Hukumar Alhazai Ta Kano Ta Bukaci NAHCON Ta Kara Wa'adin Biyan Kudin Kujerar Hajji

Darakta Janar na Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kano, Alhaji Laminu Rabi’u Danbappa, ya bukaci Hukumar Alhazai ta kasa (NAHCON) ta yi la’akari da tsawaita wa’adin biyan kudaden hajji da akalla makonni biyu.

A sanarwar da Jami'in hulda da jama'a na hukumar, Sulaiman Abdullahi Dederi ya sanyawa hannu, yace Wannan roko na zuwa ne a daidai lokacin da jama'a ke neman cin gajiyar shirin tallafin da gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusif ta bullo da shi.

Tallafin wanda ya kai Naira dubu dari biyar (₦500,000) ga kowane mahajjaci da ya yi rajista, ya haifar da kishi sosai a tsakanin masu son zuwa aikin hajji. Tare da rage ma’auni a yanzu ya kai naira 1.418,032.91 ga wadanda suka fara biya naira 4.699,000, da kuma naira 1.617,032.91 ga wadanda suka biya naira miliyan 4.5, da dama sun kosa su yi amfani da wannan damar.

Alhaji Laminu Rabi’u ya jaddada bukatar tsawaita wa’adin, inda ya bayar da misali da yadda aka mayar da martani da kuma sarkakiyar aiwatar da gyare-gyaren tallafin a cikin wa’adin da aka kayyade.

 Ya nanata cewa damar kwana hudu da ake da ita na biyan cikon na aikin hajji ya yi kasa wajen karbar yawan tambayoyi da hada-hadar kasuwanci da ke zuwa cikin sashen.

Bugu da kari, Alhaji Laminu Rabi’u ya jaddada muhimmancin yin taka-tsan-tsan da rubuce-rubucen da ma’aikatan sashen ajiye bayanai ke yi don tabbatar da gaskiya da inganci a tsarin bayar da tallafin.

A yayin da bukatar tallafin da Gwamna Abba Kabir ke karuwa, Hajji  ke ci gaba , hukumar jin dadin alhazai ta jihar Kano ta jajirce wajen ganin maniyyatan sun amfana cikin sauki ga wadanda suka cancanta.



      
       

Popular posts from this blog

Yanzu - Yanzu: Bankuna Zasu Karbi Tsofaffin Kudi Ko da Bayan Karewar Wa'adi - Emefiele

Zababben Gwamnan Kano Ya Kafa Kwamitin Karbar Mulki