Kotu Ta Kwace Kujerar Sanatan APC A Kogi, Ta Ba Natasha Ta PDP

Kotun Daukaka Kara ta Ayyana Natasha Akpoti ta jam’iyyar PDP a matsayin halastacciyar wacce ta lashe zaben kujerar Sanatan Kogi ta Tsakiya.

Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) dai a watan na Fabrairu ta ayyana Sanata Abubakar Ohere na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben, amma Natasha ta garzaya kotu.

Daga bisani dai kotun sauraron kararrakin zabe da ke Jihar Kogi ta soke zaben na Ohere, sannan ta tabbatar mata da nasara.

Kotun dai, wacce Mai Shari’a K.A Orjiakor ya jagoranta, ta ce an yi wa Ohere aringizon kuri’u a wasu rumfunan zabe tara da ke Karamar Hukumar Ajaokuta.


Alkalin ya ce an kuma cire sakamakon Natasha a mazabun da karin wasu guda uku, duka dai a cikin Karamar Hukumar.

Hakan ne ya sa kotun ta ayyana ta a matsayin wacce ta lashe zaben da kuri’u sama da 54,074, sabanin kuri’a 51,291 da ta ce Ohere ya samu.


Sai dai Sanatan bai gamsu da hukuncin ba, inda daga bisani ya garzaya kotun daukaka karar, amma ta tabbatar da hukuncin kotun bayan.

(AMINIYA)

Popular posts from this blog

Yanzu - Yanzu: Bankuna Zasu Karbi Tsofaffin Kudi Ko da Bayan Karewar Wa'adi - Emefiele

Zababben Gwamnan Kano Ya Kafa Kwamitin Karbar Mulki