MAI MARTABA SARKIN KANO ALHAJI AMINU ADO BAYERO: Baƙon Shehu Maghili
Daga: Magaji Galadima
A ranar Litinin 12 ga watan Disamba 2022 gwamnatin ƙasar Aljeriya ta aiko da wani jirgi na musamman domin ya ɗauki mai martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero zuwa ƙasar ta Aljeriya domin halartar taron duniya na musamman don tunawa da rayuwa da kuma aiyukan shahararren malamin addinin Musulunci sharifi kuma masanin falsafa wato Shehun malami Muhammad Abdurrahman al-Maghili wanda yayi rayuwarsa tun a ƙarni na goma sha biyar.
Jigin ya tashi daga Kano da karfe 9:45 na safe. A cikin waɗanda suka samu alfarmar raka Sarki wannan tafiya akwai Sarkin Dawakin Tsakar-gidan Kano Alhaji Ahmad Ado Bayero hakimin Kumbotso da Ambasada Ahmad Umar Ɗanmalikin Kano da Dakta Ibrahim Ɗahiru Bauchi wanda ya wakilci Sheikh Ɗahiru Bauchi da Malam Isa Sanusi Bayero da Dakta Lawi Atiku Sanka da kuma ni Magaji Galadima Kachallan Kano, sannan sai wasu malamai da sharifai na Kano da kuma fadawa hadiman Sarki.
Jirgin ya ɗan yada zango a Yamai babban birnin Jamhuriyar Nijar inda ya ɗauki Sultan na Agadas da Sarkin Sharifan ƙasar Nijar da sauran malamai da muƙaddamai da malaman jami’a. Sarkin Kano da ‘yan tawagarsa sun sauka a Aljiyas babban birnin Aljeriya da misalin karfe 5:00 na yamma inda manyan ministoci da jami’an gwamnati dana diflomasiyya da kuma manyan malamai suka taryi mai martaba Sarki da tawagarsa. Daga nan akayi jerin-gwano aka raka Sarki masaukinsa.
A rana ta biyu wato Talata Sarki da ‘yan tawagarsa suka fita zuwa wajen taron ƙasa da ƙasa da aka shirya domin tunawa da shahararren malamin addinin musulunci masanin falsafa kuma sharifi wato Shehu Muhammad Abdurrahman al-Maghili wanda yayi rayuwarsa tun a ƙarni na sha biyar kuma har yazo Kano zamanin Sarki Muhammadu Rumfa.
Al-Maghili ya zauna a Kano tsawon lokaci kuma ya bijiro da sababbin tsare-tsare masu muhimmanci a fadar Kano, kana kuma yayi rubuce-rubuce akan ibada da hukunci, sannan ya rubuta wani kundi da ya zama daftari na jagorar duk wani sarki na Kano dama nahiyar yammacin Sudan.
Taron an shirya shi ne a babban ɗakin taro na ƙasar dake birnin Aljiyes. A ranar buɗe taron Sarkin Kano da tawagarsa sun isa wajen da misalin karfe 9;00 na safe amma sai aka kaishi wani ɗaki ya zauna a kauwame har sai da ɗakin taron yayi cikar kwari sannan aka shigar dashi.
Toh dama an ɗauki makwanni ana ta yaɗawa a kafafen labarai cewa ƙasar ta Aljeriya zata karɓi bakuncin wani ƙasaitaccen Sarki mai alfarma da daraja daga garin Kano a Nijeriya, don haka mutanen ƙasar duk sun zaku suga wannan ƙasaitaccen Sarki. Saboda da haka yana shiga ɗakin taron sai duk aka tashi tsaye waje ya kaure da sowa da tafi, mata kuma na rabka guɗa, su kuma ‘yan badujala suka goce da wani irin take na musamman da ake kaɗawa mashahuran mutane in sun shigo wajen taro.
An ɗauki tsawon lokaci kafin a samu natsuwa lamurra su koma daidai sannan mai martaba Sarkin Kano figinai suka yi sayi ya zauna aka gyara aka kimtsa sannan aka fara gudanar da taro.
Daga nan ne kuma sai aka fara jawabai, babban ministan harkokin addini na ƙasar shine ya wakilci shugaban ƙasa kuma yayi jawabin maraba ga mahalarta taron kana yayi godiya ta musamman ga Sarki Aminu Bayero a madadin shugaban ƙasa da al’ummar ƙasar baki ɗaya. Shima Sarkin na Kano yayi jawabi inda ya nuna farin ciki da godiya ga gwamnati da jama’ar ƙasar baki ɗaya saboda kyakkawar taryar da aka yi masa, ya kuma isar da gaisuwar jama’ar masarautar Kano da Nijeriya baki ɗaya a garesu.
Sarkin ya yaba da hangen nesan waɗanda suka assasa wannan taro na tunawa da Shehu Maghili wanda yace yafi cancanta a kira shi da Bakano maimakon dan Aljeriya saboda da dalilai da dama. Ya baiyanawa mahalarta taron cewa a yanzu haka a cikin birnin Kano akwai unguwar Sharifai waɗanda asali jama’ar da suka zo Kano tare da Shehu Maghili sune ke zaune…