Matukin Adaidaita Sahu Dan Kano Da Ya Tsinci Kudi Ya Mayar, Ya Samu Tallafin Miliyan 250 Don Yin Karatu

A wani abin da ya yi kama da gasa, matashin nan mai tuka Adaidaita Sahu mai shekaru 23 a Kano, Auwalu Salisu, wanda ya tsinci kudin wani dan kasuwa dan kasar Chadi har naira Miliyan 15  da ya manta su a kekensa tun a 2023, an ba shi tallafin karatu na naira Miliyan 250 har zuwa matakin karatun digiri na uku 

KANO FOCUS ta ruwaito cewa, LEADERSHIP Media Group ta yi bikin karamar  Auwalu a ranar Talata a wajen taron shekara-shekara da kuma bikin karramawa a matsayin wanda ya lashe lambar yabo ta ‘Fitaccen matashin matashin shekarar 2023’, saboda nuna gaskiya da ya yi.

Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar Labour Party (LP), Peter Obi, wanda aka karrama shi a matsayin Gwarzon dan siyasar LEADERSHIP na shekarar 2023, shi ne ya fara ba Awwalu guraben karatu a Jami’ar Baze da ke Abuja har zuwa matakin digirin digirgir.


Bayan haka, gwamnan jihar Neja, kuma wanda ya lashe kyautar Gwarzon Gwamnan na LEADERSHIP, Mohammed Umar Bago, ya mayar da martani cikin raha yana mai cewa jam’iyyar Labour ba za ta iya zarce jam’iyyar APC mai mulki ba.

A sakamakon haka Bago ya sanar da kyautar N250m ga Awwalu don jin dadin aikinsa na gaskiya da kuma karfafawa sauran matasan Najeriya kwarin gwiwa don nuna halin kirki.

Ya ce Awwalu zai samu tallafin Naira miliyan 50 kowanne daga gare shi da kansa da kuma shugaban kasa Bola Tinubu da ministocinsa da kungiyar gwamnonin APC da kuma gwamnatin jihar Neja.


Bago ya kara da cewa zai bayyana daya daga cikin ayyukan tituna da yake gudanarwa a jihar Neja da sunan matukin babur din na Kano.

Popular posts from this blog

Yanzu - Yanzu: Bankuna Zasu Karbi Tsofaffin Kudi Ko da Bayan Karewar Wa'adi - Emefiele

Zababben Gwamnan Kano Ya Kafa Kwamitin Karbar Mulki