Buhari Zai Sayo Motocin Sulke 400 Don Tsaron Su Abuja



Shugaba Buhari ya amince da sayo motocin sulke guda 400 don amfani da su wajen tabbatar da tsaro a babban birnin tarayya da jihohin Nasarawa da kuma Neja.

Sabon Kwamandan Rundunar Tsar Birgediya, Manjo-Janar Mohammed Usman ne ya bayyana hakan a ranar Laraba a jawabin godiyarsa a bikin nada masa anininsa bayan karin girma da ya samu.

Shugaban kasa tare da Babban Hafsan Sojin Kasa, Laftanar-Janar Faruk Yahaya da uwargidan kwamandan, Dokta Rekiya Usman, ne suka nada masa aninin.

Jim kadan bayan kammala bikin a Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja, shugaban kasa ya bayyana shi a matsayin fitaccen jami’in da yake yi wa kasa hidima.

Buhari, a cikin wata sanarwa da hadiminsa, Garba Shehu ya fitar, ya yaba wa iyalan kwamandan bisa hakurin da suka yi na jure kalubalen da ya fuskanta wajen gudanar da aikinsa.

A nasa jawabin, Manjo-Janar Usman, ya gode wa shugaban kasa bisa irin gagarumin goyon bayan da ya bai wa Rundunar Sojin Najeriya, inda ya bayar da umarnin sayo motocin sulke guda 400.

A cewarsa, sun isa su tabbatar da tsaron yankin babban birnin tarayya, Nasarawa da sassan Jihar Neja.Ya bayyana farin cikinsa kan karin girma da aka yi masa, wanda ya ce  zai kara zaburar da shi wajen yin abin da ya dace game da nauyin da ya rataya a wuyansa.

(AMINIYA)


Popular posts from this blog

Yanzu - Yanzu: Bankuna Zasu Karbi Tsofaffin Kudi Ko da Bayan Karewar Wa'adi - Emefiele

Zababben Gwamnan Kano Ya Kafa Kwamitin Karbar Mulki