Search This Blog

Sunday, 4 February 2024

Rikicin ECOWAS Na Iya Illata Nijeriya — Masana

 Ficewar Nijar ya fi janyo damuwa musamman ga ’yan Nijeriya wadanda suke da al’adu da harshe da addini kusan daya.



Alamu na nuna cewa Nijeriya na iya tafka asara idan aka kwatanta da sauran kasashe 12 na Kungiyar Tattalin Arziki ta Kasashen Afirka ta Yamma (ECOWAS) ta fannin tsaro da tattalin arziki sakamakon ficewar kasashen Mali da Burkina Faso da Nijar daga kungiyar, kamar yadda wasu masana da wasu daga cikin al’ummomin da ke a kan iyakar kasar suka shaida wa Aminiya.

Sai dai wasu masana sun musanta cewa ficewar kasashen uku zai yi illa ga harkokin kasuwanci da tattalin arziki da zuba jari wanda hakan ka iya illata dokar kasuwanci ta Afirka (AfCFTA).

An samar da Dokar AfCFTA ce a matsayin wata hanya ta kasuwancin bai-daya a Afirka domin bunkasa ayyukan kasuwanci a nahiyar.

Idan ba a manta ba, sojojin da suka yi juyin mulki a kasashen uku, a ranar Lahadin makon jiya sun fitar da sanarwar ficewa daga Kungiyar ECOWAS.

Wannan ya biyo bayan takunkumin da kungiyar ta sa wa kasashen uku ne bayan hambarar da shugabannin dimokuradiya a kasashensu.

An dakatar da kasar Mali daga Kungiyar ECOWAS a shekarar 2021 bayan juyin mulki biyu da suka yi. Burkina Faso kuwa a shekarar 2022 ce aka dakatar da ita, sannan sai Nijar a shekarar 2023.

Duk da cewa dokar Kungiyar ECOWAS ta nuna dan kungiyar zai iya ficewa ce kawai bayan wa’adin shekara guda, amma wadanda suka tattauna da wakilanmu sun nuna al’amura ba sa daidaita masu ba tun a bara kuma suna ganin hukuncin da kasashen uku suka yanke zai kara ta’azzara lamarin ne maimakon saukaka musu.

Ba kamar abin da ya faro da Mali da Burkina Faso ba, dakatar da Nijar ya fi janyo damuwa musamman ga ’yan Nijeriya da kuma ’yan Nijar din wadanda suke da al’adu da harshe da addini kusan daya.

Iyakar Nijeriya da Nijar na da fadin kilomita 999, kuma ta shafi jihohin Sakkwato da Kebbi da Jigawa da Yobe da Borno.

Babu wata rata mai yawa da ya raba kasashen a jihohin bakwai wanda hakan ya sa kasashen ke cudanya da juna cikin sauki.

Baya ga wasu ’yan takardun da ake cikewa, al’ummomin kasashen biyu ba sa bukatar biza wajen tsallakawa kasashen domin gudanar da kasuwancinsu ko mu’amalarsu ta yau da kullum.

Amma da aka sanya wa Nijar takunkumi a shekarar 2023 tare da sanya musu ido sun ji a jikinsu domin kowa hakan ya sa an rufe dukkan iyakokin kasashen biyu.

Matakain dai ya janyo karancin kayan abinci da bukatun yau da kullum a yankunan kan iyakan. Kasar ta Nijar ta dogara ce matuka daga kayan abinci da na gine-gine daga Nijeriya.

Ita kuwa Nijeriya tana dogara ce daga dabbobin da ake shigowa da su daga Nijar da suka hada da rakuma da tumaki da awaki da kuma dabino da sauransu.

Juyin mulkin soja da aka yi a Nijar da kuma matakan da Kungiyar ECOWAS ta dauka wanda Nijeriya ke shugabanta ya shafi hadin gwiwa wajen yaki da ta’adanci da kasashen biyu ke yi a kan iyakokinsu a Arewaci da Kudancin kasashen kamar yadda jami’an tsaron da ke aiki a kan iyakar Tafkin Chadi suka tabbatar.

A watan Nuwamba 2023 Aminiya ta ruwaito irin gibin da aka samu sakamakon wannan takaddama a tsakanin kasashen biyu wanda hakan ya janyo karuwar hare-haren a Tafkin Chadi.

Wasu wurare a kan iyakokin kasashen biyu musamman ta yankin Gaidam a Yobe da Malam Fatori da Damasak a Jihar Borno suna fuskantar karuwar hare-haren ’yan ta’adda.

A cewar majiyoyinmu a Gaidam, kasar Nijar ta janye sojojinta daga iyakar kasar ta Gaidam wanda ya janyo karuwar hare-haren.

’Yan gudun hijirarmu na cikin kaka-ni-ka-yi — Gwamnatin Borno

Shugaban Kungiyar Dattawan Jihar Borno Dokta Bulama Mali Gubio ya ce idan aka yi la’akari da kawancen da ke tsakanin kasashen biyu, janyewar Nijar daga ECOWAS zai yi illa ga harkokin kasuwanci a Nijeriya da kuma ’yan gudun hijirar Nijeriya da ke Nijar.

“Muna magana ce a kan kasuwancin da ke gudanar a kan iyakokin kasashen biyu ba ’yan fasa kwauri ba.

“Yanzu mutanenmu dole sai sun nemi biza kafin tsallakawa cikin Nijar. Yanzu babu maganar shiga yadda aka ga dama da kayayyakin abinci,” in ji shi.

Ya yi kira ga ’yan Nijeriya da ke a kan iyakokin Nijar da su goyi bayan matakin da Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu zai dauka da kuma kungiyar ta ECOWAS wajen yin amfani da tattaunawa domin magance matsalar.

“Ko babu komai ’yan Arewa su yi abin da za su iya yi domin tabbatar da an kare kasancewarsu da aka kulla shekaru masu yawan gaske.

“Sarakunanmu da malamanmu da da tsofaffin shugabannin kasashen da kuma ’yan kasuwarmu duk sun yi kokarinsu wajen tabbatar da an samu zaman lafiya, amma sojojin sun ki ta hanyar ci gaba da rike mulki duk kuwa da talakawan ba sa so,” in ji shi.

Haka kuma wata majiyarmu a cikin jami’an tsaro a kan iyakar Abadam wanda gari ne da ke kan iyakar kasashen biyu inda dubban ’yan Nijeriya ke gudun hijira a Diffa, Nijar ta ce an fara samun masu komawa gida da yawa.

“’Yan gudun hijira ’yan Nijeriya da ke dawowa daga Diffa da wasu yankuna na Nijar akwai damuwa.

“Yawancin lokuta muna tura su ne zuwa sansanin ’yan gudun hijira da ke Monguno.

“Yanzu haka sansanin a cike yake makil wasu ba su da wurin kwanciya sannan babu isasshen abinci ga wadanda ke sansanin,” in ji majiyar.

Abdullahi Ibrahim wanda lauya ne kuma mai kare haƙƙin mutane a Maiduguri ya ce a yayin da Nijar ta dogara da Nijeriya a fannin tattalin arziki ita ma Nijeriya ta dogara da Nijar ta fannin yaki da ’yan ta’adda musamman Boko Haram.

“Mutane a Malam Fatori suna shiga Maine Soroa a Nijar domin neman magani. Suna kuma sayen kayan bukatun yau da kullum kamar ruwan sha da kayan abinci saboda ya fi sauki da su zo Maiduguri ko Mongono,” in ji shi.

Wani jami’in tsaro da ke aiki a Arewa maso Gabas wanda ba ya so a ambaci sunansa ya ce, “Muna bukatar goyon bayan Nijar domin kawar da ’yan ta’adda musamman a Abdam da Kukawa da Marte da Tunbus a yankin Tafkin Chadi,” in ji shi.

Ya ce, “ISWAP ana ganinsu a yankin Gashegar da Arkubma da Shilay inda suke tsayawa domin kai hare-harensu da kuma karbar haraji a wajen al’ummomin yankin.

“Ko a kwanakin nan ISWAP sun fito da motoci biyu da babura shida inda suka kwana a kauyen Late da safe suka dan yi zagaye a cikin garin a kusa da Kareto da Laye.

“Yawancin ’yan kungiyar ISWAP sun fito ne daga yankin Gaidam. Wannan yankin na karkashin Karamar Hukumar Mobbar ce,” in ji shi.

Matakin zai kara jefa mu cikin wahala — Mazauna Yankunan Katsina

Da suke bayani a kan lamarin da ke faruwa a kan iyakokin kasashen biyu, Shugaban Kungiyar Al’ummar Jibiya, Alhaji Hide Dahiru ya ce al’amuran kasuwanci suna cikin wani yanayi a yankin, inda ya ce ficewar kasahen uku za ta kara ta’azara lamarin a yankin.

“Akwai dokokin kan iyakokin kasashen da cike da shigi da fice domin gudanar da kasuwanci.

“Yanzu da wadannan kasashen suka fice daga ECOWAS hakan ya nuna ke nan wadannan dokoki ba za su yi amfani ba sababbi za a fito da su.

“Kamar yadda ka sani akwai kayayyaki irin su hatsi da dabino da ake samu daga Nijar da ba a biya musu haraji.

“Idan wannan mataki ya jima ya zama ke nan wadannan kayayyaki za a sanya su cikin wadanda ake safararsu ke nan,” in ji shi.

Wani masanin tsaro Muhammad Nasir Abdullahi ya ce akwai hadin gwiwa a tsakanin Nijar da Nijeriya wajen yaki da ta’adanci a kan iyakokin kasashen biyu, inda ya ce idan aka tsinke shi lamarin zai lalace.

Dangane da zamantakewa kuwa ya ce akwai mu’amala sosai a tsakanin mazauna iyakar kasashen biyu daga auratayya wanda kuma tsaurara matakan zai iya shafar wannan mu’amala ta iyalai.

Hadin kan kasashen na cikin barazana — Farfesa

A cewar Farfesa Tanko Baba masanin siyasa a Jam’iar Usman Dan Fodiyo da ke Sakkwato, matakin zai fi illa wa Nijeriya.

“Nijeriya ce a kan gaba wajen batun ECOWAS. Nijeriya ce ta fi yawan jama’a a cikin kasashen 15.

Kasuwancin Arewacin Nijeriya har cikin Nijar da Mali da Burkina Faso, ke nan kasuwancin da ke tsakanin wadannan kasashe uku zai lalace.

“Ina son ka sani cewa tattalin arzikin Nijeriya a fannin kasuwancin dabbobi kusan kaso 69 zuwa 79 na dabbobin da ke shigowa Nijeriya daga Nijar ne.

“Wasu ma ba daga Nijar kadai suke ba wasu daga Senegal ne a kullum. A yanzu ke nan za a samu nakasu a fannin.

“Bayan matsalar tsaro da muke fama da ita a yankin Arewa. A tarihi Nijeriya ba ta da makwabciya da ke biyayya gare ta kamar Nijar.

“Yanzu ke nan Nijeriya na iya fuskantar barazanar matsalar tsaro a yankin.

“Yanzu Nijar ta fice kuma ’yan ta’addar nan da barayin shanu duk suna da asali da irin wadannan kasashe irin su Mali da Burkina Faso da Nijar,” in ji shi.

Dokta Bashir wanda shi ma masanin tattalin arziki ne a Jami’ar Usman Dan Fodiyo ya ce kasuwanci a tsakanin Nijar da Mali na da girma.

“Idan ka je kan iyakar kasashen nan ka ga irin kasuwancin da ke faruwa a can za ka fahimci cewa mutane da yawa sun dogara da wadannan kasashe wajen kasuwancinsu, ficewar kasashe uku ba karamar matsala ba ce,” in ji shi.

Ya ce kuɗaɗen da ke shigowa a dalilin kasuwanci a tsakanin Nijar da Nijeriya ya kai Dalar Amurka biliyan daya a bara.

(AMINIYA)

An Sako Daliban Da Aka Yi Garkuwa Da Su Ekiti

An sako daliban da malaman nasu ne kimanin mako guda bayan an yi garkuwa da su 



Dalibai tara da malamansu da aka yi garkuwa da su a Jihar Ekiti sun kubuta daga hannun ’yan bindiga.

Da misalin karfe 2 na dare, kafin wayewar garin yau Lahadi ne masu garkuwa da su suka sako su.

Hukumomi a jihar sun tabbatar da sako daliban su tara tare da malamansu.

An sako daliban da malaman nasu ne kimanin mako guda bayan an yi garkuwa da su a makarantar Apostolic Faith Group of Schools da ke yankin Emure-Ekiti.

Kawo yanzu dai babu bayanin ko an biya kudin fansa.

An yi garkuwa da su ne a makarantar Apostolic Faith Group of Schools da ke yankin Emure-Ekiti.

(AMINIYA)

Saturday, 3 February 2024

INEC Ta Dakatar Da Sake Zabe A Enugu, Kano, Akwa Ibom Sakamakon Rikici, Sace Jami'an Zabe

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta dakatar da sake gudanar da zabukan da aka gudanar a wasu mazabu na jihohin Enugu, Kano, da Akwa Ibom, sakamakon tarzoma, da rashin bin ka’ida, da kuma sace jami’an zabe.

Yankunan da abin ya shafa sun hada da mazabar Enugu ta Kudu 1 a jihar Enugu, da kuma mazabar tarayya ta Ikono/Ini a jihar Akwa Ibom, da kuma mazabar Kunchi/Tsanyawa dake jihar Kano.

Wannan sanarwar ta fito ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Sam Olumekun, kwamishinan na kasa & shugaban kwamitin yada labarai da wayar da kan masu zabe, a ranar Asabar.

Dakatarwar ta biyo bayan rahotannin ‘yan daba da sace kayan zabe a wadannan jihohin. A mazabar Enugu ta Kudu 1, an dakatar da zabukan a dukkan runfunan zabe takwas da aka yi na farko

A mazabar Kunchi da Tsanyawa da ke jihar Kano, an dakatar da zabuka a dukkanin mazabu goma da ke karamar hukumar Kunchi sakamakon mamayewa da barna da kuma kawo cikas da ‘yan daba.

An yanke wannan hukuncin ne bisa ga sashe na 24(3) na dokar zabe ta 2022. INEC ta bayyana cewa za ta sanar da karin matakan da za ta dauka kan mazabar da abin ya shafa bayan wani taro a ranar Litinin da ta gabata, sannan ta gayyaci jami’an tsaro da su binciki lamarin. Hukumar ta kuma yi alkawarin yin nazari sosai kan duk wani sabani da ya shafi jami’anta.


Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC na gudanar da zabuka a kananan hukumomi 80 da ke fadin jihohi 26 domin cike gurbi a kananan hukumomi 3, da na tarayya 17 da kuma mazabu na jiha 28 da suka yi rajista 4,904,627, wadanda 4,613,291 suka karbi katin zabe na dindindin (PVCs).

(Leadership Newspaper)

Labari Da Dumiduminsa: NAHCON Ta Sanar Da Kudin Hajjin 2024

Idan dai za a iya tunawa da farko Shugaban Hukumar Alhazai ta Najeriya (NAHCON), Malam Jalal Ahmad Arabi ya yi niyyar barin kudin aikin Hajjin 2024 a kan Naira miliyan 4.5 da aka karba a matsayin kudin ajiya tun farko. 

A sanarwar da mataimakiyar daraktar harkokin hulda da da dab'i ta hukumar, Fatima Sanda Usara ta sanyawa hannu, taceHasashen ya kasance mai girma har sai da batun kara karyewar darajar Naira ya faru a tsakiyar mako. Abin takaici, rashin tsayawa da aka samu a farashin Dala a baya-bayan nan ya tilasta yin gyare-gyaren da ya dace duk da kokarin da Shugaban Hukumar NAHCON, Jalal Ahmad Arabi ya yi na kula da farashin aikin Hajjin bana a kan wannan adadin.
 
A karshen watan Janairu ne shugaban Arabi ya tattauna kan samun rangwame mai yawa tare da masu ba da ayyukan Alhazai a masarautar Saudiyya, tare da kokarin rage farashin maniyyata aikin hajji. Sai dai kuma halin da ake ciki na tabarbarewar kudi a cikin satin, ya sa hukumar ta dauki tsattsauran mataki na karfafa nasarorin da aka samu wajen rage farashin hidimar aikin Hajji, wanda idan ba tare da haka ba farashin aikin hajjin na shekarar 2024 zai iya zuwa kusan  Naira miliyan shida
 
Don haka, ana bukatar maniyyatan da suka fito daga yankin Kudancin Najeriya su biya N4,899,000 a matsayin kudin aikin Hajji; wadanda suka fito daga tsakiyar Arewa za su biya Naira miliyan 4,699,000, na aikin Hajji, kuma mahajjata daga Yola da Maiduguri za su biya Naira miliyan 4,679,000 na aikin Hajjin 2024.
 
Da yake bayyana nadamarsa, Shugaban Hukumar Arabi ya bayyana cewa, wannan nufin Allah ne, domin Hukumar, tana fuskantar tsaikon wa’adin ranar 25 ga watan Fabrairu, ta tanadi wasu zabukan da za su ci gaba da kasancewa a cikin iyakar Naira miliyan 4.5 da ya yi aiki da su. Don haka, NAHCON ta bayyana kudin da za a iya yi na aikin Hajji don cika wa’adin lokacin da ke tafe.
 
Don haka an shawarci maniyyatan da su cika ragowar kudinsu nan da zuwa ranar Litinin 12 ga watan Fabrairu don baiwa hukumar damar mika kudaden kafin cikar wa’adin.
 
Hukumar NAHCON tana tabbatar lwa al’umma kudurinta na ganin an gudanar da aikin hajji cikin nasara da duk da kalubalen da ke tattare da canjin kudaden kasashen waje. Hukumar ta yaba da fahimta da hadin kan al’ummar Musulmin Najeriya a wadannan lokuta.
 

Wednesday, 24 January 2024

Har Yanzu 29 Ga Watan Afurilu Ce Ranar Karshe Ta Rufe Yin Bizar Hajin 2024 - Laminu Rabi'u Danbaffa

Darakta Janar na Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kano, Alhaji Laminu Rabi’u Danbappa ne ya bayyana hakan a yau yayin liyafar cin nasara a kotun koli da jami’an hukumar alhazai 44 suka shirya cewa masarautar Saudiyya ta tsaya tsayin daka kan dokokin aikin Hajji na shekarar 2024. 

A sanarwar da Jami'in hulda da jama'a na hukumar, Sulaiman Abdullahi Dederi ya sanyawa hannu, yace Alhaji Laminu Rabi’u Danbappa ya bukaci jami’an cibiyar Hajji da su rika fadakar da al’umma wannan wa’adin don tabbatar da cewa ba a bar wani mahajjaci a baya ba.

Da yake jawabi kan liyafar da aka karrama Gwamna Alhaji Abba Kabir Yusif, Alhaji Laminu Rabi’u Danbappa ya bayyana cewa, wannan shi ne mataki na farko, kuma ana sa ran za a samu ci gaba.

 Ya kuma roki Allah Madaukakin Sarki da Ya yi wa Gwamna Alhaji Abba Kabir Yusif jagora ya kuma kare shi a dukkan al’amuransa.

A nasa jawabin shugaban kungiyar Jami'an Alhazai na kananan hukumomi na Jahar Kano wanda kuma ya kasance jami’in Alhazai na karamar hukumar Bichi, Alhaji Habibu Idris Bichi ya bayyana cewa sun shirya liyafar ne domin karrama gwamna Alhaji Abba Kabir Yusif bisa nasarar da ya samu a kotun koli a kwanakin baya, ta hanyar kokarin da aka yi. na Babban Daraktan Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kano, Alhaji Laminu Rabi’u Danbappa.

Alhaji Habibu Idris Bichi, a madadin daukacin jami’an hukumar alhazai na kananan hukumomi 44, ya yi alkawarin yin kokari wajen sayar da kujerun aikin Hajji domin cimma burin da aka sa gaba.



            

Sunday, 21 January 2024

Dalilin Da Dokar Hana Lefe Ba Za Ta Yi Aiki Ba A Kano

Shi kansa mai laifi ne, domin ya yi lefe a nasa auren da na ’yan uwansa.

 Masani a bangaren Shari’a Barista Isa Umar Sulaiman, ya bayyana cewa duk da cewa akwai Dokar Hana Lefe a Kundin Dokokin Jihar Kano, hakan ba zai sa ta yi aiki ba saboda tana kunshe da wasu sharuɗa.

Barista Sulaiman ya faɗi haka ne yayin da yake mayar da martani ga fitaccen lauyan nan da ya yi shuhura a kafafen sada zumunta, Barista Abba Hikima.



A cewar Barista Sulaiman, neman tayar da kura ko kawo hargitsi ya sanya Barista Hikima ya dago da batun dokar hana lefe a jihar ta Kano.

A makon da muke ciki ne dai cikin wani shiri na gidan rediyo a Jihar Kano da kuma shafinsa na Facebook, Abba Hikiman ya dauko batun cewa a Dokar Kano laifi ne ka yi lefe kamar yadda ake yi a yanzu.

Wannan magana dai ta ta da kura musamman a soshiyal midiya, inda wasu ke ganin bakinsa wasu kuma ke sam barka.

Sai dai Lauya Sulaiman ya ce Hikima tsakuro sashi na 5 na dokar ya yi, ba wai gaba ɗaya dokar kacokan ya fassara ba.

“Saɗarar da ya ke magana a kai ita ce ta 3 a sashi na 5 na dokar.

“Doka ce da aka yi ta tun zamanin mulkin soja a shekarar 1988 wacce aka sanya wa ‘Dokar Aure da kuma sanya ido a kan abubuwan da suka shafi al’adun auren’. Amma fa mutane ba za su fahimci dokar ba sai an dauko gundarinta,” in ji shi.

Barista Sulaiman ya ce sashin da aka tsakuro batun lefen, ya zayyano al’adun aure 19 da suka haɗa da Gara, Zaman Ajo da Gaisuwar Iyaye sai Lefe, wanda shi ne ya zo a na 3 a lissafin.

“Bayan sashi na 4 da ya yi bayani kan haramcin auren dole, da sashi na 3 da ya yi na sadaki, akwai muhimmin sashi wato na 7 da ya yi bayanin sakin auren da za a iya kome da na rabuwa.”

“Daga saki ɗaya zuwa na biyu, dokar ta ce mace za ta ci gaba da zama gidan mijinta ne ya ci gaba da kula da ita kamar yadda yake yi kafin sakin.

“Shi kuma saki 3 za ta koma gidan iyayenta, amma zai ci gaba da daukar nauyin ’ya’yan da suka haifa.

“Haka kuma sashi na 9 na kundin dokar ya yi bayanin cewa kotun sasanta ma’aurata ce ke da hurumin hukunta duk wanda ya saba wa dokar, wacce a halin yanzu kwata-kwata babu ita.”

Barista Sulaiman ya kuma yi karin haske kan kotun, da kuma hukuncin da dokar ta tanada ga duka wanda ya saba mata.

“Kotu ce da ta haɗa masanin addinin Musulunci da zai jagorance ta, sai babban limamin masallacin Juma’a, sai Magatakardar yankin, sai mutane biyu da ke aiki a Ma’aikatar Walwalar Jama’a, da ta Matasa da Wasanni, sai kuma wakilan bangarorin 2, da Mai unguwa, sai kuma wani malamin ko Limamin gari baki ɗaya.

“Abun tambayar shi ne yanzu akwai irin wadannan kotunan yanzu? Babu a Kano. Haka kuma akwai batun yin rajistar duk auren da aka yi a wuraren da aka ware don yin hakan, wanda shi ma babu yanzu.”

Sulaiman ya ce don haka a nasa ra’ayin neman suna ne da kuma son ta da kura ya sanya Abba Hikima tsakuro doka ya yi bayanin wani bangare nata ya kyale sauran sassan da suka fi bangarori masu muhimmanci.

Ya kuma ce idan har za a yi amfani da ita, shi kansa mai laifi ne, domin ya yi lefe a nasa auren da na ’yan uwansa.

“Dukkanmu lauyoyi ne, kuma mun san cewa akwai dokokin da suna nan a rubuce, amma barci suke yi saboda ba a yin aiki da su ko ba zai yiwu a yi aiki da su ba.

“Misali ko tarar da aka tanada ga wanda ya karya dokar Naira 200 ne ko daurin watanni 2,” in ji shi.

(AMINIYA)


An Sako Kannen Nabeehah Da Ke Hannun ’Yan Bindiga

 Da misalin kare 12:30 na daren Asabar ne kannen na Nabeeh suka isa gidansu da ke Abuja, da rakiyar jami'an tsaro.



Masu garkuwa da mutane sun sako ’yan uwan marigayiya Nabeeha Al-Kadriyah hudu da suka sace a Abuja bayan sun shafe kwanaki 19 a hannunsu.

Da misalin kare 12:30 na daren Asabar ne kannen na Nabeeh suka isa gidansu da ke Abuja, da rakiyar jami’an tsaro.

Kawunsu  Sherifdeen, ya shaida wa wakilinmu ta wayar tarho da safiyar Lahadi, “An sako ’yan matan ne da yammacin ranar Asabar kuma tuni sun nufi gida”.

Su hudun su ne Najeeba ’ya aji 500 a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya da kanwartar da ke aji 300 a jami’ar Nadherah, tare da tagwayen kannensu, Habeeba da Haneesa.

Dawowarsu bayan sun shafe kwanaki 19 a hannunsu ’yan bindigar da suka sace su a ranar 2 ga Janairu, 2024 ta sanya murna tskanin al’ummar unguwar.

Sanarwar da Sherifdeen ya sanya wa hannu ta ce, “farin cikinmu game da dawowarsu ba zai misaltu ba, muna godi ga Allah da al’umma da suka ba mu gudunmawa.

“Muna addu’ar samun rahama ga wadanda suka rasu, Allah ya kawo dauki ga iyalan wadanda ke hannun masu garkuwa, ya kubutar da su.”

An yi garkuwa da ’yan matan su biyar ne tare da mahaifinsu, wanda daga bisani masu garkuwar suka sako shi cewa ya kowa kudin fansarsu Naira miliyan 60 cikin kwana uku.

Rashin samun kudaden ya sa suka kashe Najeeba, ’yar aji 500 a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, suka kuma kara kudin fansan zuwa miliyan 100, gami da baranar kashe ragowar idan ba a kawo kudin cikin lokacin da suka kayyade ba.

Duk da cewa an biya kudin fansa Naira miliyan 100, masu garku wa da su sun ci gaba da tsare su na tsawon kwanaki, lamarin da ya sanya iyalan cikin zullumi har zuwa daren Asabar.

(AMINIYA)

Saturday, 20 January 2024

Darakta Janar Na Hukumar Alhazan Kano Ya Dawo Najeriya Bayan Ziyarar Aiki Da Ya Kai Saudia

A yau ne Darakta Janar na Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kano, Alhaji Laminu Rabi’u Danbappa ya dawo daga kasar Saudiyya tare da tawagar magoya bayansa.

A sanarwar da Jami'in hulda da jama'a na hukumar, Sulaiman Abdullahi Dederi ya sanyawa hannu, yace da yake jawabi ga mazauna unguwar Galadanci da ke karamar hukumar Gwale da jami’an hukumar alhazai na kananan hukumomi 44, Alhaji Laminu Rabi’u ya bayyana abubuwan da ya sa a gaba a tafiyar.
 Ya mayar da hankali ne kan inganta masaukan alhazai da ciyar dasu, da sufuri ga alhazai a yayin aikin Hajjin 2024 mai zuwa.

A yayin jawabin, Alhaji Laminu Danbappa ya yi amfani da damar wajen taya Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusif murnar nasarar da ya samu a kotun koli a kwanakin baya.
Ya bukaci daukacin ma’aikatan hukumar da su ba da hadin kan da ya dace domin cimma burin da aka sanya a gaba. 

Alhaji Laminu Rabi'u ya yi alkawarin yin aiki tare da dukkan ma'aikata domin cimma manufofin da aka sanya a gaba 

Ya Kuma nuna jin dadinsa, ya yabawa Gwamna Alhaji Abba Kabir Yusif bisa yadda yake ba hukumar damammaki a kai a kai.




Friday, 19 January 2024

Kotun Koli Ta Tabbatar Da Gwamna Abdullahi Sule A Matsayin Gwamnan Jahar Nassarawa

Kotun Koli ta yi watsi da karar da dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP, David Umbugadu, ya shigar kan zaben Gwamna Abdullahi Sule na Jihar Nasarawa.

Kotun ta kori karar kan rashin cancanta, amma ba ta ci tarar dan takarar na jam’iyyar PDP ba.



Cikakken bayani na tafe…


Barrister Muhuyi Ya Ziyarci Kwamishinan Shari'a, Inda Ya Nemi Yin Gyara A Dokokin Da Suka Kafa Hukumar Da Yake Jagoranta

Shugaban Hukumar Korafe-korafe da Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Kano, Barista Muhuyi Magaji Rimingado ya kai ziyarar aiki ga Kwamishinan Shari’a na Jihar Kano, Barista Haruna Isa Dederi, a wani gagarumin ci gaba da aka gudanar da nufin karfafa yaki da cin hanci da rashawa.


A cewar wata sanarwa da jami’in yada labarai na ma’aikatar shari’a ta jihar Kano, Musbahu Aminu Yakasai ya fitar, a yayin ziyarar a ranar Alhamis, Rimingado ya tattauna da kwamishinan domin neman goyon bayan gyara dokar hukumar.

An tsara gyare-gyaren da ake shirin yi don inganta ingantaccen aiki da ingancin hukumar wajen magance cin hanci da rashawa, inganta gaskiya da kuma tabbatar da bin doka da oda a cikin jihar.

Da yake yaba da muhimmiyar rawar da tsare-tsare na shari’a ke takawa wajen yaki da cin hanci da rashawa, Muhuyi Magaji ya nuna jin dadinsa da samun damar hada kai da ma’aikatar.

Ya tabbatar da kudurinsa na samar da ingantaccen yanayi na shari’a wanda ke baiwa hukumar yaki da cin hanci da rashawa damar tunkarar kalubalen da ke kunno kai tare da kiyaye ka’idojin adalci a jihar.


Shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ya nuna godiya ga kwamishinan Dederi bisa yadda ya amince da shi kuma yana fatan ci gaba da hadin gwiwa wajen neman al’ummar da ba ta da cin hanci da rashawa.

A nasa bangaren kwamishinan shari’a Barista Haruna Isa Dederi ya yi maraba da shirin, inda ya jaddada muhimmancin samar da cikakken tsarin doka a yaki da cin hanci da rashawa.

Ya yi alkawarin tallafa wa ma’aikatar wajen samar da gyare-gyaren doka da suka dace da kuma yin aiki tare da Hukumar Korafe-korafen Jama’a da Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Jiha don karfafa aikinta.



Ya ce gyare-gyaren da ake sa ran za su kasance wani muhimmin mataki na ciyar da kwarjinin hukumar gaba da kuma tabbatar da cewa ta kasance mai karfin gaske wajen kare dukiyar al’umma da kuma kiyaye mutuncin cibiyoyin gwamnati.
(Justice watch)

Kada Ku Nemi Na Saki 'Yan Daba - Muhuyi Magaji Ya Gargadi 'Yan Siyasa

Tinubu Commissions Section III of Abuja–Kaduna–Zaria–Kano Expressway, Boosts Road Safety and Trade

President Bola Ahmed Tinubu has commissioned Section III of the Abuja–Kaduna–Zaria–Kano Expressway, covering the Zaria–Kano corr...