Hukumar Alhazai Ta Kano Ta Jaddada Aniyarta Na Hada Gwiwa Da Majalisar Dokoki Ta Kano

Laminu Rabi’u Danbappa, ya bayyana hakan ne yau a lokacin da ya karbi bakuncin kwamitin majalisar kan harkokin aikin hajji a ofishinsa wanda ya kai ziyarar ban girma ga hukumar.
 
A sanarwar da Jami'in hulda da jama'a na hukumar, Sulaiman Abdullahi Dederi ya sanyawa hannu,Laminu ya kara da cewa Hukumar Jin Dadin Alhazai, tana iya yiwuwa ne kawai idan aka hada hannu da juna domin kare abin da aka damka wa alhazai.

A nasa bangaren, shugaban kwamitin alhazai na majalisar, kuma dan majalisar wakilai mai wakiltar karamar hukumar, Honarabul Sarki Aliyu Daneji, ya ce sun kasance a hukumar alhazai domin nuna fuskokinsu a matsayinsu na mambobin kwamitin daga majalisar dokokin jiha.
Sarki Aliyu Daneji, yayi kira ga ma’aikatan gudanarwa da su bada hadin kai domin cimma burin da aka sanya a gaba.

A nasa jawabin dan majalisar wakilai mai wakiltar karamar hukumar Dala a majalisar dokokin jiha Hon Lawan Hussaini Cediyar yan’gurasa ya shawarci hukumar alhazai ta jiha da ta tabbatar da cewa an baiwa alhazan da zasu yi aikin hajjin bana isasshen lokaci domin su yi shiri sosai.


Lawan Hussaini, ya yi alkawarin taimakawa hukumar ta gyara dokar tasu a majalisar dokokin jihar.

Da yake jawabi tun da farko, Shugaban Hukumar Alh, Yusif Lawan, ya yi alkawarin yin duk mai yiwuwa don ganin ba a yi wa maniyyata wahala ba a ayyukan Hajjin bana.
Alh, Yusif Lawan, ya godewa kwamitin aikin Hajji na majalisar jiha bisa wannan ziyarar.


            

Popular posts from this blog

Yanzu - Yanzu: Bankuna Zasu Karbi Tsofaffin Kudi Ko da Bayan Karewar Wa'adi - Emefiele

Zababben Gwamnan Kano Ya Kafa Kwamitin Karbar Mulki