Shugaba Bola Tinubu Ya Bayar Da Umarnin Bude Iyakokin Najeriya Da Nijar Ta Kasa Da Sama Tare Da Dage Sauran Takunkumi

Shugaba Bola Tinubu ya bayar da umarnin bude iyakokin Najeriya ta kasa da ta sama da Jamhuriyar Nijar tare da dage wasu takunkumin da aka kakabawa kasar nan take.

A sanarwar da mai taimakawa Shugaban kasar kan harkokin yada labarai, Chief Ajuri Ngelale, yace wannan umarnin ya yi daidai da shawarar da kungiyar ta ECOWAS ta yanke a babban taronta na musamman da ta yi a ranar 24 ga Fabrairu, 2024, a Abuja.

Shugabannin ECOWAS sun amince da dage takunkumin karya tattalin arziki da suka kakabawa Jamhuriyar Nijar, Mali, Burkina Faso, da Guinea.

Shugaban ya bayar da umarnin a dage takunkumin da aka kakaba wa Jamhuriyar Nijar nan take:

(1) Rufe iyakokin kasa da ta sama tsakanin Najeriya da Jamhuriyar Nijar, da kuma hana zirga-zirgar jiragen sama na ECOWAS a duk jiragen kasuwanci da ke zuwa ko kuma daga Jamhuriyar Nijar.

(2) Dakatar da duk wani hada-hadar kasuwanci da hada-hadar kudi tsakanin Najeriya da Nijar, da kuma dakatar da duk wasu hada-hadar hidima da suka hada da ayyukan amfani da wutar lantarki zuwa Jamhuriyar Nijar.

(3) Daskarar da kadarorin Jamhuriyar Nijar a Babban Bankin ECOWAS da kuma daskarar da kadarorin Jamhuriyar Nijar, da kamfanonin gwamnati, da ma'aikatu a bankunan kasuwanci.

(4) Dakatar da Nijar daga duk wani tallafi na kudi da mu'amala da duk hukumomin kudi, musamman EBID da BOAD.

(5) Hana tafiye-tafiye ga jami'an gwamnati da 'yan uwansu.

Shugaba Tinubu ya kuma amince da dage takunkumin kudi da tattalin arziki da aka kakabawa Jamhuriyar Guinea.




Popular posts from this blog

Yanzu - Yanzu: Bankuna Zasu Karbi Tsofaffin Kudi Ko da Bayan Karewar Wa'adi - Emefiele

Zababben Gwamnan Kano Ya Kafa Kwamitin Karbar Mulki