Shugaban Tinubu ya amince da tsarin Biyan Tiriliyan 3.3 Domin Mayar Da Ingantacciyar Wutar Lantarki

Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya amince da tsarin biyan kuɗaɗe domin kammala biyan bashin da ake bin bangaren wutar lantarki a ƙarƙashin Shirin Gyaran Harkokin Kuɗi na Fannin Wutar Lantarki na Ƙasa.

A sanarwar da mai bawa Shugaban kasa Shawara kan yada labarai da dabaru, Bayo Onanuga ya fitar, yace wannan tsarin biyan bashin ya biyo bayan cikakken nazari na ƙarshe kan tsofaffin basussuka da suka addabi bangaren wutar lantarki fiye da shekaru goma.

Basussukan sun taru ne tsakanin watan Fabrairu na shekarar 2015 zuwa Maris na shekarar 2025.

 Bayan tantancewa, an amince da jimillar Naira tiriliyan 3.3 a matsayin cikakken biyan bashin, domin tabbatar da adalci da gaskiya wajen warware matsalar.

An fara aiwatar da shirin, inda tashoshin samar da wutar lantarki guda 15 suka rattaba hannu kan yarjejeniyar karɓar biyan bashin da ya kai Naira tiriliyan 2.3. Gwamnatin Tarayya ta riga ta samar da Naira biliyan 501 domin fara biyan kuɗaɗen. Daga cikin wannan adadi, an riga an fitar da Naira biliyan 223, yayin da ake ci gaba da sauran biyan kuɗaɗen.

Abin da wannan ke nufi ga ‘yan Najeriya: Yayin da kuɗaɗe ke isa ga dukkan sassan samar da wutar lantarki, samar da wuta zai fi karko. Da zarar an tallafa wa tashoshin wutar lantarki, ingancin wuta zai inganta.

Haka kuma, yayin da bangaren ke farfaɗowa, za a samu karin zuba jari, karin ayyukan yi, da ingantattun ayyuka.

Olu Arowolo-Verheijen, Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkokin Makamashi, ta ce:
“Wannan shiri ba wai kawai biyan tsofaffin basussuka ba ne.

 Manufarsa ita ce dawo da amincewa a bangaren wutar lantarki — tabbatar da cewa masu samar da iskar gas suna samun kuɗinsu, tashoshin wuta na ci gaba da aiki, kuma tsarin ya fara zama abin dogaro.”

“Wannan yana daga cikin manyan gyare-gyaren da ake aiwatarwa  ciki har da inganta tsarin mita (metering) da kuma tsarin farashin sabis wanda ke da alaƙa da ingancin wutar da kake samu da abin da kake biya.”

“Gwamnati na kuma bai wa harkokin kasuwanci, masana’antu, da kananan sana’o’i fifiko wajen samar da wuta  domin ingantacciyar wuta na da matuƙar muhimmanci wajen samar da ayyukan yi, tallafa wa rayuwar jama’a, da bunƙasa tattalin arziki.”

“Manufar ita ce mai sauƙi: ingantacciyar wuta ga gidaje, karin tallafi ga ‘yan kasuwa, da tsarin da zai yi aiki yadda ya kamata ga kowa da kowa,” in ji ta.

Shugaba Bola Tinubu ya yaba wa dukkan masu ruwa da tsaki da suka taimaka wajen warware matsalolin da suka dade suna addabar bangaren wutar lantarki. Haka kuma ya tabbatar da cewa mataki na gaba (Series II) zai fara a wannan zangon.

Popular posts from this blog

Yanzu - Yanzu: Bankuna Zasu Karbi Tsofaffin Kudi Ko da Bayan Karewar Wa'adi - Emefiele

Zababben Gwamnan Kano Ya Kafa Kwamitin Karbar Mulki