Search This Blog

Monday, 16 January 2023

LABARI DA DUMIDUMINSA! Jami’an Hukumar I DSS Sun Mamaye ofishin Gwaman Babban Bankin Najeriya

Jami’an hukumar tsaro ta farin kaya, SSS, sun mamaye hedikwatar babban bankin Najeriya CBN, inda suka karbe ofishin gwamnan babban bankin, Godwin Emefiele.

Jaridar DAILY NIGERIAN ta rawaito cewa an yi artabu tsakanin jami’an SSS da Mista Emefiele kan zargin bada tallafin yaki da ta’addanci.

A baya dai hukumar leken asirin ta nemi kotu ta kama Mista Emefiele amma ya fita kasar domin hutun shekara da zai kare a gobe 17 ga watan Janairu.

Sai dai a watan Disamba ne babbar kotun birnin tarayya ta haramtawa SSS kama, gayyata, ko kuma tsare Mista Emefiele.

Jami’an SSS da suka isa hedikwatar CBN a ranar Litinin da ta gabata, sun shigo da motoci kusan 20 dauke da jami’an tsaro.

Jami’an sun kuma hana duk ma’aikatan bankin shiga ofishin Mista Emefiele.

Peter Afunanya, mai magana da yawun SSS, har yanzu bai amsa tambayar da dan jaridan ya aike masa ba.

Cikakkun bayanai daga baya…

Messi da Mbappe da Neymar sun yi wasa tare karon farko bayan kofin duniya

A ranar Lahadi Kylian Mbappe da Lionel Messi da kuma Neymar suka buga wa Paris St Germain wasa tare karon farko tun bayan kammala Gasar Kofin Duniya a Qatar.

Argentina ce ta lashe kofin da Messi ya daga, bayan da suka yi nasara a kan Faransa tawagar Mbappe, yayin da Brazil ta Neymar ba ta kai bante ba.

Sun kuma buga wasan Ligue 1 na faransa fafatawar zagaye na 19, inda Rennes ta yi nasara da ci 1-0.

Tun farko an bai wa Messi karin lokacin hutu, domin ya samu damar murnar lashe kofi da suka yi wa kasar na uku jumulla

Sai dai kuma Messi ya ci kwallo da ya koma yiwa PSG tamaula a tsakiyar mako da ta tashi 2-2 da Angers.

Shi kuwa Mbappe bai samu buga wasa biyu ba, bayan da ya je hutu birnin New York tare da abokinsa Achraf Hakimi.

An sa ran za a fara wasa da Mbappe ranar ta Lahadi, sai ya fara da zaman benci daga baya ya canji Hugo Ekitike, inda ya hadu da Messi da Neymar daga gaba.

Buhari Zai Karbo Kyautar wanzar da zaman lafiya a Mauritaniya

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a ranar Talata mai zuwa zai karbi kyautar “Karfafa zaman lafiya ta Afirka” a birnin Nouakchott na kasar Mauritaniya.

Kakakin Shugaban, Femi Adesina ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa ranar Lahadi, inda ya ce Buharin zai karbi kyautar ce saboda irin rawar da yake takawa wajen wanzar da zaman lafiya da kuma yin sulhu a kasashe daban-daban na nahiyar Afirka.

Noman masara zai yi wahala a damina mai zuwa — Kamilu Sigau
Ko sanyi na da alaka da yawaitar tashin aljanu da iskokai?
Kwamitin Zaman Lafiya na Abu Dhabi, ne dai zai gabatar wa Buhari kyautar.

An kafa kwamitin na Shugabannin Kasashe ne a shakara ta 2014 domin a lalubo hanyoyin bunkasa zaman lafiya da kwanciyar hankali a duk fadin duniya.


Adesina ya kuma ce gabanin Buharin ya karbi kyautar, Shugaban zai halarci taron kasashen Afirka kan samar da zaman lafiya, inda zai ma gabatar da makala a wajen taron.

Kakakin ya kuma ce Buhari zai bar Najeriya ne ranar Litinin, sannan ana sa ran dawowarsa ranar Laraba.

Sanarwar ta kuma ce yayin ziyarar, Buhari zai sami rakiyar ministan Harkokin Waje, Geoffrey Onyeama, da na Tsaro, Manjo-Janar Bashir Salihi Magashi (mai ritaya) da mai ba shi shawara an harkokin tsaro, Mohammed Babagana Mongunoda kuma Shugaban Hukumar Leken Asiri ta Najeriy, Ahmed Rufai Abubakar.
(AMINIYA) 


Sunday, 15 January 2023

Muhawarawar 'yan takarar gwamna ta BBC : Kungiyar Global Group Ta Taya Gwamna Ganduje Murnar bisa Kwazon Gawuna



Wata kungiya ta duniya da ta kware wajen tantance muhawarar siyasar ‘yan takara a fadin duniya , Dandalin tantance muhawarar siyasa (PODAF) ta taya gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano murnar kwazon da mataimakin gwamnan jihar kuma dan takarar gwamna na jihar, Nasiru Yusuf Gawuna ya yi a wajen muhawarar yan takarar gwamna da Sashen Hausa na Gidan Rediyon Birtaniya (BBC) ya shirya a Makarantar koyar da harkokin Kasuwancin Aliko Dangote da ke Jami’ar Bayero, Kano, ranar Asabar.

A cikin wata wasika da aka aika wa gwamnan kuma mai dauke da sa hannun babban jami’in kungiyar na Najeriya, Mista Johnson Craig, ya bayyana cewa, “Mun gamsu matuka da yadda mataimakin ku, wanda kuma dan takarar gwamna ne na jam’iyyar APC ya yi a lokacin da aka kammala muhawarar zaben gwamna da sashen Hausa na BBC ya shirya."

Cikin sanarwar da babban sakataren yada labaran Gwaman, Malam Abba ya fitar, ta ce Wasikar a wani bangare na cewa, “Kungiyarmu ta ga ya zama dole mu taya mai girma gwamna murna bisa kyakkyawan kwazon da mataimakinsa Gawuna ya nuna, wanda ya yi kyau kuma ya tabbatar da haka, dan takarar APC gogagge ne, kwararre, kuma dan siyasa mai son zaman lafiya."

Yayin da take taya gwamnan murna, kungiyar ta PODAF ta yi imanin cewa, Kano tana da zabi mafi kyau a Mataimakin Gwamna, Dokta Gawuna. Kuma ya jaddada cewa, muhawarar ta nuna yadda Mataimakin Gwamna yake mai da hankali, kishin kasa da azama.

Ya kara da cewa, "Zaben Dr Gawuna da abokin takararsa Murtala Sule Garo, tare da dimbin gogewar da suke da shi wajen gudanar da mulki, tun daga tushe, zai taka rawa sosai a zabukan da ke tafe, wannan ya bayyana a Muhawarar BBC. Inda Gawuna ya bayyana. ya burge duk masu zabe masu tunani, kamar yadda ya bayyana da kuma mai da hankali kamar yadda ya bayyana."

Tinubu ya nada Jega, Abdulaziz a matsayin masu taimaka masa


Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya karfafa ofishin yada labaran sa tare da yiwa wasu sabbin mataimaka guda biyu.

Wadanda aka nada sun hada da Mahmud Jega a matsayin mai ba da shawara na musamman kan harkokin jama’a da Abdulaziz Abdulaziz a matsayin mataimaki na musamman kan harkokin yada labarai

Har zuwa lokacin nadin nasa, Jega, babban edita, ya kasance manazarci a cikin gida na Arise TV kuma yana gudanar da shafi na mako-mako na jaridar Thisday.

Shi ne kuma Babban Editan buga ta yanar gizo, Tarihi na Karni na 21st.

Abdulaziz wanda ya lashe kyautar dan jarida kuma mai tasiri a shafukan sada zumunta, ya kasance har zuwa lokacin da aka nada shi mataimakin babban editan jaridar Daily Trust.
Ya kuma kafa wani shiri na safe ga Trust TV, reshen kungiyar Media Trust Group.

Wata sanarwa a karshen mako da ofishin yada labarai na Tinubu mai dauke da sa hannun Mista Tunde Rahman ta ce, wadanda aka nada za su yi amfani da kwarewarsu da zurfin fahimtar al’amuran siyasa a fadin kasar nan musamman Arewa wajen bunkasa ayyukan kungiyar kafafen yada labarai.

Bayan kammala karatunsa na malami a fannin kimiyyar halittu a jami'ar Usman Danfodio da ke Sokoto, Jega ya yi aikin jarida ba tsayawa sama da shekaru talatin.

Ya yi shekara 13 a matsayin Manajan Edita, Edita, Mataimakin Babban Edita da Shugaban Edita na Jaridar Daily Trust. Kafin haka, ya yi aiki a matsayin Edita, New Nigerian Newspapers, Editan Mujallar Sentinel, Kaduna, da Mataimakin Editan Mujallar Citizen.

Abdulaziz yana da gogewa ta fannin bugawa, kan layi, watsa shirye-shirye da kafofin watsa labarun. Ya yi aiki a matsayin wakilin jarida, shugaban ofishin kuma editan yanki na jaridar LEADERSHIP, kafin ya koma jaridar Blueprint wanda ya bari a shekarar 2017 a matsayin mataimakin edita.

Kafin ya koma Aminiya a farkon shekarar 2021, Abdulaziz ya kuma yi aiki da jaridar PREMIUM TIMES ta kan layi a matsayin Mataimakin Edita.


Jami'an tsaro sun kuɓutar da fasinjojin jirgin ƙasan Edo 12


Hukumomin jihar Edo da ke kudu maso kudancin Najeriya ta ce an kuɓutar da fasinjoji 12 na jirgin ƙasa, da 'yan bindiga suka yi garkuwa da su a tashar jiragen ƙasa da ke jihar a makon da ya gabata.

An kama wasu daga cikin 'yan bindigar da suka yi garkuwa da su, to sai dai wasu daga cikinsu sun tsere tare da wasu fasinjojin biyu a lokacin da jami'an tsaro ke ƙoƙarin kuɓutar da su.

Hukumomin jihar sun ce an kuɓutar da mutanen 12 a lokacin da jami'an tsaro suka yi wa masu garkuwa da mutanen kwanton ɓauta.

Tuni aka kai mutanen da aka kuɓutar ɗin asibiti domin duba lafiyarsu.

Gwamnatin jihar ta alƙawarta ci gaba da nemo sauran fasinjojin biyu da ke hannun 'yan bindigar.

Gwamnan jihar ya soki hukumar kula da sufurin jiragen ƙasa ta ƙasar kan gaza samar da tsaro kan tasoshin jiragen ƙasan duk da faruwar makamancin wannan hari a jihar Kaduna da ke arewacin ƙasar a shekarar da ta gabata.

Tun da farko dai hukumomin sun ce mutum 32 ne 'yan bindigar suka yi garkuwa da su a harin da suka kai tashar jirgin ƙasa ta Igueben a makon da ya gabata, to sai dai daga baya hukumomin sun ce adadin mutanen 20 ne.

An saki mutum shida a farkon makon nan a wani samame da jami'an tsaro suka kai wa 'yan bindigar.

Kama mutane domin neman kuɗin fansa ba sabon abu ba ne a Najeriya, lamarin da ya zama ɗaya daga cikin manyan ƙalubalen tsaro a ƙasar a 'yan shekarun baya-bayan nan.

BBC Hausa 


Dan Takarar Shugaban Kasa na ADC ya kamu da cutar Corona

Dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar ADC, Dumebi Kachikwu, ya kamu da Coronavirus bayan sakamakon gwaji ya tabbatar yana dauke da kwayoyin cutar.

Mista Kachikwu ya bayyana hakan ne cikin wani sako da ya fitar a ranar Asabar, yana mai gargadin ’yan Najeriya da su yi taka tsan-tsan don annobar na iya dawowa.


Ya bayyana cewa tuni ya killace kansa kuma ya daina halartar tarukan jama’a da duk wasu harkalloli da suka danganci cudanya da al’umma.

Dan takarar ya ja hankalin ’yan Najeriya a kan kada su kuskura su yi wa cutar Coronavirus rikon sakainar kashi.


Ya ce a halin yanzu alkaluman masu kamuwa da cutar na ci gaba da karuwa cikin makonnin baya–bayan nan ko’ina a fadin duniya.

“Bai kamata ’yan Najeriya su yi kasa a gwiwa ba duk da cewa gwamnati ta sassauta dokokin COVID-19.

“Tsare-tsare da kuma tanadin da gwamnati ta yi a fannin kiwon lafiyarmu ba zai haifar da da mai ido ba a yayin da wannan annoba ke neman sake barkewa musamman a daidai lokacin da kwararrun masu kula da harkokin kiwon lafiyar ke tururuwar barin kasar.

“Dole ne mu kara kaimi wajen yi wa al’umma gwaje-gwaje da daukar duk matakan da suka dace don dakile yaduwar cutar.


“Kada mu zuba ido yawon yakin neman zabe da sauran tarukan siyasa su zama silar yaduwar COVID-19.

“Kar mu bari siyasa ta mayar mana da hannun agogo baya a nasarorin da aka samu wajen yakar cutar.

“Za mu tsira daga cutar Coronavirus idan kowannenmu zai kasance mai lura da sa ido sosai,” in ji Kachikwu.


NDLEA ta kama miyagun ƙwayoyi na kusan naira biliyan biyar

Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Najeroiya NDLEA ta ce ta kama wasu miyagun ƙwayoyi da kuɗinsu ya kai naira biliyan biyar a wani gidan ajiye kayyaki.

A wata sanarwa da hukumar ta wallafa a shafinta na Tuwita, ta ce ta gano tan bakwai na tabar wiwi a jihohin Legas da Borno da Edo da Enugu da Katsina da kuma birnin tarayya Abuja.

Hukumar ta ce daga cikin miyagun ƙwayoyin da ta gano sun haɗar da ƙwayar tramadol da yawanta ya kai 3,264,630, da kwalaben kodin 3,490 da wasu ƙwayoyin.

Yayin da yake yaba wa jami'an na NDLEA bisa wannan namijin ƙoƙari, shugaban hukumar Janar Buba Marwa mai ritaya ya yi kira a gare su da su ƙara tsage dantse domin kawo raguwar ta'ammali da miyagun ƙwayoyi a ƙasar.

Saturday, 14 January 2023

LABARI DA DUMIDUMINSA : Gobara ta tashi a Hedikwatar 'yan sanda ta Kano

Hedkwatar ‘yan sandan Kano da ke Bompai a karamar hukumar Nasarawa, tana cin wuta, inda ake zargin ta kona ofisoshi da muhimman bayanai da dama.

 Hukumar kashe gobara ta jihar ta ce tuni ta tura jami’an ta wurin da lamarin ya faru domin dakile gobarar da ta tashi a ginin bene mai hawa daya na rundunar.

 Rahotanni da basu tabbata ba sun nuna cewa gobara ta tashi ne a saman benen, Inda ta kama ko’ina amma banda ofishin kwamishinan ‘yan sandan jihar, Mamman Dauda.


Ko da Majiyarmu ta tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ta wayar hannu, mun sami wayarsa a kashe har lokacin haɗa wannan rahoton, amma har yanzu ba a san musabbabin tashin gobarar ba.

A Watan Maris Za A Fara Hako Man Fetur A Jihar Nasarawa – NNPC

Kamfanin Mai na Najeriya (NNPC) ya ce a watan Maris Mai zuwa zai fara aikin hako danyen man fetur a karo na farko a Jihar Nasarawa.

Shugaban kamfanin, Mele Kyari ne ya bayyana hakan ranar Juma’a, lokacin da ya karbi Gwamnan Jihar, Injiniya Abdullahi Sule da kuma wata tawaga daga Jihar a ofishinsa.

Gano man a rijiyar Keana ta Yamma da ke Jihar ta Nasarawa na zuwa ne kasa da wata biyar bayan kamfanin ya fara hakar wani a rijiyar Kolmani da ke tsakanin Jihohin Bauchi da Gombe.


A cikin sabuwar sanarwar da ya fitar ranar Juma’a, NNPC ya ce, “A ci gaba da aikinsa na gano man fetur a yankunan tsandauri na Najeriya, kamfanin zai fara aikin hako mai a rijiya ta farko a Jihar Nasarawa a watan Maris na 2023.”


Jaridar Aminiya ta ruwaito} Mele Kyari ya ce sakamakon binciken da suka gudanar ya tabbatar da akwai man fetur din dankare a yankin.

Daga nan sai ya bukaci a gaggauta fara aikin saboda ya ce sannu a hankali duniya ta fara dawowa daga rakiyar man fetur zuwa makamashin da ba ya lalata muhalli.

“Dole a gaggauta fara aikin nan saboda komai yanzu na sauyawa a duniya. Nan da shekara 10 ba lallai ne kowa ya yarda ya zuba jarinsa a harkar man ba matukar ba ya san zai ci riba ba. Saboda haka idan muka fara da wuri, ina ganin zai fi,” in ji Mele Kyari.


Kada Ku Nemi Na Saki 'Yan Daba - Muhuyi Magaji Ya Gargadi 'Yan Siyasa

Presidential delegation pays condolence visit to Hamza Darma’s family in Kano

A high-powered presidential delegation has paid a condolence visit to the family of late Alhaji Hamza Usman Darma, a prominent K...