Ƙungiyar ɗaliban makarantar FGC ta Kano sun kai ƙara gurin Tinubu bisa zargin yunƙurin wawashe filin makarantar
Kungiyar tsoffin daliban makarantar FGC ta Kano, mai suna FGCKOSA ta aike da ƙorafi ga shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu bisa abinda ta kira da wawashe katafaren filin makarantar.
Daily Nigerian Hausa ta gano cewa ma'aikatar ilimi ta ƙasa da haɗin gwiwar wani kamfani, Pluck Global Company Ltd. sun kulla yarjejeniyar yanka wa da yin gine-gine a filin, wanda a ke sa ran gobe Litinin za a ƙaddamar da aikin a harabar makarantar .
Takardar korafin ta samu saka hannu na haɗin gwiwa da shugaban ƙungiyar na duniya, Shoyinka Shodunke da kuma wasu shahararrun mambobin ta da su ka haɗa da Sheikh Bashir Umar Aliyu, shugaban majalisar ƙoli ta shari'a ta kasa da Sheikh Rabiu Ishyaku Rabiu, shugaban rukunin kamfanin IRS.
Sauran da su ka rattaba hannu a takardar korafin sun haɗa da Engr. Suleiman Adamu, Galadiman Kazure, Alhaji Nasser Ahmed Dan Darman Lokoja da kuma Abdul Samaad Rabiu, shugaban rukunin kamfanonin BUA.
An kuma aike kwafin ta ga shugaban majalisar dattawa, shugaban majalisar wakilai da ministan ilimi da ƙaramin ministan ilimi da hukumomin ICRC, EFCC da ICPC, ƙungiyar ta ce sam ba za ta saɓu ba bindiga a ruwa.
A cewar Shokunde, ƙungiyar ta samu labarin cewa ana kokarin handame filin wanda ya ƙunshi filayen wasanni da masallaci da sauran gine-gine masu muhimmanci a makarantar.
Ya kara da cewa ana shirin karbe filin makarantar ba tare da wata tuntuba ba, inda ya ce kamata ya yi ma a karawa FGC din girma na wai a rika rage ta na.
A cewar sa, FGCKOSA ta shafe sama da shekaru 30 tana kashe biliyoyin naira wajen cigaban makarantar ba tare da sa ran samun wata riba ta kuɗi ba.
"Har wata gidauniya muka bude mai suna FGCKOSA Foundation ba dan komai ba sai dan mu taimaka wajen cigaban FGC.
" A yanzu haka muna shirin sake tara biliyoyin naira domin mun cigaba da dorar da kokarin cigaban FGC, amma sai gashi mun samu wani mummunan labari.
"To ba za mu yarda da wannan ba. Za mu yi duk me yuwuwa mu dakile wannan yunkuri," in ji Shokunde.
A karon gayyatar zuwa bikin ƙaddamar da aikin a filin da Daily Nigerian Hausa ta samu kwafi, Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ne babban bako a taron, sai kuma Kwamishinan Ƙasa, Abduljabbar Garko a matsayin babban mai jawabi sai kuma dattijon jam'iyyar APC na ƙasa, Mohammed Jamu Yusuf a matsayin mai jawabi ma biyu.