Search This Blog

Friday, 3 February 2023

Babu Kasar Da Ta Taba Sauya Kudi A Lokacin Zabe Sai Najeriya —El-Rufai

Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya bayyana cewar babu matsala a sauya fasalin takardun kudi, amma duk duniya babu kasar da ta taba sauyawa a lokacin zabe sai Najeriya.

El-Rufai ya yi zargin akwai gwamnan da shi kadai ya karbi sabbin kudi har na Naira miliyan 500 a kasar nan

Ya bayyana hakan ne cikin wata hira da ya yi da sashen Hausa na BBC, inda ya ce an yi tsarin ne don masu kudi, amma da yawansu tsarin ba zai shafe su ba; zai kare ne a kan talaka.

“Babu laifi game da sauya kudi, kowace kasa na yi amma babu inda aka taba sauya kudi a lokacin zabe kuma aka bayar da wa’adi kadan, a ina aka taba yin haka a duniya?

“’Yan siyasa da manyan ’yan kasuwa da aka yi tsarin dominsu, suna da hanyoyin da za su samu kudin ba tare da sun wahala ba, wasu daga cikinsu su ke juya bankunan, amma wane hali talakawa da kananan ’yan kasuwa za su shiga?


“Duka gwamnonin APC sun gana a kan wannan matsalar, mun ga yadda mutane ke shan wahala, mun goyi bayan sauya kudi amma wa’adin da aka ware kamata ya yi a debi watanni.


"Mun bukaci CBN da gwamnoni da manajojin bankuna mu zauna don tattauna wannan matsalar domin mu yi aiki tare don warware wannan matsala, kamata ya yi a ce mun tsara yadda za mu bi mutane zuwa gidajensu, kauyukansu ba wai tilasta musu zuwa bankuna masu nisan kilomita don sauya kudadensu ba.


“Ina tabbatar muku wannan sauyin kudin bai shafi ’yan siyasa ba, saboda suna da kudi kuma suna da hanyar samun kudaden

“Sun shirya sosai, talakawa ne kadai ba su san yadda za su samu kudin ba; ko a jiya an fada mana akwai gwamnan da shi kadai aka bai wa miliyan 500 na sabbin kudi,” in ji shi

AMINIYA 

Babu Wanda Nake Tsoro —El-Rufai Ga ‘’Yan Fadar Buhari’

 


Gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai ya kalubalancin ’yan fadar shugaban kasa da yake zargi da zagon kasa ga takarar Bola Tinubu a zaben shugaban kasa da ke tafe. 

Tun a ranar Laraba El-Rufai ya fara tayar da kura da zargin cewa akwai jami’an Fadar Shugaban Kasa da ke neman yi wa takarar Tinubu kafar ungulu.

A wata hirarsa da Sashen BBC na Hausa, an ji shi yana cewa, “Na rantse babu mahalukin da nake tsoro a duk fadin kasar nan.

“Don ana ganin girmn mutum ba soronsa ake ji ba; Amma idan muna girmama mutum, amma yana nuna shi ba babba ba ne, to wallahi za mu ake shi.”

BBC sun fitar da somin-tabin hirar ce kafin a fitar da shi gaba dayansa.

A ranar Laraba, a waya hira da shirin Sunrise Daily na gidan alabijin na Channels ne El-Rufai ya yi zargin akwai magoya baan wadanda suka nemi takarar shugaban kasa a APC wanda Tibubu a lashe da ke fakewa da Shugaba Buhari domin cimma manufofinsu.

A cewarsa, “Suna so mu fadi zabe saboda hakarsu ba ta cim ma ruwa ba; suna da ’yan kararsu , amma an kayar da ’yan kararsu a zaben dan kakara. “Suna so mu fadi zabe, suna fakewa  da shugaban kasa da abin da yake ganin daidai ne,” in ji El-Rufai.

Mai dakin shugaban kasa, Aisha, ta mara wa kalaman na El-Rufai baya, inda ta wallafa bidiyon zargin nasa a shafinta na Instagram.

A zargin na El-Rufai ya i nuni ga wasu da ba mambobin APC ba ne da ke ke fakewa da shugaban kasa wajen cim ma bukaunsu.

Amma Ministan Yada Labarai da Raya Al’adu, Lai Mohammed, ya ce gwamnati ba ta da masaniyar wadanda ke wa Tinubu zagon kasa a Fadar Shugaban Kasa.

A cewarsa, Buhari na daukar daukacin ’yan akra da matsai daya, domin ganin an gudanar da sahihin zabe kuma yana goyon baan Tinubu dari bisa dari.

Thursday, 2 February 2023

Cibiyar Koyar Da Ayyukan Hajji Ta NAHCON, Za Ta Fara Gudanar Da Harkokin Koyarwa


Hukumar Alhazai ta Najeriya (NAHCON), Cibiyar Aikin Hajji  za ta fara gudanar da harkokin karatun ta na shekarar 2023/24 a ranar Talata 7 ga Fabrairu, 2023 rukunin farko na dalibai.

Taron budewar wanda  Ministan ilimi, Adamu Adamu zai kaddamar da da shi, yayin da ministan babban birnin tarayya, Muhammad Musa Bello, zai kasance babban bako na musamman.

A sanarwar da mataimakin daraktan harkokin yada labarai da hulda da jama’a na hukumar NAHCON, Mousa Ubandawaki, and yace Cibiyar za ta fara ne da shirin sati 4 na bayar da takardar shaida ga dalibanta na "Tsarin Gudanar da Ayyukan Hajji da Umrah".

Shugaban hukumar, Alhaji Zikrullah Kunle Hassan, ya bayyana farin cikinsa da kafuwar wannan cibiya. “Muna gaggauta taya dukkan masu ruwa da tsakinmu murnar wannan nasarar da muka samu. Ba za mu iya yin da'awar cewa mun cimma wannan kawai ba. Don haka, mun fahimci gudummawar da hukumar da ta gabata ta bayar. Don haka ina kira ga masu ruwa da tsaki da su hada kai a matsayin abokan hadin gwiwa don daukaka wannan cibiya zuwa kololuwar matsayi ko da kuwa ba za mu bar wani abu ba wajen ganin an kiyaye mutuncin masu gudanar da aikin Hajji a nan gaba ba tare da wata tangarda ba.

Cibiyar na daya daga cikin kudirin hukumar da ke da burin gina kwararrun masu lura da aikin Hajji don gudanar da aikin Hajji a nan gaba. Tunanin kafa Cibiyar Hajji yana kunshe ne a cikin dokar kafa hukumar NAHCON Ta 2006 kuma tana kan gaba wajen tabbatar da kafuwar cibiyar 

Daga yanzu Bankuna Zasu Rinka Bayar da Sababbin Kudi A Kan Kanta

Babban Bankin Najeriya (CBN) ya ce daga yanzu Bankuna Zasu rinka bawa mutane kudi a kan Kanta, sabanin umarnin da ya bayar na baya kan cewa sai a Na'urar ATM kadai zasu sanya kudaden domin masu hulda dasu su cira.

Hadimin Shugaban kan harkokin kafafen yada labarai na yanar Gizo, Bashir Ahmed ne ya wallafa wannan labari a shafinsa na Instagram 
Za a iya tunawa cewa A ranar da Gwamnan Babban Bankin Najeriya Ya gana da Shugaba Buhari ne ya fitar da sabuwar sanarwar da ta ce ko bayan Karewar Wa'adin kashe tsofaffin kudi, Bankuna Zasu ci gaba da karbarsu domin mikawa Babban Bankin 

Kotun Koli ta sake tabbatar da Hajiya Laila Buhari a matsayin 'Yar Takarar Sanatan PDP Ta Kano Tsakiya

A ranar Alhamis ne kotun koli ta sake tabbatar da Hajiya Laila Buhari a matsayin ‘yar takarar Sanatan Kano ta tsakiya a jam’iyyar PDP.

SOLACEBASE ta ruwaito cewa a baya kotun daukaka kara ta tabbatar da Laila Buhari ta soke zaben Danburan Nuhu.

Kotun kolin da ta yanke hukuncin da mai shari’a Muhammad Lawal Garba ya karanta, ta yi watsi da dukkan dalilan daukaka kara ta Danburam Nuhu.

Jastis Garba na tare da Jastis Kudirat Kekere Ekun, da Jastis Saulawa da Jastis Ibrahim Jauro, da Jastis Emmanuel Agim

Cikakken labarin zai zo muku nan gaba 

Wednesday, 1 February 2023

Atiku Abubakar Zai Kaddamar Da Makarantar Haddar Alkur'ani A Kano


 Dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, zai kaddamar da makarantar sakandaren kwana ta haddar Al-Kur’ani mai dalibai 500 a Jihar Kano.

Atiku zai bude wannan makarantar haddar Al-Kur’ani ce a unguwar Gunduwawa da ke Karamar Hukumar Gezawa, a yayin ziyarar yakin neman zabensa a Jihar Kano, wadda za a gudanar ranar 9 ga watan Fabrairun da muke ciki.

Wannan makarantar haddar Al-Kur’ani “Na da wurin kwanan dalibai mata 250, maza 250, kuma za su rika haddace Al-Kur’ani a cikin wata bakwai, kafin su tafi makarnatun gaba da sakandare,” inji kakakin kwamitin yakin neman zaben Atiku a Jihar Kano, Sule Ya’u Sule.

Sanata mai wakiltar Kano ta tsakiya, Malam Ibrahim Shekarau ne dai ya gina makarantar ta haddar Al-Kur’ani mai daukar dalibai 500 a matsayin aikinsa na raya alu’m

Sule Ya’u Sule ya sanara ranar Laraba cewa, Atiku zai kaddamar da makarantar ce a ranar taron yakin neman zabensa, ko kuma washegari.

A cewarsa, “Wazirin Adamawa zai zo Kano ranar 9 ga Fabrairu, don haka jama’ar Kano ku shirya ganin dan takara mai karsashi da koshin lafiya.

“Atiku ba ba irin ’yan takarar na ba newadanda cikinsu wani da kyar yake magana,  wani ko makirfon ba ya iya rikewa, wani kuma cewa ya yi ya zo Kano ne don ya yi rawa.”

(AMINIYA)

Hajj2023: Hukumar Alhazai Ta Kano Za Ta Fara Gudanar Da Bitar Alhazai Ga Maniyyata Aikin Hajin bana


Sakataren Hukumar Jin dadin Alhazai ta Jihar Kano, Alhaji Muhammad Abba Danbatta, shi ne ya bayar da wannan umarni ga dukkan Shugabanni da Malaman Bita, na Bitar mako-mako dake fadin jahar Kano 
A sanarwar da Mataimakin Sakataren kwamitin malaman Bitar na Jaha, Malam Dahiru Kabiru Guringawa ya fitar, ta ce akwai shugaban kwamitin Bitar, Sheikh Haroon Muhd Sani Ibn Sina yace, za a fara gudanar da bitar ce daga ranar Asabar 4 ga watan Fabarairu na 2023 da karfe 10 na safe 

Za a fara gudanar da Bitar ce a dukkanin Cibiyoyin bitar dake fadin jahar Kano. 

A saboda sai sanarwar ta yi kira ga dukkanin Jami'an Alhazai na kananan hukumomi dasu tabbata sun sanarwa da dukkanin maniyyatansu don su halarta 

Akwai Makiyan Tinubu A Fadar Shugaban Kasa – El-Rufa’i

 


Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’i, ya yi zargin cewa akwai makiyan dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar APC, Bola Tinubu a Fadar Shugaban da suke kokarin ganin sun kai shi kasa.

Ya bayyana haka ne yayin tattaunawarsa da gidan talabijin na Channels, a cikin shirinsu na Sunrise Daily da safiyar Laraba.

El-Rufa’i ya ce mutanen, wadanda bai bayyana sunansu ba, sun fusata ne tun lokacin da aka kayar da dan takararsu a zaben fid-da gwani na APC.

Ya kuma ce mutanen na fakewa da bukatar ganin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi abin da ya dace.

“Wadannan mutanen na kokarin fakewa da bukatar Buhari ya yi abin da ya dace. Zan bayar da misalai biyu; wannan batun na biyan tallafin mai wanda ya ke sa Najeriya ta kashe makudan kudade abu ne da dukkanmu mun dade da amincewa a cire shi.

“Sai da ma na tattauna da Shugaban Kasa a kan haka, inda na nuna masa dalilin da zai sa dole a cire. Saboda ta yaya zaka ware biliyan 200 don manyan ayyuka sannan ka kashe tiriliyan biyu wajen biyan tallafi? Wannan maganar muka tattauna da shi a 2021, kuma aka amince za a cire saboda kudin sun tashi sosai

“Misali na biyu kuma shi ne canjin kudi. Ya kamata a fahimci Shugaban Kasa. Mutane na zargin Gwamnan CBN, amma ba haka batun yake ba. Idan muka koma tarihi, ko zamanin mulkin Buhari na soja, ya canza kudi saboda maganin barayi da masu jibge haramtattun kudade a gida.

Kalaman na El-Rufa’i dai na zuwa ne mako daya bayan Tinubu ya yi zargij akwai masu yi masa zagon kasa a cikin jam’iyyarsa, wadanda ya ce ba sa so ya lashe zaben.

Dan takarar ya yi zargin cewa da gangana aka kirkiro wahalar man fetur da canja fasalin kudi domin a yi masa zagon kasa.

(AMINIYA)

Shugaban Hukumar NAHCON Ya Karbi Sabon Kwamishinan Kudu Maso Gabas

Dokta Afikpo ya zama Kwamishinan NAHCON ne bayan rasuwar wakilin shiyyar siyasa, Alhaji Ibrahim Ogbonnia Amah, a ranar 30 ga watan Nuwamba, shekarar da ta gabata.

Shugaban Hukumar Alhazai ta Najeriya (NAHCON), Alhaji Zikrullah Kunle Hassan a ranar Laraba ya karbi bakuncin sabon kwamishinan hukumar da ke wakiltar Kudu maso Gabas, Dr Sulaiman Afikpo.

Dokta Afikpo ya zama Kwamishinan NAHCON ne bayan rasuwar wakilin shiyyar siyasa, Alhaji Ibrahim Ogbonnia Amah, a ranar 30 ga watan Nuwamba, shekarar da ta gabata.

Hisbah Ta Wanke Matar Da Ta Auri Saurayin ’Yarta A Kano Daga Zargi

 


Kwamitin da Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kafa kan binciken auren matar da ta auri saurayin ’yarta, ya wanke ta daga zarge-zargen da ake mata.

Wannan na cikin wata sanarwa da kakakin hukumar, Alhaji Lawan Ibrahim ya fitar a Kano a ranar Talata.

Sanarwar ta ce “Gabatar da rahoton binciken da kwamiti ya ya yi karkashin jagorancin Kwamanda Malam Hussain Ahmed, an gano auren halal ta yi kuma ta cika duk wasu sharuda da addini ya tanadar.”

Sanarwar ta kuma ce bincikensu ya nuna cewar matar mijinta ya sake ta tun da fari kuma ta yi iddar wata uku kamar yadda addinin Musulunci ya tsara, kafin daga bisani ta auri saurayin ’yarta da ta daina so.

Mataimakin Kwamandan ya yi watsi da zargin da ake wa matar na cewar ita ta kashe aurenta don ta auri saurayin ’yarta.

“Auren halal suka yi kamar yadda Musulunci ya tsara, shi ya sa Kwamandan Hisbah a Karamar Hukumar Rano ya jagoranci daurin auren.”

Babban Kwamandan Hukumar Hisbah na Jihar, Harun Ibn-Sina, ya jinjina wa kwamitin kan yadda suka gudanar da bincike tare da gudanar da aikinsu kan lamarin

Ibn Sina ya ce hukumar ta yi nazari ntsanaki wajen zabar mambobin kwamitin duba da tarin iliminsu na Addini da kuma gogewa wajen warware matsalolin zamantakewa

Ya gargadi jama’a da su guji yada labaran karya da fadar abin da ba su sani ba game da Musulunci.

Ya kuma bukaci al’umma da suke neman ilimi, domin Addinin Musulunci ya yi tanadin komai game da aure da abin da ya shafi iyali.

Tun da farko, Aminiya ta ruwaito yadda matar ta auri saurayin ‘yarta, wanda hakan ya sa mutane suka dinga tofa albarkacin bakinsu.

Wasu da dama sun yi Allah wadai da halin matar kan aure saurayin da diyarta ta yi soyayya da shi

(AMINIYA)

rai

Kada Ku Nemi Na Saki 'Yan Daba - Muhuyi Magaji Ya Gargadi 'Yan Siyasa

FG Urges KOICA, FAO to Align Agricultural Intervention with Nigeria’s Development Priorities, Ward-Based Strategy

The Federal Government has called for stronger alignment between development partners’ interventions and Nigeria’s national deve...