dan ko a mutu ko a yi rai ne, bai mai son Dimokuradiyyar da yake ikirari ba ne shi, saboda mai sonta bai kamata ya yi amanna da ita kawai lokacin da ya lashe zabe ba,” in ji Ministan.

Kada Ku Nemi Na Saki 'Yan Daba - Muhuyi Magaji Ya Gargadi 'Yan Siyasa

Gimba Kakanda Celebrates Abdulmumin Jibrin at 50

Public affairs commentator and writer, Gimba Kakanda, has described Hon. Abdulmumin Jibrin as an archetype of a young Nigerian w...