Labari Da Dumiduminsa: Gwamnatin Kano Ta Rage Kudin Kujerar Aikin Hajjin Bana

Sakamakon karin kudi har kimanin Naira miliyan daya da dubu dari tara (1,900,000) da Hukumar kula da aikin Hajji ta Najeriya ta yi akan kowacce kujerar aikin Hajji, Gwamnan ya sanar da cewa dukkanin maniyyatan jihar Kano Gwamnatin Kano ta musu ragin Naira dubu dari biyar (500,000) akan kowacce kujera.

Gwamnan ya sanar da hakan ne a shafinsa na Facebook a ranar Laraba

Gwamnan yace  ragin da aka samar a yanzu haka na nufin duk wani maniyyaci da ya biya Naira miliyan hudu da dubu dari bakwai (4,700,000) kudin babbar kujera da wadanda suka biya Naira miliyan hudu da dubu dari biyar (4,5000,000) kudin karamar kujera za su cika Naira miliyan daya da dubu dari hudu (1,400,000) ne kacal maimakon Naira miliyan daya da dubu dari tara (1,900,000) 

Popular posts from this blog

Yanzu - Yanzu: Bankuna Zasu Karbi Tsofaffin Kudi Ko da Bayan Karewar Wa'adi - Emefiele

Zababben Gwamnan Kano Ya Kafa Kwamitin Karbar Mulki