ฦ˜udurin wanda ya samu goyon bayan ฦ™asa 87, sai 26 suka nuna adawa da shi ciki har da Amurka da Burtaniya.

Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya tana da ฦ™arfin yanke hukunce-hukuncen da wajibi ne a yi musu biyayya, amma ba ta iya tilasta aiki da su.

ฦ˜uri'ar ta ranar Juma'a, ta zo ne kwana ษ—aya bayan rantsar da Benjamin Netanyahu a matsayin firaminista na gwamnatin Isra'ila mafi tsaurin ra'ayi a tarihi.

Isra'ila ta mamaye Gaษ“ar Yamma da Kogin Jordan kuma ko da yake ta janye daga Gaza amma har yanzu Majalisar ฦŠinkin Duniya tana kallon yankin a matsayin wanda ke ฦ™arฦ™ashin mamaye.

Isra'ila na iฦ™irarin cewa gaba ษ—ayan ฦ˜udus ne babban birninta, yayin da Falasษ—inawa ke cewa Gabashin ฦ˜udus ne babban birnin wata ฦ™asarsu da za a kafa nan gaba.

Amurka na cikin tsirarun ฦ™asashen da suka amince da ฦ˜udus a matsayin babban birnin Isra'ila.

Falasษ—inawa na iฦ™irarin mallakar Gaษ“ar Yamma da Kogin Jordan da Gabashin ฦ˜udus wanda Isra'ila ta haษ—e cikin ฦ™asarta da Zirin Gaza don kafa ฦ™asar da suke fatan gani a nan gaba.

Jami'an Falasษ—inu sun yaba wa ฦ™uri'ar da Majalisar ฦŠinkin Duniya ta kaษ—a a matsayin wata nasara a gare su.

Nabil Abu Rudeineh ya ce lokaci ya yi da za a kama Isra'ila "da alhaki kan laifukan da ake ci gaba da aikatawa a kan jama'armu".

Sabon firministan Isra'ila, a nasa ษ“angare, ya bayyana matakin a matsayin wani "abin ฦ™yama"."Al'ummar Yahudawa ba 'yan mamaya ba ne a ฦ™asarsu ta haihuwa kuma ba masu mamaya ba ne a babban birnin ฦ˜udus da Allah ya ba mu kuma babu wani ฦ™udurin Majalisar ฦŠinkin Duniya da zai iya kankare wannan gaskiyar abin tarihi," in ji Mista Netanyahu ranar Asabar da yamma.

A ranar Alhamis ne, Benjamin Netanyahu ya sake dawowa a matsayin fira minista na wata gwamnatin gamin gambiza ta ฦ™awancen masu tsattsauran ra'ayin kishin ฦ™asa da masu tsananin kishin Yahudanci na ainihi.

ฦ˜a'idar farko da ke yi wa gwamnatin jagora wadda aka wallafa ranar Laraba, ta ayyana cewa "Al'ummar Yahudawa ne ke da 'yancin da ba wata tababa a kan duk yankunan ฦ™asar Isra'ila, su kaษ—ai".

Ta ce a ciki har da Gaษ“ar Yamma da Kogin Jordan da ke ฦ™arฦ™ashin mamaye kuma ta yi alฦ™awarin "ci gaba da kuma bunฦ™asa" matsugunnai a can.

Yahudawa kimanin 600,000 ne ke zaune a matsugunnan da aka gina guda 140 tun bayan mamayen da Isra'ila ta yi wa Gaษ“ar Yamma da Gabashin ฦ˜udus a shekarar 1967.

Mafi rinjayen ฦ™asashen duniya na kallon matsugunnan a matsayin haramtattu a ฦ™arฦ™ashin dokokin ฦ™asashen duniya, ko da yake, Isra'ila tana jayayya da hakan.

Sabuwar gwamnatin ta kuma yi alฦ™awarin halatta wasu cibiyoyin soji kimanin 100 a Gaษ“ar Yamma waษ—anda aka gina ba tare da izinin Isra'ila ba - kuma za ta haษ—e Gaษ“ar Yamman da ฦ™asarta.

Mai magana da yawun Burtaniya a MajaDu na cewa ba ya jin kai batun gaban kotun hukunta manyan laifuka zai "taimaka wajen dawo da ษ“angarorin kan teburin tattaunawa". Ya kuma ce hakan "bai kamata ba tun da babu yardar duk ษ“angarorin biyu" na neman shawarar kotu a kan "abin da tun ainihi taฦ™addama ce ta ษ“angare biyu".

(BBC HAUSA)