Gwamnan Kano ya bayar da kyautar Miliyan daya, kujerar Haji da kuma daukar aiki na dundundun ga ma'aikacin wucin gadin hukumar alhazai

Dayyabu Bala Gezawa (Dan Gezawa) shi ne ma'aikacin wucin gadin hukumar alhazai ta Kano da ya tsinci dala dubu 16 kudin guzurin maniyyatan wata kararmar hukuma gaba daya kuma ya damkasu ga Darakta Janar na hukumar 

Gwamnan Kano ya bayar da kyautar Miliyan daya, kujerar Hajj da kuma daukar aiki na dundundun ga ma'aikacin wucin gadin hukumar alhazai da ya mayar da naira miliyan 16 ya guzurin alhazai da ya tsinta

Alhaji Abba Kabir Yusuf ya bayar da wannnan kyauta ne a ranar Litinin, yayin taron mika masa rahoton aikin Hajin 2023 daga hannun Hukumar kula da Jin dadin Alhazai ta Jahar Kano

Gwamnan wanda ya bayyana farin cikinsa bisa tarin nasarorin da sabon shugabancin hukumar ya samar a yayin aikin hajin da ya gabata, duk Kuwa da cewar sun tarar da tarin matsaloli dangane da shirin aikin Hajin

Yace gwamnatinsa na bayar da cikakkiyar kulawa ta dukkanin lamarin da ya shafi Harkokin addinin islama, musammam ma aikin haji da ya kasance daya daga Cikin shikashikan musulinci
Alhaji Abba Kabir Yusuf Wanda yay Amfani da taron wajen yabawa hali na gari da tarbiyya ta ma'aikacin wucin gadi na Hukumar Alhazai ta Kano wanda ya tsinci kudin guzurin maniyyatan Karamar hukuma daya da ya kai naira miliyan 16 kuma ya damkasu ga shugaban Hukumar

A bisa wannan hali na gari da ma'aikacin ya nuna, Gwamnan ya gwangwaje shi da kyautar naira miliyan daya da kujerar Aikin Hajji tare kuma da tabbatar da shi a matsayin cikakken ma'aikaci na hukumar

Ya kuma bawa Hukumar umarnin fara karbar kudin aikin hajin 2024 da ma dukkanin wasu shirye-shiryen da suka shafi aikin da suka hada da kama gidajen alhazai kusa da harami da zabar Kamfanin da zai yi abincin alhazai da ma na harkokin sufuri yayin aikin Hajin


Popular posts from this blog

Yanzu - Yanzu: Bankuna Zasu Karbi Tsofaffin Kudi Ko da Bayan Karewar Wa'adi - Emefiele

Zababben Gwamnan Kano Ya Kafa Kwamitin Karbar Mulki