Gwamnatin Kano Za Ta Samar Da Rumbun Tara Bayanai Na Matasa - Ogan Boye

Shirye-shiryen gwamnatin Jihar Kano tare da kulawar Ofishin Mai ba wa Gwamna Shawara akan harkokin Matasa da Wasanni sun kammala wajen kirkiro da rumbun tara bayanai na Matasan Jihar Kano.

Mai ba wa Gwamna Shawara akan harkokin Matasa da Wasanni Ambasada Yusuf Imam Ogan Boye ne ya shaida hakan lokacin da yake yi wa manema labaru jawabi dangane da manufa da amfanin yin rumbun tara bayanan matasan a Ofishinsa.

A sanarwar da jami’in hulda da jama’a na ofishin mai bawa gwaman shawara, Yusuf Ibrahim ya sanyawa hannu, Ogan Boye ya bayyana muhimmancin tara bayanan wajen taimakawa gwamnati don inganta tsare-tsaren bunkasa harkokin matasa a Jihar Kano, ya yi dogon bayani kan muhimmancin matasa a fanin kasuwanci da tattalin arzikin kasa.

Yace " Ina da yakinin cewa wannan batun rumbun tara bayanan matasa zai karfafi tsare-tsaren gwamnati na samar da guraben aiyuka da sana'o'i tare da rage yiwuwar fadawar matasa miyagun aiyuka" in ji Ogan Boye.

Ambasada Yusuf Imam ya ce Shirin yana cike da haskaka makoma da kyakkyawan zaton cigaban Jihar Kano tare da matasanta wanda shi ne manufar Gwamnatin Mai Girma Alhaji Abba Kabir Yusuf.

Ya kara da cewa Matasa karkashin wannan tsarin za su yi rijista a yanar gizo ko kuma a fadojin Hakimai, Dagatai da masu Unguwanni nan da wani lokaci kadan.

Popular posts from this blog

Yanzu - Yanzu: Bankuna Zasu Karbi Tsofaffin Kudi Ko da Bayan Karewar Wa'adi - Emefiele

Zababben Gwamnan Kano Ya Kafa Kwamitin Karbar Mulki