Dalilin Da Dokar Hana Lefe Ba Za Ta Yi Aiki Ba A Kano
Masani a bangaren Shari’a Barista Isa Umar Sulaiman, ya bayyana cewa duk da cewa akwai Dokar Hana Lefe a Kundin Dokokin Jihar Kano, hakan ba zai sa ta yi aiki ba saboda tana kunshe da wasu sharuÉ—a.
Barista Sulaiman ya faÉ—i haka ne yayin da yake mayar da martani ga fitaccen lauyan nan da ya yi shuhura a kafafen sada zumunta, Barista Abba Hikima.
A cewar Barista Sulaiman, neman tayar da kura ko kawo hargitsi ya sanya Barista Hikima ya dago da batun dokar hana lefe a jihar ta Kano.
A makon da muke ciki ne dai cikin wani shiri na gidan rediyo a Jihar Kano da kuma shafinsa na Facebook, Abba Hikiman ya dauko batun cewa a Dokar Kano laifi ne ka yi lefe kamar yadda ake yi a yanzu.
Wannan magana dai ta ta da kura musamman a soshiyal midiya, inda wasu ke ganin bakinsa wasu kuma ke sam barka.
Sai dai Lauya Sulaiman ya ce Hikima tsakuro sashi na 5 na dokar ya yi, ba wai gaba É—aya dokar kacokan ya fassara ba.
“SaÉ—arar da ya ke magana a kai ita ce ta 3 a sashi na 5 na dokar.
“Doka ce da aka yi ta tun zamanin mulkin soja a shekarar 1988 wacce aka sanya wa ‘Dokar Aure da kuma sanya ido a kan abubuwan da suka shafi al’adun auren’. Amma fa mutane ba za su fahimci dokar ba sai an dauko gundarinta,” in ji shi.
Barista Sulaiman ya ce sashin da aka tsakuro batun lefen, ya zayyano al’adun aure 19 da suka haÉ—a da Gara, Zaman Ajo da Gaisuwar Iyaye sai Lefe, wanda shi ne ya zo a na 3 a lissafin.
“Bayan sashi na 4 da ya yi bayani kan haramcin auren dole, da sashi na 3 da ya yi na sadaki, akwai muhimmin sashi wato na 7 da ya yi bayanin sakin auren da za a iya kome da na rabuwa.”
“Daga saki É—aya zuwa na biyu, dokar ta ce mace za ta ci gaba da zama gidan mijinta ne ya ci gaba da kula da ita kamar yadda yake yi kafin sakin.
“Shi kuma saki 3 za ta koma gidan iyayenta, amma zai ci gaba da daukar nauyin ’ya’yan da suka haifa.
“Haka kuma sashi na 9 na kundin dokar ya yi bayanin cewa kotun sasanta ma’aurata ce ke da hurumin hukunta duk wanda ya saba wa dokar, wacce a halin yanzu kwata-kwata babu ita.”
Barista Sulaiman ya kuma yi karin haske kan kotun, da kuma hukuncin da dokar ta tanada ga duka wanda ya saba mata.
“Kotu ce da ta haÉ—a masanin addinin Musulunci da zai jagorance ta, sai babban limamin masallacin Juma’a, sai Magatakardar yankin, sai mutane biyu da ke aiki a Ma’aikatar Walwalar Jama’a, da ta Matasa da Wasanni, sai kuma wakilan bangarorin 2, da Mai unguwa, sai kuma wani malamin ko Limamin gari baki É—aya.
“Abun tambayar shi ne yanzu akwai irin wadannan kotunan yanzu? Babu a Kano. Haka kuma akwai batun yin rajistar duk auren da aka yi a wuraren da aka ware don yin hakan, wanda shi ma babu yanzu.”
Sulaiman ya ce don haka a nasa ra’ayin neman suna ne da kuma son ta da kura ya sanya Abba Hikima tsakuro doka ya yi bayanin wani bangare nata ya kyale sauran sassan da suka fi bangarori masu muhimmanci.
Ya kuma ce idan har za a yi amfani da ita, shi kansa mai laifi ne, domin ya yi lefe a nasa auren da na ’yan uwansa.
“Dukkanmu lauyoyi ne, kuma mun san cewa akwai dokokin da suna nan a rubuce, amma barci suke yi saboda ba a yin aiki da su ko ba zai yiwu a yi aiki da su ba.
“Misali ko tarar da aka tanada ga wanda ya karya dokar Naira 200 ne ko daurin watanni 2,” in ji shi.
(AMINIYA)