Search This Blog

Tuesday, 3 October 2023

Gwamnatin Kano Ta Bayar Da Hutun Bikin Takutaha

Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya ayyana yau Laraba 4 ga Oktoba, 2023 a matsayin ranar hutu domin tunawa da haihuwar fiyayyen halitta Annabi Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi.

A Cikin sanarwar da Kwamishinan yada labarai na Kano, Injiniya Abba Malam Baba Halilu Dantiye ya sanyawa hannu, Gwamnan ya bukaci al’ummar jihar da su yi amfani da lokutan bukukuwa domin yin tunani a kan koyarwar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama da sanya su cikin harkokinsu na yau da kullum.

Ya kuma bukaci jama’a da su rika yin addu’a domin samun zaman lafiya da ci gaba a Kano a Najeriya baki daya.

Ya yi addu’ar Allah ya ganar damu wannan lokaci mai wuya, ya kuma sa mu dace a wannan damina da kuma damina mai zuwa.


Kada Ku Nemi Na Saki 'Yan Daba - Muhuyi Magaji Ya Gargadi 'Yan Siyasa

Head of Service Urges Civil Servants to Uphold Ethical Conduct

The Head of Service, Kano State, has called on civil servants to strictly adhere to the Civil Service ethical code and show grea...