Kungiyar Kannywood Ta Bawa Kwamishinan Kudi Na NAHCON Lambar Yabo

Da yake jawabi, jagoran tawagar Alhaji Ahmed Kaka ya taya hukumar murnar kammala aikin Hajjin 2023 cikin nasara duk da kalubalen da ake fuskanta.

A sanarwar da Shafi'i Sani Muhammad na sashen yada labarai da Dab'i na Hukumar NAHCON ya sanyawa hannu, Shugaban kungiyar ya yi kira da a hada kai a tsakanin bangarorin guda biyu musamman ta fannin wayar da kan alhazai da tsawaita amfani da kafafen sada zumunta na zamani.

Kungiyar ta baiwa Alhaji Nura Hassan Yakasai, Kwamishinan kudi lambar yabo ta taimakon jin kai bisa gudunmawar da ya bayar wajen bayar da muhimmin taimako ga marasa galihu a cikin al’umma.

Alhaji Yakasai wanda ya bayyana jin dadinsa ga dandalin ya tabbatar musu da shirye-shiryen Hukumar na yin bincike da hada kai da kungiyar nan gaba.


Tunda farko da yake nasa jawabin, Shugaban Hukumar NAHCON, Alhaji Zikrullah Kunle Hassan ya yi kira ga ‘yan wasan kwaikwayon Najeriya da su ci gaba da amfani da kafar sadarwar su wajen wayar da kan ‘yan Nijeriya musamman Alhazai ta hanyar fasaharsu.
Ya bayyana haka ne a yau a lokacin da kungiyar Kannywood Action Forum karkashin jagorancin Alhaji Ahmed Kaka ta kai ziyarar ban girma ga hukumar NAHCON a  Abuja.

Shugaban ya bayyana imaninsa cewa tare da dimbin masu sauraronsu musamman a Arewacin Najeriya, ayyukansu ko labaransu za su taimaka matuka wajen nuna kyakykyawan kimar kasar da kuma taimakawa wajen kawo canji ga al’umma.


Popular posts from this blog

Yanzu - Yanzu: Bankuna Zasu Karbi Tsofaffin Kudi Ko da Bayan Karewar Wa'adi - Emefiele

Zababben Gwamnan Kano Ya Kafa Kwamitin Karbar Mulki