EFCC Ta Yi Gwanjon Kadarorin Su Diezani A Kasuwa


Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) ta sanar da yin gwanjon wasu kadarorin da ta kwace daga hannun ’yan siyasa da ’yan kasuwa ga ’yan Najeriya masu bukatar saya.

Hukumar ta ce kadarorin dai na jibge ne a Jihohin Legas da Ribas da Abuja da Anambra da Gombe da Ebonyi da Kaduna da Delta da Edo daKwara da Kuros Riba da Osun da kuma Oyo.

Aminiya ta gano cewa daga cikin kadarorin har da na tsohuwar Ministar Man Fetur ta Najeriya, Diezani Allison-Madueke, wadanda hukumar ta ce an mallake su ta haramtacciyar hanya.

A wata sanarwar da hukumar ta wallafa ranar Asabar, EFCC ta ce daidaikun mutane da kuma kamfanoni da kungiyoyin da ke son sayen kayan da aka yi gwanjon dole ne su kasance ba a taba daure su ba a baya.

Kadarorin da aka yi gwanjon nasu sun hada da wani gida a rukunin gidaje na Heritage Court a Jihar Ribas da wani mai daki uku a rukunin gidaje da ke rukunin gidaje na Foreshore a unguwar Ekoyin Jihar Legas fa sauran su.

Popular posts from this blog

Yanzu - Yanzu: Bankuna Zasu Karbi Tsofaffin Kudi Ko da Bayan Karewar Wa'adi - Emefiele

Zababben Gwamnan Kano Ya Kafa Kwamitin Karbar Mulki