Labari Da Dumiduminsa: NAHCON Ta Sanar Da Kudin Hajjin 2024

Idan dai za a iya tunawa da farko Shugaban Hukumar Alhazai ta Najeriya (NAHCON), Malam Jalal Ahmad Arabi ya yi niyyar barin kudin aikin Hajjin 2024 a kan Naira miliyan 4.5 da aka karba a matsayin kudin ajiya tun farko. 

A sanarwar da mataimakiyar daraktar harkokin hulda da da dab'i ta hukumar, Fatima Sanda Usara ta sanyawa hannu, taceHasashen ya kasance mai girma har sai da batun kara karyewar darajar Naira ya faru a tsakiyar mako. Abin takaici, rashin tsayawa da aka samu a farashin Dala a baya-bayan nan ya tilasta yin gyare-gyaren da ya dace duk da kokarin da Shugaban Hukumar NAHCON, Jalal Ahmad Arabi ya yi na kula da farashin aikin Hajjin bana a kan wannan adadin.
 
A karshen watan Janairu ne shugaban Arabi ya tattauna kan samun rangwame mai yawa tare da masu ba da ayyukan Alhazai a masarautar Saudiyya, tare da kokarin rage farashin maniyyata aikin hajji. Sai dai kuma halin da ake ciki na tabarbarewar kudi a cikin satin, ya sa hukumar ta dauki tsattsauran mataki na karfafa nasarorin da aka samu wajen rage farashin hidimar aikin Hajji, wanda idan ba tare da haka ba farashin aikin hajjin na shekarar 2024 zai iya zuwa kusan  Naira miliyan shida
 
Don haka, ana bukatar maniyyatan da suka fito daga yankin Kudancin Najeriya su biya N4,899,000 a matsayin kudin aikin Hajji; wadanda suka fito daga tsakiyar Arewa za su biya Naira miliyan 4,699,000, na aikin Hajji, kuma mahajjata daga Yola da Maiduguri za su biya Naira miliyan 4,679,000 na aikin Hajjin 2024.
 
Da yake bayyana nadamarsa, Shugaban Hukumar Arabi ya bayyana cewa, wannan nufin Allah ne, domin Hukumar, tana fuskantar tsaikon wa’adin ranar 25 ga watan Fabrairu, ta tanadi wasu zabukan da za su ci gaba da kasancewa a cikin iyakar Naira miliyan 4.5 da ya yi aiki da su. Don haka, NAHCON ta bayyana kudin da za a iya yi na aikin Hajji don cika wa’adin lokacin da ke tafe.
 
Don haka an shawarci maniyyatan da su cika ragowar kudinsu nan da zuwa ranar Litinin 12 ga watan Fabrairu don baiwa hukumar damar mika kudaden kafin cikar wa’adin.
 
Hukumar NAHCON tana tabbatar lwa al’umma kudurinta na ganin an gudanar da aikin hajji cikin nasara da duk da kalubalen da ke tattare da canjin kudaden kasashen waje. Hukumar ta yaba da fahimta da hadin kan al’ummar Musulmin Najeriya a wadannan lokuta.
 

Popular posts from this blog

Yanzu - Yanzu: Bankuna Zasu Karbi Tsofaffin Kudi Ko da Bayan Karewar Wa'adi - Emefiele

Zababben Gwamnan Kano Ya Kafa Kwamitin Karbar Mulki