Hisbah Ta Rufe Wuraren Shan Giya Sama Da 100 A Zariya



Wata kungiyar addinin Musulunci mai zaman kanta mai suna Hisbah, ta jagorance garkame wuraren shan giya sama da 100 a Karamar Hukumar Sabon Gari da ke Jihar Kaduna.

Dan Majalisar Dokokin Jihar Kaduna mai wakiltar mazabar Sabon Gari, Garba Datti Babawo ne ya tabbatar da hakan, yayin gabatar da hsaidar kammala karbar horo ga ’yan kungiyar su 750 da ya gudana a hedkwatar Karamar Hukumar ta Sabon Gari.

Dan majalisar ya ce tun da Karamar Hukumar take ba ta taba samun sa’ida daga ayyukan badala ba sama da lokacin da aka kafa rundunar ta Hisbah.

Daga nan sai Babawo ya ja kunnen dakarun da su tabbatar suna bin dokokin dokoki yayin gudanar da ayyukansu.

Tun da farko sai da Kwamandan rundunar a yankin, Abubakar Auwal ya ce dakarun su 750 sun sami cikakken horo a harkar tsaro kan yadda za su gudanar da ayyukansu.

Kwamnadan ya kuma ce 500 daga cikin dakarun maza ne, yayin da 250 kuma mata ne, kuma za su sadaukar da kawunansu wajen hidimta wa al’umma.

Popular posts from this blog

Yanzu - Yanzu: Bankuna Zasu Karbi Tsofaffin Kudi Ko da Bayan Karewar Wa'adi - Emefiele

Zababben Gwamnan Kano Ya Kafa Kwamitin Karbar Mulki