Mun himmatu wajen kare rayuka da dukiyoyin al’ummar Kano – Gwamna Abba Kabir Yusuf

Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya bayyana kudurinsa na kare rayuka da dukiyoyin al’ummar jihar.

Gwamna Yusuf ya bayyana haka ne a lokacin da ya karbi bakuncin shugabannin tsaron Kano a wani taron buda baki a gidan gwamnati da ke Kano.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar a ranar Litinin.

A cikin sanarwar, gwamnan ya yabawa jami’an tsaro bisa rawar da suke takawa wajen tabbatar da tsaro da walwalar ‘yan kasa, tare da sanin irin gudunmawar da suke bayarwa.

Gwamna Yusuf ya nanata jajircewar gwamnatin sa wajen karfafa tsarin tsaro domin isar da muhimman ayyukan da gwamnati da al’ummar Kano ke sa ran yadda ya kamata.

Ya kuma bayyana cewa gwamnatin sa ta fara siyan kayan abinci domin rabawa, inda jami’an tsaro na cikin wadanda suka ci gajiyar shirin.

Bugu da kari, ya yabawa gwamnatin tarayya musamman shugaban kasa Ahmed Bola Tinubu bisa amincewa da rabon kayan abinci da za a raba ga marasa galihu a fadin jihar nan gaba kadan.

Da yake amfani da wannan dama, gwamnan ya ja hankalin mahalarta taron da su ci gaba da rokon Allah Madaukakin Sarki da yin addu’o’i ba tare da katsewa ba domin samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar Kano da ma fadin Nijeriya a wannan wata mai alfarma na Ramadan.

Jami’an tsaro da dama da suka hada da Kwamishinan ‘yan sanda Muhammad Hussaini Gumel da Birgediya Janar M.A Sadiq na Birgediya 3 na Sojojin Najeriya da ke Barikin Bukavu da Kwamandan J.K Adedeji na Kwalejin Kula da Kayayyakin Sojoji da ke Dawakin Tofa sun bayyana jin dadinsu da wannan tallafin. Gwamnatin jihar Kano ta baiwa hukumomin tsaro.

Sun kuma jaddada aniyarsu ta tabbatar da tsaro a jihar Kano, inda suka bayyana taron buda baki a matsayin dandalin tattaunawa kan muhimman batutuwan da suka shafi inganta ayyukan hukumomin tsaro a Kano.


Popular posts from this blog

Yanzu - Yanzu: Bankuna Zasu Karbi Tsofaffin Kudi Ko da Bayan Karewar Wa'adi - Emefiele

Zababben Gwamnan Kano Ya Kafa Kwamitin Karbar Mulki