Kwastam ta kama tirelar shinkafa ‘yar-waje takwas da aka shigar Nijeriya
Hukumar fasa-ƙwauri ta Nijeriya, Kwastam ta ce ta kama tirela takwas maƙare da shinkafa ƴar-waje a kan iyakokin ƙasar da ke yankin Kudu maso Yamma.
A wani taron manema labarai da Shugaban Kwastam na riƙo Bashir Adewale Adeniyi ya yi a Legas wanda ya ce mai matuƙar muhimmanci ne ga tattalin arzikin ƙasar, ya ce jami’an hukumar sun kama shinkafar buhu 7,029 ne a lokuta da wurare daban-daban a shiyyar Kudu maso Yammacin.
Mr Adeniyi ya ce an samu wannan nasara ce bayan ƙaddamar da wasu jerin ayyuka da hukumar ta yi don ceto fannin noma na ƙasar da ya zama babban makamin da gwamnatin tarayya ke riƙe da shi don inganta samar da abinci.
“Kamar yadda aka sani fannin noma, wanda shi ne ƙashin bayan tattali arzikin Nijeriya, ya zama muhimmin abun da gwamnatin tarayya ta mayar da hankali a kai don samar da isasshen abinci ga ƴan ƙasar da kuma inganta tattalin arziki.
“Ana gudanar da wannan samame da jami’anmu ke yi ne don abu biyu ne; karya gwiwar ƴan kasuwar da ke son su dinga hada-hadar fasa-ƙwauri da kuma son jawo wa masu fasa-ƙwauri asara,” Shugaban na Kwastam ya ce.
Sauran kayayyaki
Baya ga shinkafar da aka ƙwace, hukumar Kwastam ta kuma ce an yi nasarori da dama a Satumba na ƙwace wasu kayayyakin da suka haɗa da:
Baya ga shinkafa an kuma kwace wasu kayayyaki da dama da aka shigar da su Nijeriyar ba bisa ka'ida ba. Hoto: NCS
Lita 35,000 ta man fetur
Lita 1,100 na dizel
Kwantena ɗaya mai girman ƙafa 40 maƙare da dilar gwanjo 360
Kwantena ɗaya mai girman ƙafa 40 maƙare da jakankunan hannu na mata da gajerun wanduna
Kwantena ɗaya mai girman ƙafa 20 maƙare da katakon da ba a sarrafa ba
Katan 106 na daskararrun kaji ƴan ƙasar waje
Firiji 55 da aka yi amfani da su
Na’urar kwamfureso 110
Katan 148 na sabulu ƴan waje
Katan 121 na man gashi da ya lalace
Motoci Tokunbo 25.
Mr Adeniyi ya ce an fara gudanar da bincike kan waɗannan kayayyaki da aka ƙwace. “An kama mutum 14 da ake zarginsu da hannu a laifuka da dama da suka haɗa da take dokokin fasa-ƙwaurin kaya," in ji shi.
Ya ce jumullar kuɗaɗan haraji da aka biya a kan kayan da aka ƙwace din sun kai naira biliyan ɗaya da miliyan dari bakwai da hamsin da biyar da dubu tamanin da dari takwas da casa’in da takwas, (1,755,080,898).
“Sannan sashen na kwastam ya samu kudi har naira miliyan 72,807,025.11 na haraji a hanyar bincike. Kuma muna kira ga masu shigo da kaya da ke da lasisi da su dinga bin dokokin shiga da fitar da kaya don saukaka mu’amala a kan iyakokinmu,” ya faɗa.
(TRT HAUSA)