Darakta Janar Na Hukumar Alhazai Ta Kano Yayi Ta'aziyya Ga Jami'in Alhazai Na Karamar Hukumar Bichi

Daga Faruk Musa Sani Galadanchi

Darakta Janar na Hukumar kula da jin dadin Alhazai ta Jahar Kano, Alhaji Laminu Rabi'u Danbaffa, ya bayyana rasuwar Maddassir Habib Idris a matsayin babban rashi.

Alhaji Laminu Rabi'u Danbaffa ya bayyana hakan ne lokacin da ya jagoranci tawaga domin yin ta'aziyya ga mahaifin mamacin wanda kuma ya kasance jami''in Alhazai na Karamar Hukumar Bichi, Malam Habib Idris Bichi
Laminu ya bayyana marigayi Mudassir a matsayin matashin Jami''in Hukumar tsaro ta farin kaya mai da'a wanda yake jajircewa da aiki tukuru wajen gudanar da aikinsa wanda ya rasa rayuwarsa sakamakon harin da yan bindiga suka kai musu suna tsakiyar gudanar da aikinsu a Jahar Kaduna

Darakta janar din yace rasuwar Maddassir ta bar Babban gibi ga iyalan Malam Habib Idris Bichi da ma daukacin al'umar jahar Kano baki daya
Don haka Alhaji Laminu Rabi'u a madadin Shugaban Hukumar da ma'aikata yayi addu'ar Allah ya gafarta masa ya kuma bawa iyalansa hakurin jure rashin da suka yi.
A nasa jawabin, mahaifin marigayin, wanda kuma ya kasance Jami'in Alhazai na Karamar Hukumar Bichi, Malam Habib Idris Bichi, ya godewa Darakta janar din da yan tawagarsa bisa ziyarar ta'aziyya

Popular posts from this blog

Yanzu - Yanzu: Bankuna Zasu Karbi Tsofaffin Kudi Ko da Bayan Karewar Wa'adi - Emefiele

Zababben Gwamnan Kano Ya Kafa Kwamitin Karbar Mulki