Darussa Daga Siyasar Kano Ta 2023 - Dr Sa'idu Ahmad Dukawa

Tun lokacin da Injiniya Abba Kabir Yusuf ya zama gwamnan Kano daga zaben da aka gudanar a watan Maris na wannan shekarar (ta 2023) har izuwa ranar Laraba, 20/9/23, siyasar Kano (wacce ake yiwa taken “sai Kano!”) ta dada zafafa fiye da ko da yaushe a wannan zubin dimokaradiyyar (ta Jamhuriya ta hudu). A bisa fahimtata, dalilai kamar shida ne suka janyo haka. 

Za mu yi bitarsu a takaice domin amfanin gaba.

1. Zafin hamaiyar siyasa tsakanin Senator Rabiu Musa Kwankwaso da Dr. Abdullahi Umar Ganduje. Wannan ta sa wadannan jagororin na Kano guda biyu sun fifita bukatun kansu, na neman wani ya ga bayan wani a siyasance, fiye da bukatar da Kano take da ita na su hada kansu domin su samarwa da Kano zaman lafiya da cigaba mai dorewa. 

A dalilin haka magoya bayansu sun dukufa wajen ganin jagoransu ne a sama ta kowane hali. Don haka cece-kuce ya kazanta a tsakanin juna. Da Allah zai sa idan aka kai karshen tirka-tirkar wadannan manyan biyu su yafewa juna su yi sulhu a tsakaninsu da zai fi kyau ga Kano da ma Kasa baki daya.

2. Karancin tazara tsakanin APC da NNPP ya sa kowa yana ganin ba zai ja da baya ga dayan ba. Wannan ce ta sa APC ba ta dangana ba game da zaben 2023 ta garzaya kotu. Sabanin abinda ya faru a zaben 2003, lokacin da Malam Ibrahim Shekarau ya karba daga hannun Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso, wanda tazara tsakanin ANPP da PDP ta sa PDP ta saduda ba tare da ta je kotu ba. Haka ma a 2011, lokacin da Kwankwaso ya dawo ya karba daga hannun Shekarau. Ko da yake ANPP ta garzaya Kotu, amman shari’ar ba ta dauki hankali kamar a wannan karon ba, saboda sauran abubuwan da suka faru a wannan karon ba su faru a wancan lokacin ba. 

To amman fa karancin tazara a tsakanin jam’iyyu biyu bai kamata ya zama matsala ba. Hasali ma kamata ya yi ace ya zamo riba saboda jam’iyya mai mulki ta rika yin taka-tsantsan, sannan hamayyar siyasa ta sa a inganta shugabanci. Kuma idan an samu sauyi a zabe a dada samun ingancin shugabanci. Amman fa duk sai hamayyar da ake yi akan manufa ake yinta ta neman cigaban kasa da al’umma baki daya.

3. Yadda gwamnatin NNPP ta dauki wasu matakai a cikin garaje ya haifar da ta’azzara a hamayyar da ake yi a siyasar Kano. Alal misali, yadda aka kaddamar da bincike akan tsohon gwamna Ganduje nan take zai bashi hoton kamar ana son a ga bayansa ne a siyasance, don haka dole zai dauki matakai ba kawai na kare kansa ba amman har na ganin ya ga bayan abokan hamayyarsa a siyasance. Ya kamata ace an gane cewar idan Kwankwaso yana da gwamnatin Kano, Ganduje kuma yana tare da gwamnatin Tarayya. Da ace hada kansu suka yi wajen nemarwa Kano abinda zai amfaneta da ya fi su tsaya gwada kwanji. Akwai fatan bayan wannan dambarwas a samu daidaito a tsakanin shumagabannin biyu. Wani misalin shine yadda aka yi garaje wajen yin rusau daga hawan gwamnatin.
 Anan ba rusau dinne a karan kasa matsala ba. Amman rashin tsayawa a tantance, a kare wadanda ba su da hakki daga fadawa cikin hasarar da ba suji ba, ba su gani ba. Akwai fatan duk wani aiki da za a yi anan gaba a yi la’akari da kaucewa daukar hakki. Zai rage cece-kuce da fadawa cikin matsalar da za a iya kauce mata.

4. Karyewar kawancen siyasa tsakanin Shugaban Kasa, Bola Ahmad Tinubu, da Senator Rabiu Musa Kwankwaso ba za ta rasa nasaba da dagulewar harkokin siyasa a Kano ba. Da ace an yi wannan kawancen da hamayya za ta ragu tsakanin jagororin biyu, ko da ba ta kare gaba daya ba. Amman wannan karayar ta haifar da Karin masu hamayya da Senator Kwankwaso. 

Don haka siyasar ta Kano ta dada zafafa. Anan ‘yan Majalisar Tarayya na jam’iyyar NNPP suna da rawar da za su taka wajen samar da sasanci tsakanin Madugunsu da Shugaban Kasa. Yana da kyau su yi kokarin yin hakan. Su sun san hanyoyin da ake bi wajen yin hakan. Bukatar da Kano take da ita na neman zaman lafiya da karuwar arziki ita ya kamata a fifita.

5. Yakin ‘yan Media (Sojojin Baka) na bangarorin biyu ya ta’azzara hamayya a siyasar Kano. Yadda kowane bangare ya rika shiga kafafen yada labarai yana yanke hukunci akan shari’ar da ake yi ta zabe bai dace ba ko kadan. Yana da kyau a samu wasu su nemi Kotu ta haramta irin wannan dabi’ar a Shari’un da za a yi a nan gaba.

6. Kalaman tinziri da wasu jami’an gwamnati suka yi a gabanin yanke hukuncin shari’ar zaben na gwamnan Kano matsalace babba. Barazana ce ga tsarin shari’a da ma shugabanci baki daya. Wadanda suka yi wannan kalaman ba su yi la’akari da cewar gwamnatin jiha suke wakilta ba, kuma gwamnatin Taryya suke nunawa yatsa! Da sun yi la’akari da abinda yake samun ‘yan kungiyar IPOB, na yankin Igbo, da watakil ba su yi barazanar ba. Anan dole ne a yabawa gwamna Abba Kabir Yusuf game da matakin ladabtarwa da ya dauka nan take. Akwai bukatar duk mai kaunarsa ya kiyayi irin wannan kalaman daga nan har a gama appeal, da ma bayan an gama.

A karshe akwai bukatar ‘Yansiyasa su karanta dokar zabe ta Kasa, da ma sauran dokokin da suke da alaka da zabe, su yi kokari su fahimce su, su bisu sau da kafa. Wannan zai rage matsalolin zabe wadanda suke haifar da sai an kai ga shari’ar zabe. Haka kuma zai sa a fi fahimtar hukuncin da Kotunan zabe suke yankewa.

Muna fatan Allah Ta’ala ya tabbatar da zaman lafiya da karuwar arziki a Kano da Kasa baki daya.

Popular posts from this blog

Yanzu - Yanzu: Bankuna Zasu Karbi Tsofaffin Kudi Ko da Bayan Karewar Wa'adi - Emefiele

Zababben Gwamnan Kano Ya Kafa Kwamitin Karbar Mulki