Gyara a dokar aikin Hajji zai rage tsadar tafiya Makkah a Najeriya - Sanata Dan Baba
Dan Majalisar Dattijai mai wakiltar Sokoto ta Kudu a Majalisar Dokokin Najeriya Sanata Ibrahim Abdullahi Dan Baba ya sha alwashin yin duk abin da zai iya wajen ganin an yi wa dokar aikin Hajji kwaskwarima a sabuwar majalisa ta goma da za ta fara aiki. Sanatan wanda ya kasance a tsohuwar majalisa ta tara wacce za ta gama aikinta cikin watan Mayun shekaran nan ta 2023 ya ce tun da farko ya gabatar da kudurin gyaran a gaban majalisar mai karewa. Sanata Dan Baba ya kara da cewa lokaci ya yi da ya kamata a samar wa mahajjata sauki wajen biyan makudan kudade domin aikin Hajji. A cewar dan majalisar, yin gyara ga dokar Hukumar Aikin Hajji ta kasar shi ne zai magance yadda ake samun karuwar kudin tafiya Hajjin. Ya ce ya bukaci majalisa ta gudanar da bincike kan badakalar da ke cikin aikin Hajji a Najeriya kuma majalisar ta kafa wani kwamitin bincike. "Biciken ya gano ana sama da fadi da kudaden mahajjata, otel da ya kamata a kama na kwana arba'in sai a kama na tsawon kwan