’Yan Najeriya Na Kushe Ni Duk Kokarina —Buhari

 

’Yan Najeriya Na Kushe Ni Duk Kokarina —Buhari


Shugaba Buhari ya ce ba zai yi kewar shugabancin Najeriya ba saboda kushe shi da ’yan kasar ke yi duk kokarinsa.

Buhari ya bayyana hakan ne a liyafar da ’yan uwa da abokan arziki suka sirya masa don taya shi murnar cikarsa shekaru 80 da haihuwa a Abuja, inda ya ce ’yan Najeriya na raina duk fadi tashin da yake kan kasar, don haka ba zai yi kewar mulkar ta ba idan wa’adin mulkinsa ya cika.

“Abubuwan da zan yi kewar su a matsayina na shugaban kasa a gwamnatance ba su da yawa, saboda raina kokarina da ’yan Najeriya ke yi a kodayaushe.

“Ina iya bakin kokarina, amma wasu na ganin za su iya tsoratar da ni don su samu yadda suke so,” in ji shi.

Da yake amsa tambayar ’yan jarida kan jita-jtar da ake yadawa cewa ba shi ne Buharin da ’yan kasar suka sani a baya ba, Buhari ya ce yana sane da hakan, sai dai sanin cewa ’yan Najeriya mutane ne masu son raha ya sa bai damu ba.

Ya ce wannan batu ba abin dariya ba ne saboda wasu ne ke kokarin amfani da hakan don kau da hankalin ’yan Najeriya daga kan abubuwan da suke da muhimmaci.

Popular posts from this blog

Yanzu - Yanzu: Bankuna Zasu Karbi Tsofaffin Kudi Ko da Bayan Karewar Wa'adi - Emefiele

Zababben Gwamnan Kano Ya Kafa Kwamitin Karbar Mulki