Yanzu-yanzu: Gwamnan Kano ya yi sabbin nade-naden mukaman shugabannin ma'aikatun gwamnati

A bisa kokarin sanya hannun da suka dace don inganta shugabanci na gari, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya amince da nadin shugabannin hukumomin na jihar nan take.

A sanarwar da babban sakataren yada labaran Gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya sanyawa hannu, yace Wadanda aka nada sune kamar haka.

1. Salisu A. Kabo, Darakta Janar na hukumar Kula da ci gaban matasa

2. Dr. Hamisu Sadi Ali, Darakta Janar na ofishin kula da basussuka

3. Abduljabbar Mohammed Umar, Darakta Janar na KAN-INVEST

4. Yusuf Kabir Gaya, Shugaban Hukumar SUBEB

5. Mustapha Adamu Indabawa, Manajan Daraktan Gidan Talabijin na Abubakar Rimi (ARTV)

6. Hamisu Dogon Nama, Manajan Daraktan Kasuwar Kantin Kwari

7. Abdulkadir B. Hussain, Manajan Daraktan Kasuwar Sabon Gari

8. Dr Kabiru Sani Magashi, Mukaddashin Manajin Darakta na KASCO

9. Aminu Aminu Mai-Famfo, Mataimakin Manajin Darakta na KASCO

10. Engr, Abubakar Sadiq J. Mataimakin Manajin Darakta Hukumar sufuri ta  Kano Line

Gwamnan ya umarci wadanda aka nada da su yi amfani da kwarewarsu wajen gudanar da ayyukansu ta yadda za su yi wa al’ummar jihar hidima da kuma tabbatar da amincewar da aka yi musu.


Popular posts from this blog

Yanzu - Yanzu: Bankuna Zasu Karbi Tsofaffin Kudi Ko da Bayan Karewar Wa'adi - Emefiele

Zababben Gwamnan Kano Ya Kafa Kwamitin Karbar Mulki