Search This Blog

Thursday, 5 January 2023

Hajin bana: Hukumar kula da jin dadin alhazai ta jahar Kano za ta fara gudanar da bita ga maniyyata aikin haji nan da mako biyu

 

 

Tun bayan da aka kammala aikin Hajin 2022, Hukumomin Hukumar alhazai ta Najeriya (NAHCON) da sauran hukumomin jin dadin alhazai na Najeriya, suka fara tunkarar aikin hajin shekara ta 2023 domin gujewa sake afkuwar matsalolin da aka samu a aikin hajin da ya gabata 


Ana tsakiyar wadannann shirye-shirye ne katsam sai hukumar kula da aikin Haji da Umrah ta kasar Saudi Arabia ta bayyana sake dawowa da Najeriya yawan adadin kujeru dubu casa’in da biyar da (95,000) da ta saba bata tun kafin bullar cutar Covid-19 

Da yake yi wa manema labarai jawabi a ofihinsa, Sakataren zartawa na hukumar kula da jin dadin ta jahar Kano, Alhaji Muhammad Abba Dambatta, ya ce ya zuwa yanzu hukumar ta mayarwa da kaso fiye da casa’in da tara na maniyyatan da basu samu zuwa aikin hajin da ya gabata ba kudadensu 


Alhaji Muhammad Abba ya bayyanawa maneman labaran cewa tuni hukumar ta kammala dukkanin shiri domin fara gudanar da bitar alhazai a tsakiyar watan Janairun da ake cikin 

Dambatta yayi kira ga maniyyatan da suka bar kudadensu ga hukumar, dasu gaggauta zuwa domin sake sabunta ragistarsu ta koma ta wannan shekara da muke don gujewa samun matsala da ka iya faruwa 


Sakataren zartarwa ya kara da cewa a yanzu haka hukumar aikin Hajin Saudi Arabia ta gayyaci jami'an hukumar NAHCON da dukkanin shugabannin hukumomin alhazai na jahohi domin sake tattaunawa kan shirin aikin hajin bana 


Ya kuma bayyana cewa ana sa ran maniyyata aikin hajin bana na Najeriya zasu fara tashi zuwa kasa mai tsarki daga ranar 4 ga watan Mayu na wannan shekarar da muke ciki, inda ya sanar da cewa tuni kasar Saudia ta sake samar da karin filin saukar jirage sababbi guda biyu a birnin Madina 


Daga nan sai ya yi kira ga dukkanin masu son zuwa aikin hajin na bana dasu gaggauta biyan kudinsu tun kafin lokacin ya kure musu domin a cewarsa har yanzu hukumar na ci gaba da karbar kudin kujerar na aikin hajin bana 

Wednesday, 4 January 2023

Mutanen Kano sun tabbatar min da yakinin zan lashe zabe - Tinubu



Dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana cewar yana da yakinin jam’iyyar za ta kai ga nasara duba da irin fitowar dangon-kwari da magoya suka yi mata a Jihar Kano.

Jaridar Aminiya ta rawaito cewa A ranar Talata ce dai Tinubu ya ziyarci Kano don kaddamar da yakin neman zabensa a Arewa Maso Yamma, gabanin shiga zaben Shugaban Kasa a wata mai kamawa.

Da yake jawabi ranar Laraba a filin wasa na Sani Abacha, Tinubu ya ce, “Manuniya ta nuna cewa a yakin neman zaben nan, jama’ar Kano sun san abin da ya kamata su zaba.

“Ina da yakinin goyon bayan da Gawuna da Garo ke samu zai kai jam’iyyar nan ga nasarar lashe zaben gwamna har zuwa na Shugaban Kasa,” in ji Tinubu.

Tinubu ya bayyana farin cikinsa kan yadda mutane suka yi dafifi don nuna goyon bayansu ga takararsa.

A nasa bangaren, Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya bukaci magoya baya da su kada wa jam’iyyar APC kuri’arsu a babban zaben da ke tafe.

Ganduje ya bai wa Tinubu tabbacin cewar kuri’ar jama’ar Kano ta APC ce duba da yadda mutane ke mararin sake ganin jam’iyyar ta mulke su.

Haka kuma, Shugaban Jam’iyyar APC na Kasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya bukaci jama’ar yankin Arewa maso Yamma da su sake zabar APC don dorawa daga inda Shugaba Muhammadu Buhari zai tsaya.

Adamu, ya ce irin jama’ar da suka tarbi Tinubu a Kano, wata ‘yar manuniya ce da ke nuna alamar jam’iyyar za ta kai ga nasara.

Shugaban APC na kasa, ya mika tutar jam’iyyar ga dan takarar Gwamnan Jihar, Nasiru Yusuf Gawuna, wanda shi ne Mataimakin Gwamnan Jihar a yanzu.

Daga cikin wadanda suka halarci taron yakin neman zaben a Kano; akwai Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Ahmed Lawan, Shugaban Kwamitin Yakin Neman Zaben Tinubu da Shettina, Gwamna Simon Lalong na Jihar Filato tare da gwamnonin Jihohin Arewa Maso Yamma da suka hada da Jigawa, Katsina, Zamfara, Kebbi da kuma Kaduna

INEC ta ce zata gurfanar da iyayen yaran da aka kama suna kada kuri'a

Shugaban hukumar zaben Najeriya mai zaman kanta INEC, farfesa Mahmoud Yakubu.

Hukumar zaben Najeriya ta ce matukar aka samu kananan yara da ke kokarin kada kuri’a a lokacin zabuka masu zuwa, to lalle kuwa za a kama tare da gurfanar da iyayensu a gaban shari’a.

Wannan dai na kunshi ne a wani sakon gargadi da hukumar zaben ta fitar, a ci gaba da daukar matakai domin hana magudi a zabukan da za a yi cikin wanna shekara.

Domin sauraron cikakken rahoto kan wannan batu tare da Muhammad Kabiru Yusuf, shiga alamar sauti

Wayar salula ce ta haddasa mutuwar sojojin Rasha 89



Rundunar sojin Rasha ta ce, akwai yiwuwar sojojinta sun yi amfani ne da wayoyin salula wadanda suka bai wa takwarorinsu na Ukraine damar gano matsuguninsu har suka kai musu farmakin da ya kashe 89 daga cikinsu.

Sai dai tuni Rashawa suka fara mayar wa da rundunar sojin martani da suka ce, ta fadi haka ne domin wanke kanta daga zargin sakaci.

Hatta masharhanta da ke goyon bayan shugaba Vladimir Putin sun ce, watakila ma adadin sojojin da suka mutun ya zarta 89.

Asarar sojoji 89, ita ce mafi girma da Rasha ta ce ta yi tun bayan barkewar yaki tsakaninta da Ukraine a cikin watan Fabairun bara.

Sojojin na Rasha sun mutu ne sakamakon wani harin makami mai linzami da Ukraine ta kaddamar musu a Makiivka da ke yankin gabashin Ukraine, inda Rasha ta mamaye.

(RFI)

Gwamnatin tarayya za ta dena biyan tallafin man Fetur

 


Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ce daga ฦ™arshen watan Yunin wannan shekara za ta daina biyan tallafin man fetur a ฦ™asar.

Ministar kuษ—i, kasafi da tsare-tsare ta ฦ™asar Zainab Ahmed ce ta bayyana haka a lokacin gabatar da kasasfin kuษ—in shekarar 2023.

BBC Hausa ta rawaito cewa Misis Zainab ta ce gwamnatin tarayya ta ware kimanin naira tiriliyan 3.36 domin biyan tallafin man fetur ษ—in a cikin wata shida na farkon shekarar 2023.

Ministar ta ฦ™ara da cewa hakan na daga cikin tsarin tsawaita cire tallafin zuwa wata 18 da gwamnatin ta bayyana a shekarar da ta gabata.

An Kama Mai Gyaran Wuta A Cikin Likitocin Bogi Masu Aiki A Asibitoci Fiye Da 100 A Kano



Gwamnatin Jihar Kano ta cafke wani mai gyaran wutar lantarki a cikin jerin likitocin bogi masu aiki a fiye da asibitoci da wuraren karbar magani 100 a jihar.

Jaridar Sahara Reporters ta ruwaito cewa, a duk cikin likitocin na bogi, guda daya ne kacal ya mallaki kwalin sakandire kamar yadda bayanan kwamitin masu bincike suka nuna.

Haka kuma, an samu wani mai gyaran wutar lantarki a cikin jerin likitocin na bogi da yake duba marasa lafiya a wani asibiti mai gado takwas.

An gano wannan asibiti ne dai tare da karin wasu 129 yayin binciken kwamitin da Shugaban Karamar Hukumar Tudun Wada, Ahmad Tijjani Matata ya kaddamar.

Karafe ya ce daya daga cikin likitocin bogin ya tsiyaya wa wata mata jini mai dauke da kwayoyin cutar HIV a jikinta, duk da kuwa cutar zazzabin cizon sauro kadai ta yi korafin tana fama da ita.

“Wannan abin takaici ya kai intaha, domin kuwa mun samu wani mai gyaran wutar lantarki a daya daga cikin asibitocin yana duba marasa lafiya har da karin jini da ruwa da rubuta magani da kuma duba mata masu juna biyu.“Akwai daya daga cikin likitocin bogin da ya kara wa wata mata jini mai dauke da kwayoyin cutar HIV.

“A yanzu duk mun mayar da marasa lafiyar asibiti domin samun kulawar da ta dace, kuma galibi ba su da wata masaniya a kan abin da ya shafi kiwon lafiya.

“Wani daga cikinsu ma cewa ya yi shi malamin kula da masu jinya ne, amma da muka yi bincike mun gano kwalin sakandire kadai ya malla

ka,” a cewar Karafe.

Kada Ku Nemi Na Saki 'Yan Daba - Muhuyi Magaji Ya Gargadi 'Yan Siyasa

Governor Yusuf Celebrates ATM Gwarzo at 66

Kano State Governor, Alhaji Abba Kabir Yusuf, has congratulated the former Deputy Governor and State Coordinator of Arewa For As...