Kasidar European Champions League - Professor Salisu Shehu

Da sunan Allah Shi Daya
Zan fara bayani bai daya. 

Rabbu Kai Tilo ne Kai Daya
Ba kama a gareKa gaba daya.

Duk halittun kas da samaniya
Kai ne Ka yiwosu gaba daya.

Rabbana saita mini zuciya
Nai bayani ba wata zamiya

Nai salati na yo tahiya
GA Abin kaunarmu gaba daya. 

Al--Bashiru Aminin duniya 
Ka ji Mai cetonmu gaba daya. 

Ni nufina zan yi matashiya
Ga shababu su bar sharholiya. 

Watakila a yo mini tambaya, 
Kan batun me zaka matashiya? 

Kan batun kwallon Birtaniya, 
Wofin banza na Pirimiya. 

KO batun kwallo na Spaniya, 
La Liga abin hauragiya. 

Ga Juventus can ta Italiya,
Wadansu kanta suke ta hayaniya. 

Masu sonta su ce mata gimbiya 
Ba karatu sai dai tankiya

Wasu har Azumi fa suke niyya, 
Don sadaukarwa ga Spaniya, 

KO su yo yankar qurbaniyya, 
Zallar kaunar Barceloniya. 

David Beckham tuni ya riya, 
Baya son Ummah Islamiyya, 

Haka ma Chelsean Birtaniya, 
Basu son jinsin Ifrikiyya. 

GA su Manchester Britaniya, 
Team ne biyu 'yan gabar tsiya. 

Masu sonsu a nan Naijeriya, 
Basu son juna gabar tsiya. 

In suna musun Manchestiya
Ka ga mamakin hauragiya

Huruwar hanci da ta jijiya, 
Ga bankaura da hayaniya. 

Sun mance nasihar gaskiya, 
Sunnar Manzo Bahanifyya. 

Duk Musulmi kab baki daya, 
Yan uwan juna ne bai daya. 

Ya shababu ku zo duka bai daya
GA nasiha kukan kurciya

Kui riko da tafarkin gaskiya 
Garkuwa kenan ga hayaniya. 

Duk samarin wannan nahiya, 
Mui ta himma ba hauragiya. 

Na tino gargadi na mazan jiya, 
Zungur su Sa'adu abin biya, 

"Mu dai ilimi muka tambaya, 
Ko a London ko a Arebiya". 

Ya shababu ku lura da Duniya 
Mai bugarwa ce tamfar GIYA.

Lokacin da mutum ya ji lafiya, 
Baya komai sai barnar tsiya. 

Balle kuma in ya ga dukiya, 
Ta taru irin zinariya, 

Sai ka ganshi yana ta fahariya
Ga hululu da yin sharholiya. 

Sai ya rinka zuwa Birtaniya, 
Old Trafford can a Stadiya, 

Wani ko ya nufanci Italiya 
Inter Milan yan hauragiya, 

KO ya zoshi ya kirkiri kungiya,
Shi yake yanke mata cibiya, 

Yai ta kan renonta da DUKIYA, 
Har ta kai wata yar hamshakiya, 

Maimakon ya yi Zakkar dukiya, 
Ko ya yo sadaka mai jariyah, 

Amma sai dai ya yi tutiya, 
Wai yana da zaratan kungiya. 

Ya Allah Kai mana kariya 
Daga bin shahawowin zuciya

Kar mu fada rudun duniya, 
Mui ta bankaura da hayaniya 

Tabbatar mana tsarkin zuciya 
Mui ta addini bisa gaskiya 

Nai salati na yo tahiya, 
Ga Aminu Rasulun Gaskiya. 

Nai yabo kuma na yi ta godiya, 
GA Alimu Ilahun Gaskiya.

Tammat bihamdillahi.

Popular posts from this blog

Yanzu - Yanzu: Bankuna Zasu Karbi Tsofaffin Kudi Ko da Bayan Karewar Wa'adi - Emefiele

Zababben Gwamnan Kano Ya Kafa Kwamitin Karbar Mulki