Gwamna Yusuf ya nuna rashin jin dadinsa da shirin ciyarwa na watan Ramadan
Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya bayyana rashin jin dadinsa kan shirin ciyarwa na watan Ramadan da ake yi a cikin babban birnin Kano.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar a ranar Juma’a.
Gwamnan ya ce ya ji takaicin shirin a lokacin da ya kai ziyarar bazata daya daga cikin cibiyoyin ciyar da abinci da ke Gidan Maza, karamar hukumar Municipal.
Gwamna Yusuf ya kuma nuna rashin jin dadinsa da yadda masu gudanar da shirin ke gudanar da ayyukansu, wadanda ya ke ganin suna hana wadanda suka ci gajiyar shirin.
“Ba za mu amince da rashin gaskiya da almubazzaranci da dukiyar al’umma ba, ya zama wajibi a lura da cewa kudaden da aka ware don wannan shiri an tsara su sosai a kowace cibiya” Gwamnan ya yi gargadin.
Gwamnan ya gudanar da ziyarar ne biyo bayan rahotannin sirri da ke nuna nakasu wajen gudanar da shirin ciyarwa a cibiyoyi daban-daban na babban birnin.