Search This Blog

Tuesday, 3 January 2023

Hotunan yadda shugaba Buhari ya sanya kan kundin kasafin kudi na 2023

 





H
otunan yadda Shugaba Buhair ya rattaba hannu kan kudurin kasafin kudi na 2023 zuwa doka a yau Talata

Kasafin Kudi na 2023  ya tanadi kashe jimillar Naira Tiriliyan 21.83, an samu karin Naira Tiriliyan 1.32 bisa kudurin farko na zartarwa na kashe Naira Tiriliyan 20.51.
๐Ÿ“ทBshir Ahmad

Brentford Ta Casa Liverpool A Firimiyar Ingila

 


Liverpool ta barar da damar matse hudun farko a gasar Firimiyar Ingila, bayan da ta sha kashi 3-1 hannun Brentford a filin wasa na Community da ke Landan.

Masu tsaron bayan Liverpool sun yi sakaci musamman Konate, da hakan ya bai wa Brentford damar dawowa mataki na bakwai, maki biyu tsakaninsu da kungiyar ta Anfield.

Tun a minti na 19 da fara wasa ne Ibrahima Konate ya ci gida bayan an yi bugun kusurwa.

Sai kuma a minti na 42 Wissa ya ci ta biyu aka tafi hutun rabin lokaci 2-0.

Kuma yayin da Liverpool ta matsa don ganin ta farke ne, dan wasan gaban Brentford Mbeumo ya kwaci kwallo hannun Konate ya ci wa kungiyarsa kwallo ta uku a minti na 84.

A yanzu Brentford ta yi wasa shida ba a doke ta ba, a karon farko da ta yi irin haka a sama da shekaru 80, kuma sun koma na bakwai a teburin Firimiyar Ingila.

(AMINIYA)

Yayin da Liverpool ta barar da damar matse hudun farko da tazarar maki daya, kuma ta cigaba da zama na shida maki biyu kacal tsakaninta da Brentford.

Za a sake yi wa Bola Tinubu tarba ta musammam a Kano


A gobe Laraba ne dukkan titunan da suka isa filin wasa na Sani Abacha da ke Kofar Mata, Kano, jama'a za su yi tattaki a jihar Kano da ma sauran jihohin Arewa domin kaddamar da yakin neman zaben dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC. , Asiwaju Bola Ahmed Tinubu,da Mataimakinsa, Sanata Kashim Shettima, a jihar Kano.

A cewar sanarwar da shugaban jam'iyyar APC reshen jihar Kano, Abdullahi Abbas, za a fara kaddamar da yakin neman zaben ne da karfe 10 na safe.

Abdullahi Abbas ya ce mai girma Gwamna Abdullahi Umar Ganduje da jigo a jam'iyyar APC a jihar, yana maraba da Asiwaju Bola Tinubu, mataimakinsa, Sanata Kashim Shettima, jam'iyyar APC. 

Shugaban kwamitin yakin neman zaben jam'iyyar APC na kasa Alhaji Abdullahi Adamu da dukkan gwamnonin jam'iyyar APC na Arewa a jihar Kano zasu zo jiha don yiwa jam'iyyar APC da takararta na shugaban kasa da abokin takararsa, da sauran 'yan tawagarsa, tarbar da suka saba yi, da karbar baki, da ladabi, da kyawawan dabi'u da kuma tsari. a yayin da ya kaddamar da 

Hakazalika Jagaban zai gana da mabiya addinin kirista a Kano da kuma wasu kabilu daban-daban. ‘yan kasa mazauna jihar, a yayin ziyarar mai cike da tarihi.

A dukkan lokuta, ya bukaci mahalarta taron da su zabi jam’iyyar APC a zaben 2023 domin ci gaba da hadin kai da ci gaban kasa.

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC ya yi alkawarin komawa Kano domin gudanar da yakin neman zabe, inda ya ce, “Zan dawo a shirye in yi babban taro. Za su san mun taho.”

A yanzu haka, dan takarar Shugaban kasar na APC na cika alkawarin da ya dauka, yayin da zai isa Kano nan da sa’o’i 24 masu zuwa, domin tabbatar da nasarorin da ya samu a ziyararsa ta Oktoba a nan, da ma. ya kaddamar da yakin neman zabensa na shugaban kasa a jihar zuwa nasarar da ya samu zuwa fadar Aso Villa.

Gwamnatin Tarayya Da Gwamnonin 36 Sun Shiga Yarjejiniyar Sayar da Kamfanonin Wuta 5

 


A wata sanarwa da darekta janar na ofishin sayar da kaddarorin gwamnati wato BPE Alex Okoh ya fitar, ya nuna cewa za a sayar da kamfanonin wuta biyar a kwatan farko na wannan shekara da muka shiga, domin samar da kudade da za a cike gibin Kasafin kudin shekara 2023 da su.

Kasafin kudin na Naira Triliyan 21.82 ya zo da gibi har na kusan Naira triliyan 11 saboda rashin kudin shiga, haka ya sa aka samu gibin kashi 4.8 a ma'unin arzikin kasar wato GDP, wani abu da masanin tattalin arziki na kasa da kasa Shuaibu Idris Mikati ya nuna damuwa akan batun sayar da kamfanonin yana cewa akwai abin dubawa a wannan batun sayar da kamfanonin nan domin kar a sake fadawa cikin halin kakanakayi.

  • https://alheekmah.blogspot.com/2023/01/labari-da-dumiduminsa-yusuf-babangida.html
  • https://alheekmah.blogspot.com/2023/01/obasanjo-ya-zama-tamkar-dan-bakin-ciki.html

Mikati ya ce haka aka sayar da kamfanoni ga wadanda ba su da kudi a zamanin gwamnatin da ta shude, har suka gagara ba kasa wadataccen wuta. Mikati ya ce ya yi mamakin wai bankin UBA ne za sayar wa da kashi 60 na kamfanonin inda ya kira da a duba lamarin da idanun basira.

Kamfanonin da ke samar da wutan lantarki ( GENKOS) wadanda za a sayar sun hada da tashar wutar lantarki ta Geregu, da cibiyar samar da wutar lantarki mai karfin megawatt 562 a Calabar Jihar Kros Ribas da kuma cibiyar wutar lantarki ta Olorunsogo, amma ga mai fashin baki a al'amuran zamantakewa da gudanar da mulki Dokta Abdulrahaman Abu Hamisu ya ce wannan ya zo masa da mamaki domin ya kamata Najeriya ta yi damokradiya da gaske.

Abu ya ce matakin da ake dauka bai dace ba domin yana ba sai an sayar da kaddarori kafin a cike gibin kasafin kudi ba.

Abu ya ce ya kamata Najeriya ta yi koyi da wasu kasashe da suka cigaba wajen karban haraji maimakon sayar da kaddarori. Abu ya koka da yadda ake sace kudaden kasa ba tare da an kamo barayin ba. Ya kara de cewa idan ba a hanzarta samo hanyoyin kudaden shigowa ba, to da sauran rina a kaba, musamman yanzu da ake shirin zaben sabon gwamnati.

To sai dai ga tsohon mai ba ministan makamashi shawara a harkar gudanarwa, Idris Mohammed Madakin Jen yana mai ganin an dauki mataki mai kyau da zai kawo wa kasa wutar lantarki.

Idris ya ce dama kudaden na jihohi da kananan hukumomi ne, kuma lokaci ya yi da za a basu abinsu. Idris ya ce bankin UBA ce ta samo masu hannu da shuni da za su saye kamfanin samar da wutan lantarki musamman na birnin taraiyya Abuja.

Majalisar kula da harkokin kasuwanci ta kasa NCP ta amince da tsarin gudanar da aikin gina wani katafaren kamfani na dalar Amurka biliyan 3 da zai samar da wutan lantarki mafi girma a Afirka ta Yamma.

VOA

Monday, 2 January 2023

LABARI DA DUMIDUMINSA: Yusuf Babangida (Dawo-dawo) ya raba gari da Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso

Dan majalisar Jaha mai wakiltar yankin karamar hukumar Gwale, Yusuf Babangida (Dawo-dawo) ya raba gari da Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso, ya dawo Jam'iyyar #APC 

๐Ÿ“ท Mai taimakawa Gwamna na musamman kan harkokin daukar Hoto (Aminu Dahiru Ahmad) 

Obasanjo ya zama tamkar dan bakin ciki - Fadar Shugaban kasa

Fadar Shugaban Najeriya ta mayar da kakkausan martani kan kalaman da Tsohon Shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo ya yi a saฦ™onsa na sabuwar shekara.

A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban Najeriya Malam Garba Shehu ya fitar, sanarwar ta ce Obasanjo ba zai taษ“a daina caccakar Shugaba Muhammadu Buhari ba sakamakon Obasanjon ba zai daina baฦ™in ciki kan duk wani wanda ya sha gabansa a ayyukan ci gaban ฦ™asa ba.

Fadar shugaban ฦ™asar ta buga misali da cewa Shugaba Buhari ya kammala gadar Neja ta biyu bayan an yi shekara 30 ana alฦ™awura a kanta.

Haka kuma fadar shugaban ฦ™asar ta ce Obasanjo ya yi wa kudu maso gabashin Najeriya ฦ™arya domin ya samu ฦ™uri'unsu, amma Shugaba Buhari bai samu ฦ™uri'unsu ba amma duk da haka sai da ya yi musu aikin gadar.

Fadar shugaban ฦ™asar ta kuma ce Obasanjo yana baฦ™in ciki ne sakamakon yana ganin yadda Buhari ke samun lambobin yabo da kuma yadda shugaban ke ci gaba da da'awar cewa zai tabbatar an gudanar da sahihin zaษ“e fiye da wanda ya kawo sa kan karagar mulki.

Haka kuma fadar ta zargi Obasanjo da lalata dimokraษ—iyya a Najeriya bayan kitsa tsige wasu gwamnoni a ฦ™asar da suka haษ—a da Joshua Dariye da Rashidi Ladoja da Peter Obi da Chris Ngige da Ayo Fayose.

Wannan martanin na fadar shugaban Najeriya duk na zuwa ne bayan tsohon Shugaban Najeriyar Chief Olusegun Obasanjo ya ce Peter Obi ne zaษ“insa a zaษ“en 2023 haka kuma Obasanjon ya caccaki gwamnatin Shugaba Buhari

Obasanjo ba zai iya kawo mazabarsa ba - Tinubu


Dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu, ya gargadi Peter Obi, cewa kada ya rudu da goyon bayansa da tsohon shugaban kasar Najeriya, Olusegun Obasanjo ke yi.

Tinubu ya ce goyon bayan Obasanjo ba zai kai Peter Obi ko’ina ba, saboda Obasanjo ba zai iya lashe akwatin mazabarsa ba.

“Bincikenmu mun gano Obasanjo bai taba nasarar sa wani ya lashe kujerar shugaban kasar Najeriya ba.

“Ko a Jihar Ogun babu wanda zai dogara da shi don lashe kujerar gwamna ko kansila,” in ji Tinubu  ta hnnun Daraktan yada labarai na kwamitin yakin neman zaben Tibubu, Bayo Onanuga.

Ya ci gaba da cewa, “Muna tausaya wa Peter Obi domin Obasanjo ba zai iya lashe masa akwatin mazabarsa da ke Abeokuta ba a zaben ranar 25 ga watan Fabrairun 2023.”

Tsohon gwamnan na Legas, ya bayyana yadda Obasanjo ya goyi bayan tsohon mataimakinsa, Atiku Abubakar a zaben 2019 kuma ya sha kaye a hannun Shugaba Buhari.

Tinubu ya jadadda cewa da taimakonsa Buhari ya samu gagarumar nasara a zaben tare da tika Atiku da kasa.

Ya ce tarihi ne zai sake maimaita kan sa a zaben da ke kara kartowa a watan Fabrairu.


Rasha ta ce, an kashe mata sojoji 63


Rasha ta ce, an kashe mata sojoji 63 a wani kazamin hari da Ukraine ta kaddamar kan dakarunta a karshen makon da aka gudanar da bukukuwan shiga sabuwar shekara.

A cikin wata sanarwa da ba a saba ganin irinta, Ma’aikatar Tsaron Rasha ta ce, an kashe sojojin kasar 63 sakamakon wani harin makami mai linzami da Ukraine ta kaddamar kan birnin Makiivka da ke gabashin Ukraine wanda Moscow ta mamaye.

Wannan ne asarar sojoji mafi girma da Rasha ta yi tun bayan barkewar yaki tsakaninta da Uktraine a ranar 24 ga watan Fabairun da ya gabata.

Rasha ta ce, an yi amfani da shu’umin na’urar cilla makaman roka da aka kera a Amurka wajen kaddamar mata da wannan farmakin, yayin da a Babban Hafsan sojin Ukraine ke cewa, dakarunsu ne suka kai harin a Makiivka.

Ya kara daa cewa, sun lalata wuraren ajiyar makaman Rasha har guda 10 a yayin harin.

Tun da fari, Sashen Yada Labarai na Rundunar Sojin Ukraine ya yi ikirarin cewa, kimanin sojojin Rasha 400 ne suka mutu a Makiivka sabanin 63 da aka ba da rahoto.

An sace gangan man fetur miliyan 17 a Najeriya

 


Wani sabon bincike da aka gudanar kan lamurran da ke wakana a fannin arzikin man Najeriya ya nuna cewar, an fitar da ganga sama da miliyan 17 na danyen mai daga kasar zuwa kasashen ketare ta barauniyar hanya, a tsakanin shekarar 2016 zuwa 2020.

Rahoton da Andrew Ogochukwu Onwudili, babban jami’i mai binciken kudi na Najeriya ya fitar, wanda kuma jaridar The Nation da ke kasar ta ruwaito, ya kiyasta cewarkwatankwacin kudin danyan man fetur din da a iya cewa an sace daga kasar ya kai Dala Tiriliyan 1 da biliyan 20, da miliyan 969 da dubu 281.

A cikin rahoton, an tuhumi  Ofishin Akanta-Janar na gwamnatin Najeriya da laifin biyan sama da Naira biliyan 73 ga jami’an da suke tantance inganci da adadin albarkatun mai da isakar gas din da ake shirin fitar da su daga kasar.

Mai binciken yadda ake kashe kudaden Najeriyar ya bayyana cewar, kudaden da aka biya ba tare da an yi  kasafinsu ba, ya saba wa tanadin doka a sashi na 80(4) na kundin tsarin mulkin kasar na shekarar 1999.

Tsohon babban mai binciken kudi, Adolphus Agughu ne ya sanya hannu kan rahoton, aka kuma mika kundin ga magatakardar majalisar dokokin Najeriya a ranar 29 ga Yuni, na shekarar da ta gabata.

RFI

Kotun Senegal ta daure 'yan majalisa saboda dukan mace

 


Kotu a Senegal ta yanke hukuncin daurin watanni 6 a kan ‘yan majalisar dokokin kasar su biyu na bangaren 'yan adawa, saboda samun su da laifin dukar abokiyar aikinsu daga bangaren masu rinjaye.

A ranar 1 ga watan Disambar da ya gabata ne dan majalisar dokoki Massata Samb ya yi dirar mikiya a kan wata ‘yar majalisar mai suna Amy Ndiaye, bisa zargin furta kalaman batanci a kan Moustapha Sy, shugaban wata jam’iyyar siyasa da ke cikin gungun ‘yan adawa sannan kuma shehin malamin addinin musulunci da ake mutuntawa a kasar.

Wasu hotuna da ake rika yadawa sun nuna yadda Massata Samb ya lafta wa Amy Sy mari a cikin zauren majaliar ‘yayin da abokinsa dan majalisa Mamadou Niang ya sa kafa ya noshi matar a ciki bainar jama’a.

Bayan faruwar wannan lamari, an kwantar da ‘yar majalisa Amy Sy a asibiti bayan da bayanai suka tabbatar da cewa tana dauke da juna biyu a lokacin faruwar lamarin, to sai dai a lokacin da yake yanke hukunci, alkali ya yi watsi da zargin yunkurin kisa kamar dai yadda masu shigar da kara suka bukata.

Ko baya ga hukuncin dauri, hakazalika kotun ta bukaci mutanen biyu su biya tarar cfa jika dari a matsayin diyya saboda dukar da suka yi wa ‘yar majalisar wadda ta fito daga jam’iyyar shugaba Macky Sall.

Kada Ku Nemi Na Saki 'Yan Daba - Muhuyi Magaji Ya Gargadi 'Yan Siyasa

Muhuyi’s 60 Days: Kano Intensifies the Fight Against Drug Abuse

Sixty days into his leadership of the newly established Kano State Multi-Agency Task Force on Drug Abuse and Illicit Trafficking...