Ilimi shi ne ginshikin ci gaba a kowace Al'umma - Laminu Rabi'u Danbaffa

Darakta Janar na Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kano, Laminu Rabi’u Danbappa, shi ne ya bayyana haka a yau a lokacin wani taro da Malaman Bita na kananan hukumomi wanda aka gudanar a harabar Hukumar.
     

A sanarwar da Jami'in hulda da jama'a na hukumar, Sulaiman Abdullahi Dederi ya sanyawa hannu, yace Laminu Rabi’u Danbappa ya ce hukumar ta shirya wannan taro ne domin gabatar da sabon jagoranci na Malaman koyar da aikin Hajji daga matakin jiha.

Alh Laminu Rabi'u, ya kara da cewa, hukumar jin dadin alhazai, za ta ci gaba da bada fifiko kan fadakar da alhazai yadda ake gudanar da aikin Hajji.

A nasa bangaren Daraktan yada labarai da fadakar da Alhazai Alh Sa’idu Muktar Dambatta, ya yi kira ga Malaman da su ba da hadin kai domin cimma burin da aka sanya a gaba.

A nasa jawabin, Sabon Shugaban kwamitin Malaman Bitar na Kano, Wanda kuma ya kasance dan Hukumar gudanawa ta hukumar  Alhazan ta Kano, Shelkh Tijjani Shehu Mai-Hula, ya umarci Malaman Bitar  da su tabbatar da adalci wajen gudanar da ayyukansu.
Shelkh Tijjani Mai -Hula, ya godewa hukumar bisa shirya wannan taro mai matukar muhimmanci.


Popular posts from this blog

Yanzu - Yanzu: Bankuna Zasu Karbi Tsofaffin Kudi Ko da Bayan Karewar Wa'adi - Emefiele

Zababben Gwamnan Kano Ya Kafa Kwamitin Karbar Mulki