Karin ayyukan alheri na nan tafe ga al'ummar Kano -- Gwamna Abba K. Yusuf
Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya jaddada aniyar gwamnatinsa na ci gaba da gudanar da ayyuka da shirye-shiryen da za su inganta rayuwar al’ummar jihar.
Da yake jawabi a lokacin da yake duba ayyukan ofishin sa a cikin makonni 3 da suka gabata a yayin da aka fara taron majalisar zartarwa ta jiha karo na 7 a gidan gwamnati da ke Kano, gwamnan ya ce an fara gudanar da ayyukan alheri da dama.
A sanarwar da babban sakataren yada labaran Gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya sanyawa hannu, Gwamnan ya bayyana cewa, a cikin wannan lokaci da gwamnatin ta yi nasarar kaddamar da rabon kayan abinci da suka hada da Shinkafa da Masara a sassan jihar 484.
Ya kuma bayyana cewa gwamnati ta kuma kaddamar da rabon kayayyakin koyo da koyarwa, Uniform da jakunkuna/Takalmi, baya ga kaddamar da shirin jigilar dalibai karo na 1 da gwamnati ta dauki nauyin bayar da tallafin karatu a kasashen waje a MAKIA.
"Bach na biyu na jigilar daliban da za su je Indiya za a ci gaba da jigilar su ranar Juma'a yayin da wadanda za su je Uganda za a kai su ranar Lahadi," in ji gwamnan.
Hakazalika a cewarsa, gwamnati ta yi nasarar kaddamar da auren ma’aurata 1800 mai suna (Auren Gata) tare da bayar da tallafin kayayyakin daki, kayan abinci, tallafin kudi da sauran kayayyaki ga kowanne daga cikin ma’auratan da nufin tallafa musu.
Alhaji Kabir Yusuf wanda ya bayyana jin dadinsa ga al’ummar jihar bisa goyon baya da addu’o’i, ya kuma yabawa ‘yan jarida bisa goyon bayan da suke baiwa gwamnatinsa, tare da fatan ganin an dore.